Bayan na zabi  Buhari na koma gadon asibiti –Pasali

Shugaban Kungiyar Yakin Zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta Buhari Campaign Organization (BCO), Alhaji Danladi Garba Pasali ya ce bayan da aka dauko shi daga gadon asibitin da yake jinya ya zabi Shugaban Kasa Buhari, ya koma asibiti ya ci gaba da yin jinya.                                                                                                                                             Alhaji Danladi Garba Pasali ya bayyana haka ne a lokacin da […]

Bayan na zabi  Buhari na koma gadon asibiti –Pasali

Shugaban Kungiyar Yakin Zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta Buhari Campaign Organization (BCO), Alhaji Danladi Garba Pasali ya ce bayan da aka dauko shi daga gadon asibitin da yake jinya ya zabi Shugaban Kasa Buhari, ya koma asibiti ya ci gaba da yin jinya.                                                                                                                                             Alhaji Danladi Garba Pasali ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a garin Jos, inda ya ce bayan da aka dauko shi daga gadon asibitin da yake jinya, kuma da lokacin zaben Gwamna a makon jiya, ya je ya zabi Gwamna Lalong.

Ya ce kafin lokacin zaben Gwamnan, ya fita ya yi tarurruka da mutane daban- daban, inda ya musu bayani kan muhimmanci zaben Gwamna, musamman a Jihar Filato.

“Dama muna neman Gwamnan da zai kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar nan ne. Idan ka lura tunda aka fara rikice-rikice a jihar nan, ba a taba samun zaman lafiya kamar a wadannan shekara 4 da Gwamna Lalong ya yi yana Gwamna ba.”

Ya ce duk da an samu akasi kan za a je zaben raba-gardama a wasu mazabu da ke jihar, amma ya ce yana da yakinin in Allah Ya so Gwamna Simon Lalong ne zai ci zabe. “Domin ya fi dan takarar Jam’iyyar PDP da kuri’a sama da dubu 40. Kuma wuraren da za a sake  zaben guda 49 ne, don haka koda an je a sake wannan zabe Gwamna Lalong ne zai kasance a kan gaba,” inji shi.

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta

Sojoji sun daƙile yunƙurin mayaƙan ISWAP a Borno

An ceto ma’aikacin INEC da aka yi garkuwa a Zamfara