Bayan hukuncin CAF an fara kamen ’yan Najeriya a Libya
Wata majiya ta ce ‘yan ƙasar sun ce a kan ‘Yan Najeriya za su tara kuɗin tarar da aka yanka musu.
’Yan Najeriya mazauna ƙasar Libya, sun shiga firgici bayan da Hukumomi suka fara kamen su biyo bayan hukuncin da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ta yanke.
Lamarin ya faru ne bayan ƙorafin da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF), ta shigar kan yadda aka wulaƙanta ’yan wasan tawagar Super Eagles a ƙasar Libya a kwanakin baya.
- Ɗan ci-ranin Arewa ya zama shugaban kamfanonin haƙar ma’adinai a Kudu
- Zaɓen 2024: Me ya sa ake kaɗa ƙuri’a ranar Talata a zaɓen Amurka?
Wata majiya a ƙasar ta ce: “Sun riga sun fara kamen. Labarin ya zo min cewar sun fara kamen a ranar Asabar, sun ce ba za su biya tarar ba.”
Aminiya ta ruwaito cewa tawagar Super Eagles ta fuskanci ƙalubale a ƙasar inda suka shafe sama da sa’o’i 18, ba tare da samun wajen kwana ko abinci ba.
Tawagar ta je Libya ne domin buga zagaye na biyu na wasan neman gurbin Gasar Kofin Afrika, biyo bayan nasarar da suka yi da ci ɗaya mai ban haushi a birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom.
Hakan ne ya sa, CAF ta soke wasan, tare da bai wa Najeriya ƙwallaye uku da maki uku, tare da cin tarar Libya dala 50,000.
Wannan hukunci ta sanya kafafen yaɗa labarai na Libya, buƙatar a kama ’yan Najeriya danke zaune a ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.
Sun bayyana cewar kuɗin da aka ci tarar ƙasar kamata ya yi a samo su a wajen ’yan Najeriya ta hanyar kame.
Kafafen sada zumunta sun kuma ɗora laifin tattalin arziƙin ƙasar Libya a kan ma’aikatan Najeriya, wanda suka zarge su da ɗora wa Libya nauyi.
Wani shafin Intanet na Libya News Today 1, ya buƙaci gwamnati da ta kama ’yan Najeriya da ke zaune a ƙasar ba tare da takardu ba.
Har wa yau, ya shawarci cewar duk ɗan Najeriyar da aka kama a ci sa tarar dala 500 da kuma ɗora masa haraji mai yawa.
Wani ɗan Najeriya da ke zaune a Tripoli, babban birnin Libya, mai suna Adenaike Emmanuel, ya tabbatar da fara kamen ’yan Najeriya.
“Wani ya kira ni ya ce an riga an fara kama mutane a yankinsa. Shi ne abin da ke faruwa nan a Tripoli.
“A wasu wurare, an kama mutane da safiyar ranar Lahadi. Kamar yadda na faɗa a baya, ’yan Libya ba sa boye abubuwan da suke ji.
“A tunaninsu wannan ita ce hanyar da za su ɗauki fansarsu,” a cewar Adenaike.