Bayan Azumi Ramandan Sai me? Tare da Shaikh Amin Ibrahim Sautussunnah
A lokacin da watan Azumin Ramadan ke bankwana malamai da dama na Jan hankalin al’umma da su tabbatar sun sami rabon ayyukan alheri na Azumi har zuwa rayuwar su ta bayan Ramadan Shaikh Amin Ibrahim Sautussunnah ya yi kira ga Al’ummar Musulmi da su tasirantu da kyawawan hallayar su a lokutan watan Ramadan har izuwa […]
A lokacin da watan Azumin Ramadan ke bankwana malamai da dama na Jan hankalin al’umma da su tabbatar sun sami rabon ayyukan alheri na Azumi har zuwa rayuwar su ta bayan Ramadan
Shaikh Amin Ibrahim Sautussunnah ya yi kira ga Al’ummar Musulmi da su tasirantu da kyawawan hallayar su a lokutan watan Ramadan har izuwa bayan watan yace Allah Madaukakin Sarki ya falranta azumi ne domin al’umma zu sami takawa don haka kyawawan dabi’u har zuwa bayan alamun karbuwar ibadar da aka yi ne a lokacin azumin
Malamin ya kara da cewa, Allah Ya farlanta zakatul futiri domin ta zamo tsarkaka ga azumin da aka gabatar.
“Maganganu da muka yi da wasu abubuwa da basu kamata ba shi ne hikimar shardanta ta, sannan zakkar wajiba ce fitar da ita ga yaro da babba da mace da na miji da bawa da da, sannan wanda ke cikin ciki an so a fitar masa amma yin hakan ba waji bi bane, sannan lokacin fitar da ita kafin sallah da kwana biyu ko da kwana daya ko daren sallah kafin aje masallacin idi, wanda ya bayar kafin aje idi ta zama zakka karbabbiya wanda ya bayar bayan an je idi to ta zama sadaka, sannan ana bada sa’i daya ne ga ko wane mutum wato muddun Nabiy hudu ke nan za a fitar wa ko wane mutum da yaro da babba sannan miskini ake baiwa wanda ba shi da abin da zai ci, ba wanda aka ga dama ba, aa wanda hadisi ya tabbatar ana bada shi ne wanda ba shi da shi, kuma abin da ya fi kamata shine a fitar da ita daga matsakaici cikin abincin da jama’a suke ci wato mu a nan za a iya fitar da ita da masara wanda kuma Allah ya hore masa sai ya fitar da shinkafa kaga ya saukakawa wanda zasu sarrafa ta, ana yin haka ne domin saukakawa bayin Allah a wadata su da abinci domin a hana masu roko”. In ji shi.
Shaihin Malamin Sautussunnah ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da ya rufe karatun tafsirin da ya gabatar a Masallacin Balan Yadiko a Agege, Legas.