Bayan dawowa daga Faransa, Tinubu zai kai ziyara China
Shugaban zai kai ziyarar ne kwanaki kaɗan bayan dawowarsa daga ƙasar Faransa.
Kwanaki kaɗan bayan dawowa daga ƙasar Faransa, Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na shirin tafiya ƙasar China.
Mai magana da yawun shugaba ƙasa, Ajuri Ngelale ne, ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Talata.
- Jami’an tsaro sun gano bama-bamai da aka binne a Neja
- Mai shayi ya kashe saurayi saboda taliyar yara a Jigawa
Ya ce Shugaba Tinubu zai tafi ƙasar China ne a makon farko na watan Satumba.
Ngelale, ya bayyana cewa wannan ziyarar na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Tinubu na inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
A yayin ziyarar, ana sa ran Shugaba Tinubu zai gana da Shugaban ƙasar China, Xi Jinping, domin sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi tsakanin ƙasashen biyu.
Shugaba Tinubu zai kuma gana da shugabannin wasu manyan kamfanoni guda 10 na ƙasar China da suka shafi albarkatun mai da iskar gas, samar da aluminium, harkar noma, da kuma fasahar tauraron ɗan adam.