Bayan mako 2: Abincin Tinubu ya kasa zuwa hannun ’yan Najeriya
Shugaba Tinubu cewa a raba wa talakawa hatsi kyauta domin rage musu radadin tsadar rayuwa da yunwa, amma har yanzu gwamnati ba ta fito da hatsin ba
Sama da mako biyu bayan umarnin Shugaba Tinubu ga Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta raba wa talakawa ’yan Najeriya metric ton 42,000 na masara, gero da sauran kayayyaki kyauta daga rumbunan ajiyar gwamnati, amma har yanzu babu abin da ’yan kasar suka gani.
Hakan na faruwa ne a yayin da tsadar rayuwa ke kara kamari a kasar, matsalar da aka yi imani cewa cire tallafin mai da gwamnati ta yi da kuma tashin dala ne suka haifar.
Umarnin shugaban kasar na rabon hatsi ga ’yan kasar na da nufin magance tsadar rayuwa da kuma yunwar da ta haifar da zanga-zanga a sassan kasar.
Bayan umarnin nasa ne a ranar 8 ga watan Fabrairu, ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari, ya sanar a Abuja cewa za a raba hatsi kyauta ga talakawan Najeriya.
- Gwamnatin Binuwai ta ba wa makiyaya wa’addin ficewa daga jihar
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Samun Karin Kudin Shiga Baya Ga Albashi
“Za a raba wannan MT 42,000 na hatsi ne kyauta kuma kai tsaye ga mabukata,” in ji Minista Kyari.
Ministan ya shaida wa manema labarai cewa ma’aikatarsa za ta mika hatsin ga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) domin raba wa ’yan Najeriya.
A cewarsa, dalilin hakan shi ne saboda hukumar NEMA na da ma’aunin talauci a kasar, “Sun san ainihin inda ake bukata kuma suna da tsarin yadda suke jigilar kayayyaki da adanawa kafin a raba wa mabukata kyauta.
“Mun fara aiki a kan hakan; Mun riga mun umarci NEMA ta ba mu tsarin aikinsu domin mu yi gaggawar fito da duk abubuwan da aka bukata,” in ji Ministan.
Ba mu ga komai ba —Jihohi
Sai dai binciken da Aminiya ta yi a jihohi da dama ya nuna cewa har zuwa jiya (Laraba) ba a kai ga rarraba hatsin ba.
A Kano dai, lokacin da wakilinmu ya leka a jiya, ba a kai wa jihar hatsi ba.
Mai bai wa gwamnan jihar shawara ta musamman kan harkokin samar da abinci, Hajiya Aisha Muhammad Idris, ta ce jihar a shirye take ta raba kayan abinci da zarar an kawo su.
A Jihar Kwara ma wakilinmu ya ruwaito cewa, ba a kai wa jihar hatsin da gwamnatin tarayya ta yi alkawari ba.
Babbar jami’ar Hukumar NEMA a jihohin Kwara da Neja, Zainab Saidu, ta shaida wa Aminiya a jiya cewa “har yanzu ba a ba wa NEMA hatsin ba.
“Da akwai, da sun tuntube mu a ofishin shiyya sun kawo mana kai tsaye. Amma har yanzu babu wani abu makamancin haka.
“Hedikwatarmu ba ta tuntube mu ba game da batun, kuma na yi imanin su (gwamnatin tarayya) ba su fitar da komai ba tukuna.”
Shugaban SEMA na Jihar Kwara, Moshood Magaji, shi ma ya ce: “Babu sakon da muka samu kan hakan, kuma babu wani dabo da ofishina yake. Ban san wani rabo daga gwamnatin tarayya ba.”
A Jihar Taraba ma wakilinmu ya gano cewa babu wani hatsi da aka kai wa jihar, kuma babu hatsi a ofishin NEMA da ke jihar a lokacin da ya kai ziyara a jiya.
Haka lamarin yake a jihohin Gombe da Ogun, domin kuwa jami’an NEMA da ke jihohin sun ce har zuwa yanzu ba su samu hatsi daga gwamnatin tarayya ba.
Rahotanni daga jihohin Neja, Oyo, Cross River, Benue, Bauchi, Yobe, Kogi, da Nasarawa sun nuna cewa har yanzu gwamnati ba ta kai musu kayan abincin ba.
Muna jiran su –NEMA
Hedikwatartar hukumar NEMA da ke Abuja, ta shaida mana cewa har yanzu ba ta karbi hatsin daga ma’aikatar noma ba domin rarraba wa ’yan Najeriya.
Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar, Manzo Ezekiel, ya shaida wa Aminiya a jiya cewa suna tattaunawa da ma’aikatar noma game da lamarin, kuma da zarar an mika musu hatsin za su fara rabawa.
Dalilin jinkiri —Ma’aikatar Aikin Noma
Daraktan yada labarai na ma’aikatar noma da samar da abinci ta tarayya, Joel Oruche, bai amsa kiran waya ba ko kuma amsa sakon tes da muka aike masa kan dalilin rashin fitar da hatsin kamar yadda aka yi alkawari.
Sai dai wani jami’in ma’aikatar da ya zanta da Aminiya, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya danganta jinkirin da aka samu da tantance bayanai.
Ya ce an yi hakan ne domin kauce wa irin kura-kurai da aka tafka a lokacin rabon kayan agaji da aka yi a baya.
“Ma’aikatar ta gudanar da tarurruka da hukumomi da dama a matakai daban-daban don ganin cewa hatsin ya kai ga talakawan da ake so, maimakon fadawa a hannun da bai dace ba,” in ji shi.
Jami’in ya ce a halin da ake ciki, hatsin suna rumbunan ajiyar gwamnati da ke sassa daban-daban na kasar.
Ya kara da cewa dole ne a tsara yadda za a yi jigila da kuma samar tsaro yadda ya kamata domin a samu gudanar da aikin rarraba kayan abinci cikin sauki a fadin kasar nan.
Shin akwai wadataccen hatsi da za a raba?
Sai dai wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa duk da ikirarin da gwamnati ke yi, babu isassashen hatsi a rumbunan abinci da ke fadin kasar nan.
Daya daga cikin majiyoyin ta ce abin da ya dacewa shi ne gara gwamnati ta fito ta fada wa ’yan kasa gaskiyar halin da ake ciki maimakon ta yi musu alkawurran da ba za a cika ba.
‘Abin da ya fi dacewa’
Wata majiyar kuma ta ce shigo da hatsi daga kasashen waje shi ne kawai zabi na wucin gadi da ya fi dacewa a halin yanzu don magance matsalar karancin abinci.
Majiyar ta kuma shawarci gwamnati a dukkan matakai da su samar da tsaro domin karfafa gwiwar manoma kafin damima mai zuwa.
Karfin rumbunan ajiyar Najeriya
Bincike ya nuna cewa Najeriya na da rumbunan hatsi guda 33 wadanda ke da karfin adana metric ton miliyan 1.3.
Sai dai kusan 19 daga cikinsu an bai wa kamfanoni masu zaman kansu, shekaru da dama da suka gabata.
A halin da ake ciki dai, ma’aikatar noma ba ta bayar da cikakken bayani kan abubuwan da ke cikin rumbun ajiyar hatsin ba, inda ta bayyana shi a matsayin batun tsaron kasa.
Amma baya-bayan nan, ministan noma Abubakar Kyari ya bayyana wa taron hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Kasa cewa akwai kayan abinci a cikin rumbunan ajiyar hatsin.
“An yi tambaya cewa: Shin akwai hatsi a rumbunan ajiyar abinci? Amasar ita ce eh, kuma na shirin fito da hatsin domin rabarwa,” inji shi.
Ku zuba jari a fannin noma don magance yunwa —Amurka ga Najeriya
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya bukaci gwamnatin ta zuba jari a harkar noma domin magance kalubalen samar da abinci a kasar.
Wakiliyar na Amurka a Najeriya David Greene ya yi wannan kiran ne a Jihar Ekiti, a ziyarar da ya kai a gonakin Agbeyewa mai fadin hekta 15,000.
David Green ya bukaci shugabanni a Najeriya su yi amfani da filayen noma, kasa mai albarka da kuma yanayi mai kyau da kasar ke da su, don samar da abinci a cikin gida har da na fitarwa kasashen waje.
Ya ce: “Muna sane da kalubalen abinci da kuma asarar da aka yi bayan girbi a Najeriya.
“Amma na tabbata idan aka zuba jari, sannan aka samu jagoranci na gari, za a sauya rayuwar da dada daga cikin ’yan Najeriya zuwa mai kyau.”
Gudunmawa daga Sagir Kano Saleh, Vincent A. Yusuf, Maureen Onochie (Abuja), Mumini Abdulkareem (Ilorin), Magaji I. Hunkuyi (Jalingo), Peter Moses (Abeokuta), Haruna G. Yaya (Gombe), Adenike Kaffi (Ibadan), Eyo Charles (Kalaba), Hope Abah (Makurdi), Hassan Ibrahim (Bauchi), Habibu I. Gimba (Damaturu), Ibrahim M. Giginyu (Kano), Tijani Labaran (Lokoja) Umar Muhammed (Nasarawa) & Abubakar Akote (Minna).