Bayahude mai shekaru 75 ya mutu sa’o’i biyu da yi masa riga-kafin COVID-19

Jaridar Jerusalem Post ta ruwaito cewa dama tsohon na fama da ciwon zuciya

Bayahude mai shekaru 75 ya mutu sa’o’i biyu da yi masa riga-kafin COVID-19

Wani Bayahude mai kimanin shekaru 75 mazaunin garin Beit She’an na Isra’ila ya mutu bayan bugun zuciya, sa’o’i biyu da yi masa riga-kafin cutar COVID-19.

Jaridar Jerusalem Post ta ruwaito cewa dama tsohon na fama da ciwon zuciya tun kafin a yi masa riga-kafin.

Tuni dai Babban Daraktan Ma’aikatar Lafiya ta kasar, Chezy Levy ya kaddamar da kwamiti don binciken musabbabin rasuwar tasa.

An dai yi wa tsohon riga-kafin ne da misalin karfe 8:30 na safe a wani asibiti mai suna Clalit, inda ya dan tsaya a ciki na dan wani lokaci, daga bisani kuma suka sallame shi da suka ga bai nuna wata alamar cuta ba.

Sai dai Mista Chezy ya ce binciken farko-farko bai nuna alaka tsakanin mutuwar tasa da riga-kafin ba.

Ko a farkon watan Disamba da kamfanin sarrafa magunguna na Pfizer ya gabatar da samfurin riga-kafin ga Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasar Amurka, an gano cewa biyu daga cikin wadanda aka jarraba riga-kafin a kan su sun mutu, daya daga cikin su kuma ya nuna alamar rauni a garkuwar jikin sa.

Jita-jita iri-iri a kan illar da riga-kafin ke dauke da ita dai ta yi ta yaduwa a kafafen sa da zumunta na zamani kamar wutar daji.

Sai dai sanannun alamomin da aka iya hakikancewa da su ya zuwa yanzu sun hada da ciwon jiki, kumburi da taruwar jini a wurin riga-kafin, yawan gajiya da kuma ciwon kai.

Sai dai a kan yi fama da wadannan alamomin ne na tsawon wasu ‘yan kwanaki kadan, kafin daga baya kuma su bace.