Bayan kai masa hari, Gwamna Ortom ya yi ganawar sirri Buhari

A ranar Talata Gwamna Samuel Ortom na Jihar Binuwe, ya yi wata ganawar sirri da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadarsa ta da ke Abuja. Ganawar na zuwa ne kwanaki kadan da wasu ’yan bindiga suka kai wa gwamnan hari a karshen makon da ya gabata. Mayakan Boko Haram sun kashe mutum uku a Kamaru […]

Bayan kai masa hari, Gwamna Ortom ya yi ganawar sirri Buhari

Gwamna Ortom tare da Shugaba Buhari

A ranar Talata Gwamna Samuel Ortom na Jihar Binuwe, ya yi wata ganawar sirri da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadarsa ta da ke Abuja.

Ganawar na zuwa ne kwanaki kadan da wasu ’yan bindiga suka kai wa gwamnan hari a karshen makon da ya gabata.

A ranar Asabar ce ’yan bindiga suka kai wa ayarin motocin gwamnan hari yayin da yake dawowa daga gonarsa a kauyen Tyomu da ke kan babbar hanyar Makurdi zuwa Gboko.

Bangarori da dama a kasar sun yi ta Allah wadai da harin, inda Shugaban Kasar a ranar Lahadi ya bai wa hukumomin tsaro umarnin gudanar da bincike mai zurfi a kan lamarin.