Bayan na yi digiri na koyi kafinta- Abdulmalik Kafinta
Abdulmalik Ahmed dan asalin Jihar Katsina ne, ya yi digiri a kwas din Biology a Jami’ar Maiduguri, amma ya zabi yin sana’ar kafinta saboda sha’awa: Aminiya: Tun yaushe ka fara aikin kafinta?Abdulmalik: Bayan na kammala karatuna a Jami’ar Maiduguri a shekarar 2004 sai na fara aikin kafinta, inda nake yin kujeru da gado da sauransu.Aminiya: […]
Abdulmalik Ahmed dan asalin Jihar Katsina ne, ya yi digiri a kwas din Biology a Jami’ar Maiduguri, amma ya zabi yin sana’ar kafinta saboda sha’awa:
Aminiya: Tun yaushe ka fara aikin kafinta?
Abdulmalik: Bayan na kammala karatuna a Jami’ar Maiduguri a shekarar 2004 sai na fara aikin kafinta, inda nake yin kujeru da gado da sauransu.
Aminiya: A ina ka koyi aikin kafinta?
Abdulmalik: Ina da satifiket a kan aikin, inda na samu shaidar koyon aikin a cibiyar Borno State bocational Centre, sannan na yi Difloma a kan aikin kera kayan daki a Ramat Polytechnic da ke Maiduguri, sannan na koyi aiki na shekara biyar a cibiyar aikin kayan daki mai suna Hassan Furniture daga 1995 zuwa 2000.
Aminiya: Me ya sa ka zabi kafinta maimakon ka nemi aikin gwamnati?
Abdulmalik: Ina da sha’awar aikin kafinta ne shi ya sa.
Aminiya: Me ya sa ba ka yi digiri a kan aikin kafinta ba sai ka karanta kwas din Biology?
Abdulmalik: Ban nemi in karanta Biology ba, na tura musu ina so in karanta aikin kafinta ne, amma ba a yi a Jami’ar Maiduguri sai suka ba ni kwas din Biology, ni kuma ba na so in bata lokaci sai na karanta shi.
Aminiya: Wadansu abubuwa kake yi yanzu?
Abdulmalik: Ina yin abubuwa da dama da suka hada da buga kanta a kicin da daki da shago da sauransu. Ina yi kabet da gado da kujeru da teburi da sauransu.
Aminiya: Me mutum zai bukata kafin ya fara sana’ar kafinta?
Abdulmalik: Na farko ya kamata ya koyi aikin, sannan ya kasance mai kwazo da kuma kirkira don ya rika yin abubuwan da za su rika burge jama’a, domin kafinta ba na malalaci ba ne.
Aminiya: Alherin da ka samu ta hanyar aikin kafinta?
Abdulmalik: Aikin ya taimake ni sosai, na biya kudin karatuna, na yi aure, duk da cewa matata ta rasu a Disamban bara ta bar ni da ’ya’ya biyu. A farkon wannan shekarar na dawo Kaduna, har yanzu ban tsaya da kafafuna ba, na bar Maiduguri ne saboda na rasa komai nawa saboda rikicin Boko Haram. A Maiduguri ina da babbar ma’aikata, ina yara da suke aiki a karkashina, amma sai aka yi rashin sa’a wurin yana tsakiyar inda ake yaki, wato Umarari. Hakan ya sanya jami’an tsaro suka rufe wurin. Na bar kayayyakina tsawon wata hudu kafin na koma na dauki wadanda zan iya dauka, daga nan ne na yi kaura zuwa Kaduna.
Aminiya: Akalla kakan samu kamar nawa a wata?
Abdulmalik: A lokacin da nake Maiduguri lokacin da komai yake tafiya daidai, nakan samu kusan dubu 500 a wata, amma a nan Kaduna a yanzu ne nake sabawa da mutane, ba ni da shago har yanzu, ina wurin wani abokina ne, a bisa ga halin da nake ciki zan iya cewa ina samu sosai, nakan samu kamar dubu biyar a kowace rana.
Aminiya: Wane buri kake da shi?
Abdulmalik: A yanzu ina daya daga cikin mutanen da aka dauka don ba su horo a kan aikin kafinta da wata cibiya a Turkiyya ta shirya. Cibiyar za ta horar da mutane aikin walda da dinki da aikin kafinta da sauransu, idan har muka ci jarrabawa Gwamnatin Barno ta ce za ta taimaka mana da kayan aikin da muke bukata, don ina da yakinin bayan wannan horarwar zan samu kayan aiki da kuma kudin da nake bukata don yin aikin da dalili.
Aminiya: Shawararka ga matasa marasa aikin yi?
Abdulmalik: Ban taba cewa sai na samu aiki mai kyawu kafin in fara aiki ba, ina da burin in rika kirkiro duk wani abu da zai burge mutane, don haka ina ba marasa aikin yi shawarar kada su ce dole sai sun yi aikin gwamnati, su sani cewa suna dauke da wata baiwa da Allah Ya yi musu, don haka su yi amfani da ita don samar wa kansu aikin yi. Kada su rika jin kunyar cewa sun yi karatu don haka ba za su yi aikin karfi ba, ta haka ne za su tsaya da kafafunsu har ma wasu su yi aiki a karkashinsu.