Bauchi mai abubuwa tara sau uku

Allah  Ya albarkaci birnin Bauchi fadar Masarautar Bauchi kuma fadar Jihar Bauchi da wasu abubuwan da tarihi ba zai taba mancewa da su ba. Ga su nan kamar haka: Kofofi tara 1.Kofar Idi Kofar Ran Kofar Wambai Kofar Tirwun Kofar Jahun Kofar Wunti Kofar Wasai Kofar Dumi Kofar Nasarawa Duwatsu Tara Dutsen Warinje Dutsen Zartu […]

Bauchi mai abubuwa tara sau uku

Bauchi mai abubuwa tara sau uku

Allah  Ya albarkaci birnin Bauchi fadar Masarautar Bauchi kuma fadar Jihar Bauchi da wasu abubuwan da tarihi ba zai taba mancewa da su ba. Ga su nan kamar haka:

Kofofi tara

1.Kofar Idi

  1. Kofar Ran
  2. Kofar Wambai
  3. Kofar Tirwun
  4. Kofar Jahun
  5. Kofar Wunti
  6. Kofar Wasai
  7. Kofar Dumi
  8. Kofar Nasarawa

Duwatsu Tara

  1. Dutsen Warinje
  2. Dutsen Zartu
  3. Dutsen Kobi
  4. Dutsen Tanshi
  5. Dutsen Iya
  6. Dutsen Unguwar Mahaukata
  7. Dutsen Gayya
  8. Dutsen Unguwar Bauchi
  9. Dutsen Fa’an Jahun

Rijiyoyi

  1. Rijiyar Bauchi
  2. Rijiyar Danchanga
  3. Rijiyar Bakin Kura
  4. Rijiyar Zannuwa
  5. Rijiyar Kobi
  6. Rijiyar Gwallaga
  7. Rijiyar Gambo
  8. Rijiyar Lifidi
  9. Rijiyar Garkami

Wannan ya sa a ake yi wa Sarkin Bauchi Malam Yakubu kirari da mai abubuwa tara sau uku: Wato Mai Kofa Tara Mai Dutse Tara Mai Rijiya Tara, saboda a zamanin Sarkin Bauchi Malam Yakubu garin Bauchi yana da rijiyoyi tara ne kawaida jama’a ke amfani da su. Haka kuma yana da kofofi tara da ake iya rufe su idan dare ya yi a wancan lokaci. Kuma garin yana da manya-manyan duwatsu guda tara a Bauchi.

 

Mun samo ne daga shafin Jakadiyar Jihar Bauchi