Bauchi ta cika ta batse a lokacin Maulidin Inyass
Birnin Bauchi fadar Jihar Bauchi ya cika ya batse da dimbin jama’a da galibinsu mabiya darikar Tijjaniyya ne da suka fito daga sassan kasar nan da wasu kasashen Afirka domin halartar bikin Maulidin Sheikh Ibrahim Nyass Al-Kaulahi da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata. Wakilinmu wanda ke cikin wani ayari na masu zuwa […]
Birnin Bauchi fadar Jihar Bauchi ya cika ya batse da dimbin jama’a da galibinsu mabiya darikar Tijjaniyya ne da suka fito daga sassan kasar nan da wasu kasashen Afirka domin halartar bikin Maulidin Sheikh Ibrahim Nyass Al-Kaulahi da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Wakilinmu wanda ke cikin wani ayari na masu zuwa Mauludin da suka tashi daga Jos fadar Jihar Filato a ranar Juma’a ya ruwaito cewa dimbin motocin da suka fito daga yammacin Jihar Bauchi da kuma rashin kiyayen dokokin hanya sakamakon rige-rigen da direbobi ke yi domin isa Bauchi, ya tilasta musu kwana a kan hanya a tafiyar da ba ta fi awa daya ba.
Ya ce sun bar Jos da misalin karfe 3:45 na yamma, kuma sun isa garin Magama Gumau da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi da misalin karfe 5:00, amma bayan isarsu wasu gidaje da ke kusa da Tashar Saleh a kusa da Magama Gari da misalin karfe 5:06, sai jerin gwanon motocinsu ya tsaya cik na tsawo awa biyu ba tare da ko motsawa ba.
Ya ce sai da suka shafe awa bakwai a wurin da bai fi tafiyar minti biyu ba, inda ya zamo ba shiga ba fita daga Bauchi ko Jos, baya ga wasu motoci da suke yin yanke ta cikin daji daga bayan garin Magama Gumau suna yin Bauchi.
Galibin mutanen da wakilinmu ya tattauna da su a wannan lokaci sun koka kan yadda direbobin suka ki karbar umarni ko shawara daga ’yan agajin Jama’atu Fityanul Islam da na Munazzamatu Fityanul Islam wadanda suka yi bakin kokarinsu domin daidaita al’amura amma lamarin ya ci tura.
Ya ce da misalin karfe 11:00 na dare ne suka samu wucewa zuwa garin Bauchi, kuma suna isa kauyen Wunti Dada suka iske hanyar ta sake rufewa inda a nan suka sauka suka kwakkwanta a kan titi har zuwa wayewar gari.
Lokacin da ya isa cikin garin Bauchi kuwa ya ce mutane ne suke kai-kawo daga wannan bangare zuwa wancan ba tare da sun samu zuwa ko shiga dandalin da ake gudanar da maulidin ba, wato Dandalin Ibrahim Babangida da ke unguwar kofar Ran a garin Bauchi, sakamakon yadda filin ya dinke da dan Adam wadanda wasu suna cikin filin kwana uku zuwa biyar kafin ranar maulidin.
A jawabansu daban-daban a wurin bikin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar da fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi sun roki Allah Ya jagoranci sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari da za a kaddamar a ranar 29 ga Mayun nan ta yadda za ta magance matsalolin tattalin arziki da tsaro da suke addabar kasar nan.
Sarki Musulmi wanda Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu ya wakilta ya yi addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin daukacin ’yan Najeriya, inda ya shawarci jama’a su zauna da juna cikin lumana.
A nasa bangaren Sheikh dahiru Bauchi ya ce yana da yakinin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari mai zuwa za ta kasance mai yin adalci da tausayi ga daukacin ’yan Najeriya ba tare da lura da bambancin addini ko kabilarsu ba.
Ya bayyana maulidin Nyass na shekara-shekara karo na 29 a matsayin wani dama da Musulmi daga kasashe suka hadu don yin zikirin Allah. Sai ya gode wa malaman da suka zo daga kasashen Senegal da Masar da Moroko da Saudiyya da sauransu don halartar maulidin. Ya ce Sheikh Nyass ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yada ilimi da zaman lafiya da tattalin arziki a kasashe da dama musamman Najeriya.
Shugaban Kwamitin Tuntuba da Karbar Baki na bikin Ustaz Ahmed Tijjani ya ce kimanin mutumj miliyan hudu ne suka halarci maulidin na Nyass na bana da aka yi wa lakabi da “Makon Shehi. Kuma ya ce za a tattara bayanai da kasidun da fitattun malamai suka gabatar a lokacin taron domin mayar da su littafai saboda amfani mabiya darikar Tijjaniyya.