Bayan kwana 39, ’yan bindiga sun sako basaraken Kaduna
An ba masu garkuwa da shi sabbin babura da man fetur da taba sigari
’Yan bindiga sun sako Hakimin Rijana, Ayuba Dodo Dakolo, wanda a watan Afrilu suka yi garkuwa da shi a gonarsa da ke Kurmi, kusa da Chikwale a Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.
An saki Dakolo ne a ranar Litinin tare da wasu mutanen garin su biyu biyu bayan ’yan uwansu sun ba wa ’yan bindigar kudaden fansa da babura da wayoyi.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Tsadar Taki Za Ta Hana Noma Bana
- Alarammomin Kano sun gudanar da addu’o’i na musamman don samun tsaro da shugaba na gari
“Sai da aka shafe kwana 39 na tattaunawa kafin a sake su; Dukkansu suna cikin koshin lafiya amma an sha wahala, ”in ji wata majiya daga danginsu.
Sai dai ta ki yin karin bayani ba saboda ’yan bindigar sun gargade su da yin magana da ’yan jarida.
Aminiya ta ruwaito cewa bayan kwana biyu da sace Dakolo, barayin sun bukaci a ba su babura da man fetur da man inji da sabbin tayoyin baburansu da taba sigari da katunan waya, aka kuma ba su.
Dakolo wanda ya tabbatar wa Aminiya da sakin sa, ya ce an sayar da wani kaso na gonakinsa don samun kudi fansarasa.
Ya kara da cewa talakawansa da ’yan uwa da abokan arziki sun taimaka wajen tara kudin.
“An baiwa ’yan bindigar babura guda biyu kirar Honda da kuma kudi amma ba zan iya fadin ko nawa ba ne, an kuma ba su waya kafin su sake ni,” inji shi.
Ya ce an sake shi ne tare da wasu mutane biyu daga cikin al’ummar kuma an duba lafiyarsu an tabbatar lafiyarsu kalau.Y
“Yanzu ina hutawa, amma sun ba ni ruwa mai karanta yayin da muke hannunsu, abun ba sauki,” in ji shi.
Wani dan uwan Dakolo ya ce an kashe sama da Naira miliyan uku domin a sako hakimin.
Ya kara da cewa an sako Dakolo ne a wani wuri da ke kusa da kauyen Buruku a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.