Bayan biyan Naira miliyan 100: Kada ku sake ba da ko kwabo ga masu garkuwa da ni – Dan kasuwa
Alhaji Usman Mayo dan kasuwa ne mai matsakaicin shekaru wanda aka ce bai fi shekara 44 ba. Dan kasuwar harkar man fetur ne da aka ce ya fara sayar da fetur a jarka, inda ya yi ta bunkasa har ya kai ya mallaki gidajen sayar da man fetur guda hudu kamar yadda wata majiya mai […]
Alhaji Usman Mayo dan kasuwa ne mai matsakaicin shekaru wanda aka ce bai fi shekara 44 ba. Dan kasuwar harkar man fetur ne da aka ce ya fara sayar da fetur a jarka, inda ya yi ta bunkasa har ya kai ya mallaki gidajen sayar da man fetur guda hudu kamar yadda wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya. Matashin dan kasuwar wanda wata majiya ta ce, ko aure bai yi ba, ya kuma mallaki tankokin dakon man fetur sama da 30.
Sama da wata daya ne aka sace shi a wani gidan man abokinsa da ke kan hanyar Wukari a garin Takum da misalin karfe 4: 00 na yamma.
Aminiya ta samu labarin cewa wadanda suka sace dan kasuwar suka yi garkuwa da shi, sun bukaci makudan kudi daga dan kasuwar, inda wata majiya ta ce an biya su tsabar kudi har Naira miliyan 100, baya ga wasu biyace-biyace da suka hada da kudin magani da katin waya da sauransu. Sai dai bayan an biya masu garkuwa da shi wadannan makudan kudi, sai suka ci gaba da rike dan kasuwar suka sake neman a biya su Naira miliyan 100 kafin su sako shi. Sai dai a makon jiya a daidai lokacin da ake tattauna da danginsa, dan kasuwar ya yi ta maza ya shaida musu cewa kada su sake ba masu garkuwa da shi ko kwabo, inda ya ce ya rungumi kaddara in ma kashe shi, za su yi, su kashe shi, in ya so wannan kudi da suke nema a bar wa danginsa.
Dan kasuwan wandan asalinsa Bafillace ne da maihaifansa ya fito daga garin Mayo Belwa da ke cikin Jihar Adamawa suka dawo Takum da zama, wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, kafin a sace shi, ya kasance babu wanda ya kai shi karfi ta fuskar sana’ar sayar da man fetur a yankin na Takum.
Kuma kamar yadda wakilinmu ya kalato, Alhaji Usman Mayo yana da gidajen man fetur a wajen garin Takum bayan wadanda yake da su a cikin garin na Takum.
Sauran wuraren da Alhaji Usman Mayo ke da gidajen sayar da man fetur sun hada da garuruwan Marabar Baissa da cikin garin Baissa da garin Takum da kuma cikin garin Bali.
Garin Takum da kuma yankin Kudancin Jihar Taraba ya yi kaurin suna wajen matsalar yawan sace-sacen mutane ana garkuwa da su don karbar kudin fansa.
A nan ne a shekara biyu da suka gabata aka sace wani dan majalisa mai wakiltar Takum a Majalisar Dokokin Jihar Taraba Mista Hosea Ibbi.
’Yan uwan Mista Hosea Ibbi sun biya sama da Naira miliyan 40 ga wadanda suka sace shi, amma daga bisani suka kashe shi suka jefar da gawarsa a cikin daji.
Kwatsam, sai ga shi a cikin watan Fabairun bana an sace wannan dan kasuwa.
A cewar wata majiya wadanda suka sace dan kasuwar sun fara neman a biya su Naira miliyan 300 da farko inda suka ce in aka ba su wadannan kudi za su sako shi.
Majiyar ta ce daga bisani wadanda suka sace dan kasuwar sun sassauto zuwa Naira miliyan 100, amma bayan da aka ba su kudin sai yaudara ta shigo.
Majiyar ta ce wadanda suka sace dan kasuwar sun yi gargadin cewa kada a yarda a fada wa jami’an tsaro abin da ke gudana na neman kudin fansar. Ta ce wadanda suka sace Usman Mayo sun yi barazanar cewa idan aka shaida wa jami’an tsaro abin da ke gudana a tsakaninsu da ’yan uwan dan kasuwar to za su kashe shi.
Majiyar ta ce hakan ne ya sa danginsa ba su sanar da jami’an tsaro ba lokacin da za a kai Naira miliyan 100 da suka bukata.
A cewar majiyar ba wai kawai Naira miliyan dari ’yan uwan dan kasuwar suka bai masu garkuwa da mutanen ba, kudin da aka ba su sun zarce Naira miliyan 100.
Majiyar ta ce da farko an kai Naira miliyan 85, sa’annan daga bisani aka kai Naira miliyan 15. Kuma a cikin dare aka kai kudin a cikin daji kamar yadda wadanda suka sace dan kasuwar suka bayar da umarni.

“Bayan kuma da yake dan kasuwar na fama da ciwon hawan jini da ciwon suga, wadanda suka sace shi sun sake neman wasu kudi da sunan wai za su yi masa jinya, sai kuma kudin sayen katin waya wadanda duk an ba su,” inji majiyar.
Sai dai duk da cewa sun karbi wadannan kudi sai suka ki sako dan kasuwar kuma suka daina kiran iyalansa wanda hakan ya sa iyalai da ’yan uwansa cikin tunanin cewa watakila an kashe Alhaji Usman Mayo ne.
Ana cikin haka ne a cewar wata majiya a garin Takum sai Alhaji Usman Mayo ya kira iyalansa, amma a wannan karo ya fada wa iyalai da dangi ne cewa kada a sake bai wa wadanda suka sace shi ko sisin kwabo.
“Wadanda suka sace shi ne suka tilasta masa ya kira iyalansa don a karo musu Naira miliyan 100, to amma suna ji ya bayyana wa iyalai da danginsa cewa kada su sake bayar da ko sisin kwabo don a sake shi,” inji majiyar.
Majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa dan kasuwar ya bayar da umarnin cewa kada a sake sayar da wani kayansa a bai wa wadanda suka sace shi. Ya ce da a kara bai wa wadannan mutane kudi gara a bar shi in sun ga dama su kashe shi.
Kuma majiyar ta ce, dan kasuwar ya nemi mahaifiyarsa ta gafarce shi domin shi yanzu bai damu da duk abin da zai faru da shi ba.
Kamar yadda wakilinmu ya gano wannan matsala ta satar mutane ana yin garkuwa da su don neman kudin fansa ta yi kamari a Jihar Taraba, inda ta tilasta wa masu hannu da shuni da ke zaune a yankunan karkara yin hijira zuwa manyan birane.
Wuraren da masu hannu da shuni suka kaurace mawa don gudun kada a sace su sun hada da garin Tella da Dan’anacha da Garba-Chede da Maihula da Garin Abba da Garin Malam Ali da kuma Mutum Biyu.
Da yawa daga cikin wadanda suka yi kaura sun sayi gidaje a garin Jalingo fadar Jihar Taraba amma dawowarsu ke da wuya sai wannan matsala ta satar mutane ta kunno kai a garin Jalingo inda yanzu ta zama ruwan dare.
Bincike da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa daga shekara biyu zuwa yanzu an sace fiye da mutum 60 a kananan hukumomin Gassol da Bali da Gashaka da Ardo-Kola da Jalingo da Lau, kuma an biya sama da Naira miliyan 260 don fansarsu.
Aminiya ta gano cewa matsalar tana yin kamari ne saboda kusan dukkan wadanda aka sace ba a sanar da jami’an tsaro domin masu sace mutanen suna yi wa ’yan uwansu barazanar cewa muddin suka tsegunta wa jami’an tsaro to za su kashe su, shi ya sa ko lokutan da za a kai kudin fansar ba a shaida wa jami’an tsaro.
Daga cikin wadanda aka sace kuma aka biya kudade masu yawa kafin a sako su akwai wani dan kasuwa a garin Tella da ke Karamar Hukumar Gassol, sai mahaifiyar Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba da aka sace a garin Mutum-Biyu hedkwatar Karamar Hukumar Gassol, wadda aka biya kudi mai yawan gaske kafin a sako ta.
Sai dan majalisar yankin Takum da bayan biyan kudi mai yawa wadanda suka sace shi suka kashe shi, sai kuma Kakakin Gwamnan Jihar Taraba Ibrahim Mijinyawa wanda aka sace a hanyar Bali zuwa Serti a Karamar Hukumar Gashaka wanda shi ma aka biya kudi mai yawan gaske kafin aka sako shi.
Akwai kuma wani dillalin man fetur wanda aka sace a garin Serti da kuma wani falken shanu wanda aka sace a garin Mutum-Biyu da Sarkin Sansani a Karamar Hukumar Gassol su ma an biya kudi masu yawan gaske kafin a sako su.
Sai kuma wani babban jami’in gwamnatin Jihar Taraba da aka biya kudi mai yawan gaske kafin a sako shi.
Da yake magana dangane da dan kasuwan da ke hannun masu garkuwa da mutanen duk da an biya su Naira miliyan 100, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba, DSP Dabid Misal ya ce ya samu bayanin aukuwar wannan lamari ta hannun DPO din ’yan sanda da ke garin Takum.
DSP Misal ya ce Rundunar ’Yan sandan Jihar a koyaushe tana bai wa wadanda aka sace ’yan uwansu shawarar su shaida wa ’yan sanda kuma kada su bayar da kudi ba tare da sun shaida wa ’yan sanda ba. Ya ce amma duk da shawarar da suke bayarwa ’yan uwan wadanda aka sace ba kasafai suke shaida wa ’yan sanda ba illa kawai su dauki makudan kudi su kai ga wadannan miyagun mutane.
Ya ce rundunar tana iyakacin bakin kokarinta wajen dakile ayyukan bara-gurbi kuma an kama masu satar mutane da yawa a jihar a cikin ’yan kwanakin nan.