Bayan kaddamar da dalar shinkafa: ’Yan kasa na son gani a kasa
A ranar Talatar makon jiya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci bikin kaddalar da dalar shinkafa a Abuja Babban Birnin Tarayya. Bikin na hadin gwiwa ne tsakanin Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN). Idan dai mai karatu bai manta ba a cikin watan Nuwamban 2015, a Jihar Kabbi Shugaban […]
A ranar Talatar makon jiya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci bikin kaddalar da dalar shinkafa a Abuja Babban Birnin Tarayya. Bikin na hadin gwiwa ne tsakanin Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN).
Idan dai mai karatu bai manta ba a cikin watan Nuwamban 2015, a Jihar Kabbi Shugaban Kasa ya kaddamar da shirin noman shinkafa, mai taken Anchor Borrower ABP, wanda a karkashinsa ne aka rika ba da rancen kudade da iri da taki da sauran kayayyakin noman shinkafa ga ’yan kungiyar ta RIFAN.
- Gyaran matatun mai ya lashe N100bn a 2021 – NNPC
- ’Yan sanda sun kama yaran Bello Turji 57 a Sakkwato
Aniyar wancan shiri na ABP, shi ne zuwa shekarar 2018, Gwamnatin Tarayya za ta hana shigo da shinkafa kwata-kwata daga kasashen waje. Sannu a hankali Gwamnatin Tarayya karkashin Bankin CBN, ta yi ta fadada shirin zuwa jihohin kasar nan, da kuma shigar da wasu cimaka har 23, a cikin shirin da suka hada da shinkafar kanta da masara da rogo da man ja da koko da auduga, kai har da kiwo.
Daga wancan shiri ne aka samar da waccan dalar shinkafa. Dalar shinkafar da ta kasance daya bayan daya har 13, kowacce ta kunshi buhunnan sanfarerar shinkafar 115,000 masu nauyin kilogiram 100, kowannensu, kwatankwacin buhunna miliyan 1 da dubu 495.
A cikin jawabinsa na maraba da baki, Shugaban Kungiyar RIFAN na kasa baki daya Alhaji Aminu Goronyo cewa, ya yi dalar ko rabin kashi daya cikin 100, na yawan shinkafar da suka noma a noman ranin bara bai kai ba.
Shi ma da yake nasa jawabin Shugaba Buhari, ya fadi cewa zuwan gwamnatinsa kan karagar mulki a shekarar 2015, akwai Masana`antun sarrafa shinkafa 15 kacal a kasar nan, amma yanzu sun kai 50.
Ya kuma fadi cewa yana da yakinin wannan shinkafa da aka yi dalarta daga nan ba inda za ta zarce sai manyan masana`antun sarrafa shinkafa da ake da su a kasar nan, da fatar hakan zai saukaka farashin shinkafar.
Shi ma Gwamnan CBN Mista Godwin Emefiele ya ce, shirin na ABP, an samu ba manoma miliyan 4 da dubu 489 da 786, bashin sama da tiriliyan 1, a cikin shekara shidda da fara shi. Shirin da Mista Emefiele, ya ce bayan inganta rayuwar mutanen karkara ya kuma gina tsari mai dorewa na ganin tallafa wa kananan manoma.
A fadar Gwamnan Babban Bankin albarkacin wannan shiri na ABP yanzu ana noma tan miliyan bakwai da rabi duk shekara, alhali kafin wannan shiri ko tan miliyan 4, ba a iya nomawa na shinkafar.
A gefe daya kuma wani rahoto na Kwamitin Ayyukan Gona na Majalisar Dattawa da aka bayyana a cikin watan Disamban bara, cewa ya yi kasar nan na noma tan miliyan 5, na shinkafa duk shekara, alhali kuma tana bukatar kusan tan miliyan 7. Ka ga kenan mai karatu, an samu sabanin adadi tsakanin kididdigar Babban Banki da ta rahoton Kwamitin Dattawan, kamar yadda aka saba samu tsakanin mahukuntan kasar nan.
Kaddamar da shirin na ABP da irin yadda gwamnatin ta iya dorewa da shi har zuwa wannan lokaci wani abin a yaba ne, duk kuwa da irin yadda ’yan kungiyar ta RIFAN suke cin amanarsa, wajen yin mursisi na kin biyan bashin da aka ba su, duk kuwa da makudan ribar da suke samu Amma dai in ban da a kasar nan kome na a yi biki ne, a ra`ayina babu wani dalili da zai sanya Babban Bankin da Kungiyar RIFAN su shirya wancan gagarumin biki na nuna wa duniya cewa kasar nan ta shiga jerin kasashen duniya da suke noma shinkafa, har da gayyato wasu shugabannin kasashen makwabtanmu irin na su Jamhuriyar Benin da Nijar da Chadi, shugabannin da Alhamdulillah ba wanda aka ga keyarsa bare ta wakilinsa a wajen bikin.
Ba don kome na fadi haka ba, sai don sanin irin makudan kudaden da mahukunta kan kashe a irin wannan biki, makudan kudaden da ka iya tallafa wa `yan kasa ko da a kan samar da ruwan sha ko hanyoyi ko inganta harkokin kiwon lafiya da sauran ayyukan raya al`umma da talakawan kasar nan suke cikin tsananin bukatarsu.
Alal misali, mahukuntan da suka shirya bikin su kadai suka san irin yawan daruruwan miliyoyin Naira da aka kashe wajen gudanar da bikin, kama daga kudaden dakon shinkafar daga sassa dabandaban na kasar nan zuwa Abuja da kuma sake mayar da ita garuruwan da za a kai ta. Kar ka yi batun kudaden tallace-tallace da akai ta yi ta kafofin yada labarai kusan mako guda kafin bikin.
Sai kuma ka waiwayi nawa aka kashe wajen wallafe-wallafe da na shirya wurin taro da wadanda suke ta gadin dalar shinkafar tsawon lokaci, da `yan tandetande da lashe-lashe da za a ba baki, Allah ma Ya takaita shugabannin makwabtan kasa da aka gayyato ba su zo ba. Ya dai kamata wadanda suke bin diddigin yadda ake tasarrafi da kudaden jama`a su bincika mana su ji ko nawa aka kashe a wancan biki. Bikin kaddamar da dalar shinkafa dai ya zama tarihi. Saura da me?
Bisa ga yadda shinkafa ta zama kusan abincin kowa a kasar nan da kuma irin tsadar da take, bisa ga rashin wadatarta kamar yadda mahukuntan kasar nan suka fi kowa sani, ’Yan kasa sun zuba idanu suna zaman jiran su gani a kasa a kan saukar farashin shinkafa, wadda a yau buhu mai nauyi kilo 50, yar kasa yana Naira dubu 25, ta waje da ake fasa kwaurinta ya kai Naira dubu 35, gwarwadon inda ka same ta.