Bayan korar malamai 2,000 El-Rufai zai dauki wasu 10,000
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ta kammala shirye-shiryen daukar sabbin malaman firamare 10,000 bayan ta sallami wasu 2,000.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ta kammala shirye-shiryen daukar sabbin malaman firamare 10,000 bayan ta sallami wasu 2,000.
Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dokta Hadiza Balarabe, ta ce za a dauki karin malaman ne domin maye gurbin wadanda aka sallama don inganta ilimi da samar da wadatattun malami a makarantun jihar.
- Hajji 2022: Hajiya Aisha ta zama mahajjaciyar Najeriya ta farko da aka rasa
- NAJERIYA A YAU: Tasirin kawancen NNPP da ‘Labour Party’ a zaben 2023
Ta bayyana cewa gwamnatin jihar ba za ta daina kakkabe malaman da ba su cancanta ba daga makarantunta, komai adawar da za a yi da matakin.
Ta ce “Nagartar koyarwa na da matukar muhimmanci ga irin sakamakon da ake samu a ilimin yara, kuma ba za mu bari wasu tsirarun mutane su hana ’ya’yanmu wannan damar ba.”
“Ba za mu bari a ci gaba da ba wa ’ya’yan talakawa da masu rauni gurbataccen ilimi ba, saboda kawai suna halartar makarantun gwamanti.
“’Ya’yan talakawa ma sun cancanci samun nagartaccen ilimi da malamai, kuma hakkinmu ne ,” inji ta.
Ta bayyana haka ne a taron kaddamar da rabon kayan karatu ga daliban makarantun firamaren gwamnati 4,260 da cibiyoyin ilimi 838 da ke jihar.
A ranar 19 ga watan Yuni, gwamnatin jihar ta sallami malaman firamare 2,357 saboda sun fadi jarabawar kwarewar aiki da ta shirya musu.
A 2018 ta kori wasu 21,780 ta suka fadi irin jarabawar, tare da wasu 233 da ta kora a watan Dismaban 2021 kan amfani da takardun bogi.