Bayan karbar kudin fansa N20m, ’yan bindiga sun rike Sarkin Bungudu
Mako hudu da sace basaraken, masu garkuwa da shi sun yi mirsisi kan kudin fansa.
Masu garkuwa da mutane sun ki su sako Sarkin Fulanin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru, bayan sun karbi kudin fansa Naira miliyan 20 da suka nema a kansa.
Kimamin wata guda ke nan da masu garkuwa dauke da muggan makamai suka bude wa matafiya wuta a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, sannan suka yi awon gaba da Sarkin Bungudu.
- Najeriya A Yau: Yadda shugabannin Najeriya ke boye kudaden haram
- Na ba sojoji umarni su fara kera makaman yaki a Najeriya —Buhari
Duk da cewa an biya Naira miliyan 20 da suka bukata a matsayin kudin fansar basaraken, har yanzu sun ki su sako shi.
Aminiya ta gano cewa wani kasurgumin dan bindiga, Boderi Isiya, shi ne ya yi garkuwa da basaraken da sauran matafiya da ke motocin haya a daidai kauyen Dutse da ke kan babbar hanyar.
Boderi Isiya na aikata ta’addancinsa ne a yankin da ya tashi daga Riyawa zuwa Buruku ya dangana da Dajin Sabon Birni a Jihar Kaduna.
Wata majiya ta shaida mana cewa bayan an biya kudin fansar basaraken, sai Boderi ya tubure cewa “Naira miliyan 100 za a ba su, ba abin da suka shirya da farko ba.”
Majiyar ta ce an gargadi iyalan basaraken da masu shiga tsakani cewa da su yi hattara da Boderi Isiya, saboda ya taba shan alwashin cewa ko an biya kudin fansar ba zai sako shi ba.
Sarkin Fulanin Bungudu sananne ne wajen tsaninsa a kan ayyukan ’yan bindiga a masarautarsa inda yake goyon bayan ’yan banga, wadandan ba sa ga maciji da ’yan bindiga.
Yadda aka yi garkuwa da Sarkin Bungudu
Masu garkuwar sun tare basaraken ne a kan hanyarsa ta zuwa jiharsa ta Zamfara, domin tafiya halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya tare da wakilan gwamnatin jihar.
A yayin tabbatar da harin da aka kai da tsakar ranar 14 ga Satumba, 2021, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna, ta ce masu garkuwar da suka yi awon gaba da basaraken, sun sace matafiya da ba tantance yawansu ba.
Aminiya ta gano cewa, kasurgumin dan bindiga Boderi Isiya, wanda ake zargi da garkuwar, ya yi kaurin suna wajen wasu hare-haren da ’yan bindiga suka kai a kananan hukumomin Giwa, Chikun, Igabi da Zariya a Jihar Kaduna.
Har wa yau, Boderi Isiya yana da hannu a garkuwa da aka yi da daliban Kwalejin Gandun Daji na Tarayya da ke Afaka a Jihar Kaduna a watan Maris.