Bayan korafin APC, an cire Naja’atu daga kwamitin sa ido kan zabe
Matakin na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan APC ta yi korafi a kan ta
’Yan sa’o’i bayan Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC ya yi korafi, Hukumar Kula d harkokin ’Yan Sanda ta Kasa ta sanar da cire Naja’atu Muhammad daga kwamitin da zai sa ido kan ayyukan ’yan sanda yayin zabe mai zuwa.
Aminiya ta rawaito cewa tun da farko hukumar ta sanar da nadin Naja’atu, a matsayin wakiliyar shiyyar Arewa maso Yamma a kwamitin.
- Buhari ya inganta Najeriya fiye da yadda ya same ta a 2015 – Lai Mohammed
- Saudiyya ta tsare ‘yan Najeriya 800 —NiDCOM
Amma APC, ta bakin Kakakin kwamitin yakin neman zabenta, Festus Keyamo (SAN), ta yi Allah wadai da nadin, inda ta ce bai dace ba saboda ba za ta yi musu adalci ba.
Ya ce kwamitin na kira da a yi gaggawar sauke ta daga matsayin, don ba ta cancanta ba.
Naja’atu wacce a baya ke cikin jiga-jigan yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa na APC, Bola Tinubu, ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar kwanaki kadan da suka gabata.
Sai dai a cewar Festus Keyamo, “Mun kadu matuka da nadin da rundunar ‘yan sanda ta yi wa Naja’atu Bala Muhammad, domin matsayi ne da zai bata damar zagaya wa duk inda take so don duba yadda aikin yan sanda a lokacin zabe.
“La’akari da gamsassun bayanai da muke da su, da kuma abubuwan da ta aikata, da maganganun da ta yi a baya-bayan nan don bata dan takararmu, Bola Tinubu bayan korarta daga jam’iyyar, za mu iya cewa wannan fito na fito ne rundunar ke yi da dan takararmu.
“Kuma hakan na zuwa ne a a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke nanata cewa za a gudanar da zabe mai inganci, ba tare da magudi ba. Wannan ke tabbatar mana da cewa da gaske akwai wasu kusoshi a gwamnatin nan da ke son tade dan takararmu.
Keyamo ya kuma ce Naja’atu ba ta da gaskiya da amanar da za a dauki wannan muhimmin matsayi a ba ta, don haka suna kira ga rundunar tayi maza ta sauke ta.
Amma daga bisani, hukumar ta sanar da cire sunan Naja’atun ‘yan sa’o’i bayan korafin na APC, kamar yadda ta sanar a cikin wata sanarwa ta bakin Kakakin Hukumar Kula da Harkokin ‘Yan Sanda ta Kasa, Ikechukwu Ani.
Hukumar dai ta maye gurbinta ne da AIG Bawa Lawal (mai ritaya), wanda shi ma ya fito daga shiyyar.