Bayan kafuwar Jam`iyyar APC sai me kuma?

“Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta amince da bukatar neman da jam`iyyu uku ACN da ANPP da CPC suka yi na su zama jam`iyya daya ta APC. Bayan duba bukatarsu, Hukumar ta samu cewa jam`iyyun sun ciki dukkan ka`idoji da sharududdan da ake bukata akan hadewarsu,  don haka Hukumar INEC ta amince da bukatarsu,do […]

Bayan kafuwar Jam`iyyar APC sai me kuma?
Bayan kafuwar Jam`iyyar APC sai me kuma?

“Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta amince da bukatar neman da jam`iyyu uku ACN da ANPP da CPC suka yi na su zama jam`iyya daya ta APC. Bayan duba bukatarsu, Hukumar ta samu cewa jam`iyyun sun ciki dukkan ka`idoji da sharududdan da ake bukata akan hadewarsu,  don haka Hukumar INEC ta amince da bukatarsu,do haka Hukumar ta kuma amince da janye takardun shaidarsu na rijista, ta kuma basu takardar shaida daya da sunan jam`iyyar APC .”

Wannan na daga cikin jawabin Sakataren Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC mai barin gado Alhaji Abdullahi A. Kaugama, a ranar Larabar makon jiya, a Abuja lokacin da yake tabbatar da rijistar sabuwar jam`iyyar APC ga duniya baki daya.
Wannan shi ne karon farko tunda aka fara mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, a kasar nan wasu gungun jam`iyyun adawa suke haduwa wuri daya su kuma narke a cikin jam`iyya daya da aniyar su tunkari jam`iyya mai mulki. A yadda ake yanzu, akan zababbun wakilai  jam`iyyar PDP mai mulki a gwamnatin tsakiya, ita ke da gwamnonin jihohi 23, da `yan Majalisar Dattawa 72, da `yan Majalisar Wakilai ta tarayya 214. Yayin da gungun jam`iyyun adawa uku da suka zama APC suke da gwamnonin jihohi 11 (idan ka hada da Gwamnan Jihar Imo wanda ya yago wani bangare na jam`iyyarsu ta APGA ya shigo hadakar), da `yan Majalisar Dattawa 32 dana Majalisar Wakilai ta tarayya 134.
Idan muka koma baya kadan, a karatowar zabubbukan shekarar 2011, jam`iyyar ACN da tsohon Gwamnan Jihar Legas Alhaji Bola Ahmed Tinibu yake jagoranta a kasa baki daya da jam`iyyar CPC da Janar Muhammadu Buhari yake jagoranta suka fara yunkurin ganin sun hade don tunkarar wancan zabe, amma sabani da aka samu da kuma kuracewar lokaci ya sanya yarjejeniyar shiga zaben bata yiwu ba a wancan lokacin.
A wannan karon ma jam`iyyun ACN da ANPP, su suka fara yunkurin tafiya taren don tunkarar PDP a zabubbukan shekarar 2015, daga baya kuma ANPP ta shigo, inda suka yanke shawarar sai dai su hade wuri daya, su kuma nemi canjin suna. Haka kuma aka yi, a lokacin da a ranar 29 ga watan Janairun da ya gabata gwamnonin jam`iyyun suka yi wani taro a Legas inda suka tabbatar da aniyar jam`iyyunsu zasu hade wuri daya. Bayan taro gwamnonin jam`iyyun ne kuma Iyayen jam`iyyun a ranar 5 ga watan Fabrairun da ya gabata su ma suka hadu suka jaddada aniyar da gwamnoninsu suka dauka ta hadewa wuri daya da sunan jam`iyya daya.
Abin da da harkar siyasa, ambata wannan aniya ke da wuya da kuma rada wa sabuwar jam`iyyar tasu sunan APC, sai ga wasu kungiyoyi da za ka iya kira `yan hana ruwa gudu, har guda uku (kungiyoyin da ake zargin jam`iyyar PDP ta turo su, zargin da PDP ta sha musantawa), duk sun fito da bukatar a yi masu rijistar sababbin jami’yyunsu da lakabin APC. karewa ma da karau har yanzu maganar da ake duk da tun tuni Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta yi watsi da bukatun wadancan kungiyoyi uku akan rashin cika ka`idoji, amma dai daya daga cikinsu (Africa Peoples` Congress) tana kotu.
Yanzu dai ka iya cewa bakin alkalami ya riga ya bushe, manyan jam`iyyun adawar kasar nan a karon farko sun samu wata dama ta yin aiki tare da aniyar ganin sun karbi mulki a shekarar 2015, daga hannun jam`iyyar PDP, dake rike da shi tun a shekarar 1999, da aka komo kan mulkin demokradiyya. Don haka yanzu da samun wannan dama da `yan adawa suka yi a karon farko kuma cikin radin kansu, ina tafiya ta dosa a cikin sabuwar jam`iyyar ta APC.
Ba sai an fada ba, siyasar kasar nan musamman ta wannan karon cike take da batun addini da kabilanci, kai har ma da jinsi. Rashin fili ba zai ba ni dama ba in bi kowace shiyya cikin shiyoyi shidda ko jihohi 36, na kasar nan in ce ga matsayin kowane jigo na cikin wannan sabuwar tafiya ta APC. Abin da ake fata da zuwan APC din, bai wuce ta kasance tafiyar da ake fatan an kafata akan amana, ta yadda duk wanda aka sa a gaba, to, a kalli abin da ake son a cimma buri, ba wai wane ne shi ba ko ina ya fito ko me ye addinsa bare kabila.
Wannan ke nan, akwai kuma bukatar tabbatar da yin kome cikin gaskiya da adalci wajen zaben shugabannin da za su shugabanci wannan sabuwar jam`iyya ta APC, tun daga mazabu, zuwa kananan Hukumomi zuwa jihohi zuwa tarayya akan adalci, su kuma sai su guji yin karfa-karfa, wajen tsayar da `yan takarar da jam`iyyar ta APC za ta gabatar don shiga zabubbuka masu zuwa, kowa dai ya san irin balahirar da jam`iyyu suke ciki har zuwa wannan lokaci a wasu jihohi akan tsayar da `yan takarar akan hanyar karfa-karfa. Akwai kuma mufukai `yan muna gidan Sarki, muna gidan Waziri, su ma irin wadannan mutane akwai bukatar a zuba idanu akansu.
Tun kafin sabuwar jam`iyyar APC, ta samu rijista ake ta rade-radin cewa wasu gwamnoni da `yan Majalisun Dokoki na kasa na jam`iyyar PDP, suna da aniyar canja sheka zuwa APC din,  yanzun ma da rijistar ta samu a ci gaba da baza wannan rade-radi, wanda ba wani abin mamaki bane a siyasa irin ta wannan jamhuriyar, da sai mutum ya nemi takara a jam`iyyarsa bai samu ba, sai kuma ya matsa gaba wata ta bashi. Lallai kama a yadda APC take yanzu tana bukatar wasu gwamnoni da `yan Malisun Dokoki na PDP su canja sheka zuwa cikinta. Masu iya magana dai kan ce bukatar dara kasawa, ita ma jam`iyyar siyasa burinta ta ci zabe, don haka babban burin APC, shi ne ta ci zabe. Allah Ka bamu shugabanni na gari.