Bayan babban taron yaki da miyagun kwayoyi sai me?
“Mukasudin wannan taro da ganawa shi ne ya bube wata kafar tattaunawa da za ta kunshi masu shirya tsarin tafiyar da mulki da masu yin dokoki da hukumomin da su ke zuba idanu da aiwatar da doka da oda da shugabannin al’umma da kungiyoyin al’umma da gungun kwararru da masu bada tarbiyya da ma uwa […]
“Mukasudin wannan taro da ganawa shi ne ya bube wata kafar tattaunawa da za ta kunshi masu shirya tsarin tafiyar da mulki da masu yin dokoki da hukumomin da su ke zuba idanu da aiwatar da doka da oda da shugabannin al’umma da kungiyoyin al’umma da gungun kwararru da masu bada tarbiyya da ma uwa uba masu hada-hada ta ta’ammali da miyagun kwayoyi a zaman yau da kullum don gano kalubalen da ake fuskanta.” Ta bakin Shugaban Majalisar Dattawa Dokta Abubakar Bukola Saraki kenan.
“Kowane sarki, kowane dan siyasa, kowane Sanata, ya kamata ya je a yi masa gwaji a kan shan miyagun kwayoyi kafin ya hau ko a nada shi kowanne irin mukami a kasar nan. Zan yi mutukar farinciki wajen bayar da kaina a zaman mutum na farko don gwajin miyagun kwayoyi. Muna yaudarar kanmu idan muka ce bama cikin matsalar.” Mai martaba sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II kenan.
Wadannan jawabai da makamantansu sun fito daga bakunan wadannan manyan mutane biyu, a lokacin da Majalisar Dattawa ta gudanar da wani taron yini biyu a Kano tsakanin Litinin zuwa Talatar wancan mako 18 zuwa 19 ga watan Disimbar nan da aniyar gano bakin zaren akan annobar sha da fataucin miyagun kwayoyi da ta game kasar nan, musamman a jihohin Arewa, annobar da ta zama ba yaro ba babba ba mace ba namiji, ba malaman addinai balle Basarake, kar kuma ka yi batun mabiyansu, ta yadda ta zama annobar da ta shiga gidan kowa.
Gudanar da wannan gagarumin taro, ya biyo bayan sama da watanni biyu da suka gabata, wasu Sanatoci su kimanin 40, sun gabatar wa Majalisar wani kuduri, inda suka nemi lallai Majalisar ta yunkura wajen gano bakin zaren dangane da wannan mummunar annoba da ta game kasa ta sha da fataucin miyagun kwayoyi a kasar nan. A cikin jawabinsa na bude taro Shugaban Majalisar Dattawa Dokta Abubakar Bukola Saraki ya jaddada cewa wannan annoba ta sha da fataucin miyagun kwayoyi ta zama ruwan dare a kasar nan, ta yadda ba wanda ba ta shafa ba, annobar da ya ce bai kamata su zura mata idanu ba, tana ta ci tamfar wutar daji, wannan dalili ya sanya a karon farko Majalisar ta ga dacewar ta shigo ta san na yi. Yana mai jaddada cewa abin ya isa haka nan.
Shi kuwa mai martaba Sarkin Kano bayan wancan kira da ya yi na bukatar a rika gwajin kwakwalwar dukkan wanda zai nemi ya tsaya ko a nadashi kowane irin mukami a kasar nan ya ci a rinka masa gwajin kwakwalwarsa. San Kano din ya ce abin mamaki ga wasu ‘yan Majalisun Dokoki na kasa ko gwamnoni da mataimakansu ko Ministoci da masu bada shawara shugaban kasa da mataimakinsa da sarakuna, a ce bayan irin cikakkiyar kariyar tsaro da su ke da ita daga jami’an tsaro na kasa, amma a ce su na amfani da matasa da sunan masu karesu. Irin wadancan muatne inji Sarkin su ke ba matasan miyagun kwayoyi da su kan sha su aikata masu kowane irin ba daidai din da su ke bukata ba.
Wannan jawabi na Sarki sai ya tuna mani irin kiraye-kirayen da Hajiya Farida Waziri shugaba ta biyu da akayi a Hukumar yaki da ta’annati da kudin al’umma, wato EFCC, wadda ta rinka lallai a rinka gwajin kwakwalwar masu rike da mukaman siyasa na kasar nan, bisa ga irin yadda ta ga wasu na sace makudan kudaden kasar nan da ba su ma san me za su yi da su ba. Yanzu ga shi sama da shekaru 10, da yin wancan kira wasu masu mulkin suna kuma kira a kan a rinka gwajin kwakwalwar irin wadancan muatne. Kiraye-kirayen da idan mai karatu ya yi la’akari da su zai ga cewa har yanzu ana nan ‘yar gidan jiya a kan mummunar akidar wasu daga cikin shugabannin kasar nan na gurbata rayuwar al’umma ta kowane fanni, don kawai su cinma burinsu da ci gaba da mulkar ‘yan kasa.
Dukkan masu ruwa da tsakin da suka halarci taron suka kuma tofa ta albarkacin bakinsu sun amince da cewa sha da fataucin miyagun kwayoyi sun zama babbar annoba a kasar nan, da take bukatar daukin gaggawa daga kowa da kowa. A wajen taron an zo da wata matashiya da ta bayyana irin yadda aka yi ta fara ta’ammali da miyagun kwayoyi, abin da ta ce wani saurayi da ya yi alkawarin zai aureta shi ya koya mata shan miyagun kwayoyi, wanda kuma daga baya ya ki auren nata. A irin halin da ta tsinci kanta ne har wani ya yi mata fyade ta samu juna biyu, lokacin da ta samu juna biyun sai mahaifiyarta ta ce ba za a zubar ba da shi ba. Haihuwar wancan ciki da ta samu da namiji, da Allah Ya raya shi, shi ya yi sanadin shiga taitayinta ta daina ta’ammali da miyagun kwayoyin.
A wajen taron an kuma nemi iyayen yara da su rinka zuba idanu sosai da sosai akan ‘ya’yansu, musamman a kan wadanne irin abokai suke hulda da su, wane fadi ta shi suke yi a rayuwa, su kuma rinka jansu a jika. Idon kuma har tsautsayi ya sa yaran sun afka cikin shan miyagun kwayoyi, to, ba tsangwama da kyararsu ko korarsu za su rinka yi ba, a irin wannan lokaci ma irin wadannan ‘ya‘yan suke matukar bukatar tarairaya da ja a jiki da nuna tausayawa ta da da mahaifi, amma ba zagi da tsinuwa da kora za ta magance al’amarin ba.
A wajen taron an sake jaddada mugun kanbin da Jihar Kano take da shi a kasancewar kusan shekaru 3 a jere rahotannin ta’ammali da miyagun kwayoyi a tsakankanin jihohin kasar nan, da Hukumar kula da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, wato NDLEA ta fitar, Jihar Kano ita ce kan gaba. Dadin-dadawa an sake bayyana rahotan da Hukumar NDLEA din ta fitar kwanan baya cewa Jihar Kano ana shan kwalbar maganin tari da yake cikin magungunan da aka mayar miyagun kwayoyi, har kwalba miliyan 3, a kowane wata.
Taron ya jaddada cewa muddin ana son a cimma nasara a wannan yaki na sha da fataucin miyagun kwayoyi da ya zama annoba, to kuwa akwai bukatar hada karfi da karfe tsakankanin dukkan jami’an tsaron kasar nan da sauran masu ruwa da tsaki cikin al’umma a kan yadda za a yaki wannan annoba. Su kuma gwamnatoci tun daga sama har kasa akwai bukatar su taimaka wa Hukumomin da suke yaki da wannan annoba da isassun ma’aikata da kayan aiki. Alal misali Jihar Kano da ta yi kaurin suna akan ta’amm’ali da miyagun kwayoyi, Hukumar NDLEA ma’aikata 165 kacal ta ke da su duk da cikarta da tunbatsarta.
Tunda yanzu a karon farko Majalisar Dattawa ta shigo cikin wannan muhimmin batu, to kuwa akwai bukatar ta yi dukkan mai yiwuwa wajen gyaran dokokin kasar nan da suka shafi sha da fataucin miyagun kwayoyi, ta yadda za a rinka hukunta musamman masu shigo ko sayar da miyagun kwayoyin ga jama’ar kasar nan. Haka zalika akwai bukatar Majalisar ta yi matsin lamba ga bangaren zartarwa wajen ganin dukkan abin da hukumomi da suke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi sun samu abin da suke bukata don sauke nauyin da ke kansu. Samuwar haka kawai zai sa a ce Majalisar Dattawan da gaske ta ke.