Bayan komawa APC: Wajibi ne a samu canji a 2015 – Atiku
Tsohon Mataimakin Shuganan kasa Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa Timipre Sylba sun ce wajibi ne a samu canji a badi saboda ’yan Najeriya sun gaji da mulkin PDP. Sun bayyana haka ne a wani gangami a Yola a ranar Litinin da ta gabata, lokacin karbar Atiku a cikin Jam’iyyar APC, sakamakon bayyana komawa […]
Tsohon Mataimakin Shuganan kasa Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa Timipre Sylba sun ce wajibi ne a samu canji a badi saboda ’yan Najeriya sun gaji da mulkin PDP.
Sun bayyana haka ne a wani gangami a Yola a ranar Litinin da ta gabata, lokacin karbar Atiku a cikin Jam’iyyar APC, sakamakon bayyana komawa jam’iyyar daga PDP da ya yi a ranar Lahadin da ta gabata.
Atiku ya ce a shekarar 2015 akwai bukatar mulki ya fitce daga hannun masu ‘ra’ayin rikau’ zuwa hannun masu ‘ra’ayin canji’ wadanda suke shirye su kawo canji mai ma’ana a kasar nan. “Canji yana zuwa ga Najeriya, kuma wajibi ne a yi shi. Kawar da PDP daga gadon mulki abu ne da ba makawa, lokaci kawai ake jira. ’Yan Najeriya sun gaji da kuma za su fatattake su a shekarar 2015,” inji shi.
Ya ce, “Idan kuka ganni da Baba Mai Mangoro (Gwamna Nyako) da sauran masu ruwa da tsaki kun san canji yana zuwa a Najeriya,” inji Atiku.
Komawar Atiku APC sake hadewa ne da abokan siyasarsa a rusasshiyar Jam’iyyar AC wadda ya shiga a shekarar 2006 kuma ya zama dan takarar shugaban kasa a karkashinta a zaben shekarar 2007. Daga baya AC ta koma ACN, kuma a bara ta hade da wasu jam’iyyu da suka tada sabuwar Jam’iyyar APC.
Mai shekarar 67 Atiku bai yi magana kan ko tsaya takara ba, sai dai ya ce jama’a za su ji daga gare shi a lokacin da aka fara kamfe.
A jawabin tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa Timipre Sylba ya roki gafarar al’ummar kasar nan kan kawo Shugaba Jonathan kan kujerar Shugaban kasa, inda ya ce “Na zo nan a shekarar 2011 domin rokon Arewa ta zabi danmu. To yau ina nan ne a madadin mutanen Kudu maso Kudu domin in roki gafaraku kan kawo muku mugun iri. Na zo nan ne domin in nemi gafarar al’ummar Adamawa saboda danmu da kuka zaba bai tabuka komai ba, kuma gas hi kasar tana nutsewa saboda rashin iya shugabancinsa.”
Jigo a jam’iyyar kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas Cif Bola Ahmed Tinubu cewa ya yi shigar Atiku APC jam’iyyar kara talauci (PDP) tana shakar numfashinta na karshe ken an.
Shi kuma Shugaban Jam’iyyar na kasa Cif Bisi Akande kira ya yi ga daukacin magoya bayan jam’iyyar su fito su yi rajistar zama ’ya’yan jam’iyyar da aka fara a sassan kasar nan a wannan mako.
Sauran wadanda suka yi jawabai a taro sun hada da Gwamna Murtala Nyako da Janar Buba Marwa da Malam Nuhu Ribadu da Cif Audu Ogbe da sauransu. Kuma cikin wadanda suka halarci taron akwai Tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Sharrif da Sanata Muhammad danjuma Goje da Sanata Ahmad Sani Yarima da Alhaji Muhammadu Kwairanga Jada da Cif Marcus Gundiri da Alhaji Aminu Bello Masari da Cif Ogbonnaya Onu da sauransu.