Bayan azumi sai kuma me?
Daga Hudubar Hassan bin Abdul’aziz Alu-Assheikh, Masallacin Annabi, Madina Fassarar Salihu Makera Mukaddima. Bayan haka, ya ku al’ummar Musulmi! Wani yanayi na ayyuka masu girma ya wuce ga al’umma a daidai lokacin da matsaloli masu yawa suke shake da wuyanta, tana fama da manyan cututtuka, tana fama da bala’o’i da wahalhalu da annoba […]
Daga Hudubar Hassan bin Abdul’aziz Alu-Assheikh, Masallacin Annabi, Madina
Fassarar Salihu Makera
Mukaddima.
Bayan haka, ya ku al’ummar Musulmi! Wani yanayi na ayyuka masu girma ya wuce ga al’umma a daidai lokacin da matsaloli masu yawa suke shake da wuyanta, tana fama da manyan cututtuka, tana fama da bala’o’i da wahalhalu da annoba da cutarwa iri-iri. Tana fama da rarrabuwar kai da rauni da tarwatsewa da wulakanci da al’amura masu tsanani, tana cikin wani hali mai sanya kuka. Shin lokaci bai yi ba da za mu duba wannan hali mai radadi da tafiya ta kuskure? Shin lokaci bai zo ba, da za mu yi tsinkaya kan abubuwan da suke kawo mana rauni, mu nemo abubuwan da za su magance mana cututtukanmu da matsalolinmu?
Allah Madaukaki Yana cewa: “Shin lokaci bai yi ba ga wadanda suka yi imani zukatansu su yi tawali’u ga ambaton Allah da abin da Ya saukar na daga gaskiya?” (K:57:16).
Babu abin da ya fi dacewa ga al’umma a yau, bayan kammala azumin Ramadan mai girma, irin ta yi fatali da munanan ayyukanta, ta magance raunukanta masu yawa da suke wurare masu yawa a jikinta. Jikin da yake cike da gyambo yake fama da zogi. Kuma babu hanyar samun nasara da magani na hakika, sai ta komawa ga koyarwar addininta da riko ga cikakkiyar manhajar Littafin Ubangijinta da Sunnar Annabinta, Muhammad (Sallahu Alaihi Wassalam).
Yana daga cikin koyarwar wannan manhaja, kyautata aiki tare da gaskata Allah cewa zai taimaki addininSa a kowane wuri da kowane lokaci. Al’umma ta tsayu wajen bayar da wajibai musamman kula da raunana daga jama’a da kuma hana zalunci da cutar da bayin Allah masu rauni. “Muminai maza da muminai mata, sashinsu masoya ne ga sashi.” (K:9:71).
’Ya yan uwa a Musulunci! Lallai wajibin da ke kan ’ya’yan wannan al’umma ta Musulmi, shi ne fadaka sosai da lura ta hakika game da hadarin makiya da yadda suke kulle-kullen wargazawa da bata akidar Musulmi da zame musu kafafu da barazana ga martabarsu. Akwai miyagun abubuwan da suke yi da suka buya daga gare mu, sannan suna ta kulle-kulle iri-iri da Allah ne kawai Ya san su.
Yahudawan duniya a yau suna ta jan duniya zuwa ga hallaka da masifu, suna neman jefa al’ummar Annabi Muhammad (Sallahu Alaihi Wassalam) a cikin rafkana da fitinu da cutarwa da wulakanci. Don haka ku farka, farkawa ta hakika, ya ku al’ummar Musulmi! Ku yi kwadayi da biyayya ga wannan addini iyakar kwadayi.
Ya ’yan uwa a cikin addini! Daga cikin miyagun tanade-tanaden makiya ga Musulmi, akwai watsuwar kafafen sadarwar zamani da kafafen watsa labarai masu dauke da miyagun koyarwa da ake kokarin watsawa a wannan kasa wadda sakon Annabi Muhammad (Sallahu Alaihi Wasallam) ya bubbugo daga gare ta, kasar da take da haramomi biyu mafiya daraja a duniya, kasar da ta yi wa dan Adam abubuwa masu yawa na alheri. Ta sadaukar da abubuwa masu yawa domin tabbatar da zaman lafiya da amana da kwanciyar hankali da yada ayyukan alheri, haka ana watsa irin wadannan abubuwa a sauran kasashen Musulmi.
Don haka wajibi ne a kan Musulmi su fahimci wadannan abubuwa na barna ana yin su ne domin a yi wa al’ummar nan kisan mummuke, a rusa kyawawan halaye da dabi’unta. Allah Ya yi gaskiya inda Ya ce: “Suna gurin ku kafirta kamar yadda suka kafirta domin ku yi canjaras (ku zamo daidai).” (K:4:89).
Don haka wajibi ne a kan al’ummar Annabi Muhammad (Sallahu Alaihi Wasallam) ta fahimci manufofin addininta da dalilan maganganun Mahaliccinta. Ta fahimci ginshinki da koyarwar Musulunci, idan ba haka ba – Allah Ya kiyaye – za ta wayi gari tababbiya wadda ta yi nesa daga shiryar Ubangijinta. Allah Madaukaki Yana cewa: “Kuma ka ce: “Ku yi aiki, sa’an nan Allah zai ga aikinku da ManzonSa da kuma Muminai.” (K:9:105).
Allah Ya yi mana albarka a cikin Alkur’ani, Ya amfanar da mu da abin da ke cikinsa na ayoyi bayyanannu. Ina fadin wannan magana tawa, ina neman gafarar Allah gare mu da sauran Musulmi daga dukkan zunubi. Ku nemi gafararSa, ku tuba zuwa gare Shi, lallai ne Shi Mai gafara ne Mai jin kai.
Huduba ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah a bisa kyautatawarSa, muna yi maSa shukura a bisa datarwarSa da ni’imominSa. Na shaida babu wanda za a bauta masa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya, girmamawa ga sha’aninSa. Kuma na shaida lallai Shugabanmu kuma Annabinmu Muhammad (Sallahu Alaihi Wasallam), bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Ya Ubangiji! Ka kara tsira da aminci da albarka a gare shi da alayensa da sahabbansa da ’yan uwansa.
Bayan haka, mafi alherin zance shi ne maganar Allah, kuma mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabi Muhammad Manzon Allah (Sallahu Alaihi Wasallam). Kuma mafiya sharrin al’amura, fararrunsu, kuma kowane fararren al’amari bidi’a ne, kuma kowace bidi’a bata ce, kuma kowace bata tana cikin wuta.
Ya ku Musulmi! Mai rabo shi ne wanda ya tafiyar da lokacinsa ta hanyar gyara lahirarsa, kuma rayuwar duniya ba ta rude shi daga bayar da hakkokin Mahaliccinsa ba. Kuma kwadayin abin duniya makusanciya bai shagaltar da shi daga hakkokin Lahira masu wanzuwa ba.
Ya kai wanda ya dandani zakin da’a a watan azumin Ramadan! Ka guji auka wa sabo, ka zamo mai da’a da takawa a wanin watan Ramadan kamar yadda ka zama a cikin Ramadan din.
Sannan ka sani – ya kai Musulmi! – lallai wanda ya yi azumin Ramadan, sannan ya bi bayansa da shida a cikin watan Shawwal, kamar ya yi azumin shekara ne. Hakan ya inganta daga Manzon Allah (Sallahu Alaihi Wasallam). A duba Sahihul Muslim, Littafin Azumi, Babin Mustahabancin Azumtar Kwana Shida a Shawwal mai bi wa Ramadan, Hadisi na 1164, Hadisin Abu Ayyub (Radiyallahu Anhu). Don haka an so azumtar shida a watan Shawwal, amma wanda ake bin sa bashin azumin watan Ramadan, to, gaggauta biyan Ramadan ne ya fiye masa, domin wajibi ne mafi dacewa daga mustahabbi.
Ku sani lallai Allah Ya umarce ku da yin salati da taslimi a kan Annabi (SAW) mai girma. Ya Ubangiji! Ka yi salati da taslimi da albarka da ni’ima a bisa bawanKa kuma ManzonKa Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa.