Bayan jawabin Tinubu kan tallafin mai, layi ya fara dawowa a gidajen man Legas
Kusan dukkan gidajen man ‘yan kasuwa sun rurrufe a Legas
Dogayen layuka sun fara dawowa a wasu gidajen man Jihar Legas, ’yan sa’o’i bayan Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da cire tallafin man fetur.
Wakilinmu ya lura cewa dimbin masu ababen hawa ne suka yi wa babban gidan man fetur na NNPC da ke Ikeja a Jihar, suna kokarin shan man.
- Abba ya kafa kwamitin yaki da kwacen waya a Kano
- Zan karbo duk kadarorin gwamnati da Ganduje ya sayar ba bisa ka’ida ba – Abba
Kazalika, ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, gidajen mai na ’yan kasuwa duk sun kukkulle ba sa sayar da man.
Kazalika, a Babban Birnin Tarayya Abuja ma, sannu a hankali an fara ganin layukan a gidajen mai.
A yayin jawabinsa jim kadan bayan rantsar da shi a filin taro na Eagle Square da ke Abuja ranar Litinin dai, sabon Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnati ta daina biyan tallafin mai.
“Muna jinjina wa matakin da gwamnatin da ta gabata ta dauka na janye tallafin man fetur wanda babu wadanda yake amfana sai masu hannu da shuni, amma ba talakawa ba. Ban ga amfanin ci gaba da biyansa ba.
“A maimakon haka, za mu yi amfani da kudaden wajen bunkasa ayyukan raya kasa da ilimi da kiwon lafiya da samar da ayyukan yi da inganta rayuwar ’yan kasa,” in ji shi.
Ya kuma ce zai duba korafe-korafen da ake yi na yawan karbar haraji daga ’yan kasuwa domin bunkasa harkar zuba jari.