Bayan an tasa keyar Ngilari gidan yari
A karshen makon jiya ne wata kotu da ke Adamawa ta bayar da umarnin tasa keyar tsohon Gwaman Jihar Mista James Bala Ngilari zuwa gidan yari bisa samunsa da laifin bayar da kwangilar sayo motoci 23 ga Kwamishinoninsa ba bisa ka’ida ba. Babbar Kotun da ke Jihar Adamawa wacce Mai Shari’a Nathan Musa yake alkalanta […]
A karshen makon jiya ne wata kotu da ke Adamawa ta bayar da umarnin tasa keyar tsohon Gwaman Jihar Mista James Bala Ngilari zuwa gidan yari bisa samunsa da laifin bayar da kwangilar sayo motoci 23 ga Kwamishinoninsa ba bisa ka’ida ba.
Babbar Kotun da ke Jihar Adamawa wacce Mai Shari’a Nathan Musa yake alkalanta ce ta yanke wannan hukunci ga tsohon Gwamnan.
Alkalin ya ce an samu tsohon gwamnan da laifin sayo motoci 23 ne ga Kwamishinoninsa a kan Naira miliyan 167 ba tare da ya bi ka’ida ba. Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ce ta gabatar da wannan kara a kotun tun a watan Satumbar bara.
Alkalin kotun ya ce wannan abu da tsohon Gwamna Ngilari ya aikata, tamkar yin amfani da karfin mulki ne wajen yin “fashi da biro”. Ya ce wannan hukunci na tura tsohon gwamnan zuwa gidan yari na tsawon shekara biyar ba tare da zabin biyan tara ba, shi ne mafi sassauci a hukuncin da ya zartar a kansa. Sai dai ya amince da tayin da Lauyan Ngilari ya yi na a yi masa sassauci, inda alkalin ya amince tsohon gwamnan ya zabi kurkukun da yake son zama har na tsawon shekara biyar a kowane sashe na kasar nan. Sai dai kafin ya yanke shawarar zai zauna ne a kurkukun Yola da ke Jihar Adamawa.
Bala Ngiliri dai ana ganin shi ya janyo wa kansa wannan abin kunya, kasancewarsa Babban Lauya kuma tsohon dan Majalisar Wakilai, bayan ya yi amfani da matsayin Gwamnan wajen bayar da kwangiloli ba tare da bin ka’ida ba. An ce a lokacin da yake bayar da kwangiloli, yana zaune a ofishinsa ne yake bayar da su ga kamfanonin da ya fi shiri da su ko da ba su cancanta ba. Abin bakin ciki shi ne yadda yake sane da cewa yin haka ya saba wa ka’ida.
Maganar gaskiya, wannan shi ne karon farko tun bayan shekarar 2015 da Hukumar EFCC ta samu nasara a wata kotu inda aka yanke wa wani babban jami’in gwamnati hukunci kuma aka tasa keyarsa zuwa gidan yari ba tare da zabin biyan tara ko bayar da beli ba. Yanzu haka akwai manyan jami’an gwamnati da hukumar take tuhumarsu a kotuna daban-daban da ke fadin kasar nan amma ba a yanke musu hukunci ba saboda wadansu dalilai na daban. Hasalima ana ta dage shari’arsu ce a mafi yawan lokuta da hakan yake jefa al’umma cikin shakkun da wuya a iya zartar musu da hukunci a karshe.
Saboda haka ya dace a yaba wa Hukumar EFCC bisa nasarar da ta samu a kan Bala Ngilari na tura shi gidan yari.
Sai dai Mai Shari’a Nathan Musa ya sallami Sakataren Gwamnatin Jihar Adamawa Mista Andrew Welye da Kwamishinan kudi na Jihar Mista Sunday Lamurde saboda rashin kwakkwarar shaidar da ta nuna an same su da laifi a tuhumar da ake musu tare da tsohon Gwamna Bala Ngilari. Tuni Ngilari ya ce zai daukaka kara bayan an iza keyarsa zuwa gidan yari.
Mista Bala James Ngilari dai shi ne Mataimakin Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako a shekarar 2014. Bayan ’yan majalisar dokokin jihar sun yi yunkurin tsige Gwamnan da Mataimakinsa ne, sai Ngilari ya yi saurin aika wasikar yin murabus amma sai ya yi kuskuren aikata ga Shugaban majaisar maimakon ofishin Gwamna da hakan ta sa ya daukaka kara a wata kotu bayan an tsige Gwamnan. Daga nan ne kotu ta yanke hukuncin rantsar da shi ya zama Gwamnan Jihar ta Adamawa inda ya yi mulkin watanni bakwai kacal da ya kare a watan Mayun 2015.
Abin lura a nan shi ne a tsakanin watanni bakwai ne Ngilari ya yi watanda da dukiyar al’ummar Adamawa inda ya rika bayar da kwangiloli barkatai ba bisa ka’ida ba.
A yanzu haka hukumar EFCC da ta ICPC tana tuhumar wadansu manyan jami’an gwamnati da dama da suka hada da tsofaffin Gwamnoni da ’yan siyasa da kuma ma’aikatan gwamnati. Alal misali akwai tuhumar da take yi wa tsohon Gwamnan Jihar Abiya Dokta Orji Uzor Kalu da Ikedi Ohakim na Jihar Imo da Murtala Nyako na Jihar Adamawa da Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa da Joshua Dariye na Jihar Filato da Sule Lamido na Jihar Jigawa da Rabaran Jolly Nyame na Jihar Taraba da sauransu. Sai dai da yawa daga cikin wadannan shari’o’i an shafe fiye da shekara 10 ana yin su ne ba tare da an zartar da hukunci ba.
Muna kira ga kotuna su gaggauta zartar da hukunci a kan laifuffukan wadannan shugabanni don ya zama darasi ga na-baya.