Bayan gobara: Harkokin kasuwanci na farfadowa a Kasuwar Bwari
Harkokin kasuwanci suna farfadowa a Kasuwar Bwari da ke yankin Birnin Tarayya, Abuja bayan gobarar da ta auka wa kasuwar sama da shekara daya da ta wuce. Gobarar wanda ta haifar da asarar dukiya ta miliyoyin Naira da ta shafi akasarin shaguna, yanzu mafi yawan shaguna da suka kone kurmus a gobarar an sake gyara […]
Harkokin kasuwanci suna farfadowa a Kasuwar Bwari da ke yankin Birnin Tarayya, Abuja bayan gobarar da ta auka wa kasuwar sama da shekara daya da ta wuce. Gobarar wanda ta haifar da asarar dukiya ta miliyoyin Naira da ta shafi akasarin shaguna, yanzu mafi yawan shaguna da suka kone kurmus a gobarar an sake gyara su.
Kasuwar wacce ta kunshi shagunan kayayyakin masarufi da na tufafi da bangaren dabbobi, yanzu ana ci gaba da hada-hadar kasuwanci a cikinta, duk da yake akwai shaguna da dama da har yanzu ba a sake gina su ba saboda masu su ba su da jarin da za su sake sanyawa don ci gaba da kasuwanci.
Kasuwar Bwari, kasuwa ce da kunshi kanana da matsakaitan ’yan kasuwa wadanda galibi baki ne mazauna garin da suke gudanar da harkokin kasuwanci don neman na kansu da habaka tattalin arziki.
Ana gudanar da saye da sayarwa a kasuwar cikin walwala da zaman lafiya, duk da cewa masu sayen kayan masarufi suna kokawa kan tsadar kayayyakin, inda suke dora alhakin haka kan rashin tausayi na ’yan kasuwa wadanda a kullum suke tsauwala farashin kayansu kuma hakan yake kara jefa mazauna gari cikin tsadar rayuwa duk da matsin tattalin arzikin da ake ciki.
Sai dai a nasu bangare ’yan kasuwar suna alakanta yawan hauwawar farashin kayan masarufi ne a kan manya dillalai da kamfanonin da suke yin kayayyakin masarufi da na bukatun yau da kullum wadanda suke fakewa da karin kudin haraji daga bangaren Gwamnatin Tarayya don kara wa kayansu farashi.
Kusancin garin Bwari da Abuja da kuma wasu kauyuka da mafiya yawan mazaunansu manoma ne, ya sanya ake samun kayan abinci a farashi mai sauki a kasuwar wanda hakan ke sa mutane da dama daga birnin Abuja sukan je can da Abuja wasu wurare na nesa don saye ko sarin kayan abinci musamman doya da wake da masara da sauran kayan abinci.
Da yake karin bayani, Sakataren Kungiyar ’Yan Kasuwar Bwari Malam Shu’aibu Umar kira ya yi ga Gwamnatin Tarayya ta dafa masu da bashin kudi a kan tsari mai sauki da za su iya biya don sake farfado da kasuwanci a garin. Ya ce wannan zai tallafa wa ’yan kasuwar su samu jari sannan su inganta ginin shagunansu inda ya ce mafi yawa yanzu a cikin ginin wucin-gadi suke.
Kuma ya ja hankalin gwamnati kan ta inganta titunan cikin garin Bwari tare da yin kira ga duk hukumomi da jam’ar da suka yi musu alkawuran tallafi su cika don ceto ’yan kasuwar daga durkushewa.
Ya ce talauci da jahilci su ne makasudin rashin zama lafiya da tashe-tashen hankulla da suke faruwa a sassan kasar nan, inda ya shawarci gwamnati da attajirai su bullo da wani tsari na rage radadin talauci musamman a tsakanin matasa ta hanyar ba da lamuni na jari da kuma kakkafa masana’antu.
Ya yi kira ga al’ummomi daban-daban da suke zaune a yankin su zauna lafiya da juna inda ya ce sai da zaman lafiya ne za a samu ci gaban kasuwanci da sauran al’amuran yau da kullum.
“Kasuwar Bwari tana tallafa wa Karamar Hukumar Bwari wajen samun kudaden shiga domin aiwatar da harkokin ci gaban kasa ga wannan yanki mai cike da arzikin kasar noma da kiwo,” inji shi.
Malam Shu’aibu ya bayyana rashin gamsuwarsa da irin matakan da gwamnati ta dauka wajen tallafa musu tare da yin kiran a inganta kasuwar don kawo ci gaba mai dorewa a harkar kasuwanci a yankin. Kuma ya yi kira a zauna lafiya da juna ganin yadda hargitsin da aka samu bara, ya yi sanadiyyar rasa dukiya da rayuka a garin Bwari kuma ya durkusar da harkar kasuwanci a garin.