Bayan ba da tallafin N8,000 ga talakawa sai me?

Shirin rabon tallafin Naira dubu takwas-takwas na tsawon wata shida ya isa fitar da talakawan Najeriya daga kangin talauci?

Bayan ba da tallafin N8,000 ga talakawa sai me?

Cutar Kwarona da ta mamaye duniya a shekarun baya, inda kusan komai ya tsaya cik, ita ta kawo batun a rika ba da tallafin tsabar kudi ga mutanen kasashen duniya, musamman irin namu matalauta da niyyar rage wa ’yan kasa radadin talaucin da cutar ta jefa su.

Tallafin da manyan kasashen duniya da hukumomin ba da lamuni irin su Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya suka rika raba shi ga kasashenmu da sunan tallafi ko bashi mai ragwammen kudin ruwa da kasashen suka rika tsara yadda za a raba shi kuma ga su wa da wa.

Mu a nan kasar ko lokacin da gwamnatin soja ta marigayi Shugaba Janar Sani Abacha ta janye tallafin man fetur, ba raba tsabar kudin ta rika yi ga jama’a ba da sunan saukakawa ko rage masu radadin da suka samu kansu sanadiyyar janye tallafin. Hukuma ta kafa mai zaman kanta ta sa wa suna Asusun Man Fetur (PTF), kuma ta danka shugabanci hukumar a hannun tsohon Janar Muhammadu Buhari.

A wancan lokaci ’yan kasa sun ga dimbin ayyukan raya kasa da suka hada da ilimi da samar da ruwan sha da ginawa da gyara manya da kananan hanyoyi da ginawa da gyara asibitoci da samar da magunguna da sauran ayyukan raya kasa a dukkan sassan kasar nan.

Yau shekara 24 da shigowar gwamnatin farar hula, wadda ita ta rusa Hukumar PTF, amma ayyukan Hukumar PTF suna nan ana cin moriyarsu.

Zan iya tunawa su kansu farar hula sun yi wata hukuma da suka dora wa alhakin ci gaba da sarrafa rarar karin kudin man fetur da suka kira SURE-P.

Ta waccan hukuma, Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi sun amfana da kudaden karin kudin man fetur din ta ayyuka daban-daban, amma ba su rika raba wa talakawa tsabar kudi ba.

Amma sai ga shi a wannan karo labari ya sha bamban kan yadda za a tallafa wa ’yan kasa saboda radadin talaucin da suka kara shiga, bayan janye tallafin da gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta shirya wa gwamnatin sabon Shugaban Kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu, inda ita kuma gwamnatin Tinubu ta kara kudin man fetur din daga Naira 195 a kan kowace lita daya zuwa Naira 540.

Dama kafin gwamnatin Buhari ta bar mulki, ta riga ta ciwo bashin Dalar Amurka miliyan 800 cewa za ta raba wa ’yan kasa da sunan tallafin cire tallafin man fetur.

Maganar da ake, a makon jiya Majalisar Dokoki ta Kasa (ta Dattawa da ta Wakilai), a cikin gyaran dokar kasafin kudi na shekarar 2022, ta amince wa Shugaban Kasa ya raba wa ’yan kasa da suka fi talauci Naira biliyan 520 da sunan rage radadin talaucin da suka samu kansu a sanadiyar janye tallafin man fetur da ya yi ranar 29 ga watan Mayun bana, ya yin rantsar da shi a matsayin Shugaban Kasa.

Tun a kwanakin baya, Gwamnatin Tarayyar ta ce za ta raba wannan tallafi ne ga masu tsananin talauci a kasar nan har mutum miliyan 12, na tsawon wata shida, inda kowanensu zai rika samun Naira dubu takwas duk wata.

Rabon tallafi irin wannan da sunan a saukaka wa ’yan kasa kuncin talaucin da suka shiga ba wani sabon abu ba ne kamar yadda na ambata a baya cewa shekarun baya ma gwamnatin Buhari ta rika raba wa ’yan kasa tallafin Naira dubu goma-goma da sunan ta fitar da su daga kuncin talaucin da cutar Kwarona ta ja masu.

Rahotanni daga masana tattalin arziki sun tabbatar da cewa wadancan kudade ba su iya fid da wadanda suka ci gajiyarsu daga kangin talaucin da suke ciki ba, alkaluma nuni suka yi da cewa wasu ’yan kasar na kara fadawa cikin kangin talauci.

To in haka ne, yaushe rabon Naira dubu takwas-takwas na tsawon wata shida zai fitar da mutane daga kangin talauci idan aka yi la’akari da cewa janye tallafin man fetur din ya kara jefa ’yan kasa a cikin wani mummunan mawuyacin hali na tsadar rayuwa sanadiyyar hauhawar farashin kaya da kasar nan bat a taba tsunduma ba.

A makon jiya wasu jaridun kasar nan, har da wannan jarida sun dauko labari kan irin ayyukan raya kasa da za a iya yi da tsabar kudi har Naira biliyan 400 da gwamnatin Tinubu ta ce za ta iya samu a cikin wata daya bayan cire tallafin man fetur.

Jaridun sun ce wasu daga cikin ayyukan raya kasar da za a iya yi da wadannan makudan kudi sun hada da gina rijiyar burtsatse dubu 400 ko kananan assbitocin karkara dubu 13 ko sayo motoci safa-safa (bus-bus) dubu 20 ko taransifomomin wutar lantarki dubu 26 ko ba ’yan kasuwa miliyan 39, rancen Naira miliyan goma-goma da sauransu.

Don Allah kasar da albashi bai ishi ma’aikaci ya kashe wutar gabansa kan muhimman bukatun yau da kullum irin su ciyar da iyali da dawainiyarsu da biyan haya ko kudin makarantar ’ya’yansa kafin a yi karin farashin man fetur ba, yaushe Naira dubu takwas a tsawon wata shida za ta fitar da talaka daga talaucin da yake ciki?

Ko kusa wannan fili ba ya goyon bayan a rika raba wa talakawa wadannan kudi da ba za su kashe kishirwar talaucin da suke ciki ba. Abin tambaya a nan shi ne in an ba su cikin wata shida, sai kuma me za a ci gaba da yi masu? Ko dai za a yi ne don a rufe bakinsu, ta yadda shugabanni masu fashi da bakin biro za su ci gaba da yin barnarsu?

Don Allah mai karatu, dubi yadda a cikin wancan kasafin kudi aka ware Naira biliyan 520 ga talakawa miliyan 12, kan za a ba suNaira dubu takwas na wata shida, amma aka ware Naira biliyan 70 ga ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa su 469 (Sanatoci 109 Wakailai 360) da masu yi masu hidima (mataimaka) kusan dubu 3, a zaman albashi da alawus-alawus na shekara guda. Wannan shi ne kashin dankali

In dai so ake a taimaka wa talaka, kuma arziki ya bunkasa a kasa, to irin wadancan makudan kudi a daina wadantarsu, a rika duba muhimman ayyukan raya kasa kamar yadda jariduncan suka ambaci irin abin da za a iya yi da Naira biliyan 400, da gwamnati ta ce ta kubutar a cikin wata daya na janye tallafin man fetur.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano