Bayan nasarar Buhari sai kuma me?
Yanzu da zabe ya kare, an zabi Shugaban kasa da ’yan majalisar dokokinsa da gwamnoni da ’yan majalisun jihohinsu, kuma hankalin ya fara kwantawa babban abin da jama’a ya kamata su lura shi ne, me zai biyo baya. Muna da yakinin nasarar Janar Muhammadu Buhari a zaben Shugaban kasa za ta kawo sauyi daga halin […]
Yanzu da zabe ya kare, an zabi Shugaban kasa da ’yan majalisar dokokinsa da gwamnoni da ’yan majalisun jihohinsu, kuma hankalin ya fara kwantawa babban abin da jama’a ya kamata su lura shi ne, me zai biyo baya.
Muna da yakinin nasarar Janar Muhammadu Buhari a zaben Shugaban kasa za ta kawo sauyi daga halin da muke ciki. To amma fa kuskure ne wani ya dauka Buhari ne kawai zai gyara abubuwan da suka lalace, kowa na da gudunmawar da zai bayar wajen cimma nasarar wannan gyara. Sanatoci da ’yan Majalisar Tarayya da gwamnoni da wakilan majalisun jihohinsu da ministoci da kwamishinoni da shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da ma’aikatana gwamnati a matakin tarayya da jihohi da kananan hukumomi da sauransu da ’yan kasuwa da kuma jama’ar kasa marasa aikin yi kowa yana da gudunmawar da zai bayar a kokarin gyaran kasar nan.
Babu shakka mulkin Jam’iyyar PDP na shekara 16 ya yi kusan kai kasar nan ga halaka, kuma jiki magayi koda wani bai fada mana ba, jikinmu yana gaya mana cewa al’amura sun kai magaryar tukewa wajen tabarbarewa da lalacewa. Babu tsaro ga talaucin tsiya sun dabaibaye mu a kasar nan, ta yadda muna rayuwa ne kamar a gandun dabbobi. Galibin mutane ba su san inda suka fito ba, ba su san ina za su je ba, kowa ka gani hankalinsa ba a jikinsa yake ba. Mutane na neman wani maceci da zai kwato su daga wannan bakar jarraba wato PDP wadda Allah Ya ara mata dama na tsawon shekara 16 amma ta kasa yin amfani da damar don inganta makomar kasar nan. Yadda al’amura suka kazance a lokacin mulkin PDP, musamman a zamanin Shugaba mai barin gado, Jonathan abin akwai ban tsoro, domin mun kai wani mataki da kowanenmu yake fita daga gida ba tare da tunanin zai iya komawa gida da rai ba.
To, amma fa abin da ya kamata a sani ba zaben Buhari ne kawai zai canja halin da muke ciki ba, matukar galibin jama’a ba su gyara halinsu sun tsarkake zukatansu tsakani da Allah ba, tilas ne kowanenmu ya daura aniyar fara gyara daga kansa. Akwai abubuwan da ba gwamnati ko shugaba ne zai zo ya gyara mana ba. Yadda kowanenmu yake gudanar da mu’amalarsa a tsakaninsa da iyalinsa da yadda yake yi da makwabtansa da mutanen unguwarsu da wuraren harkokinsa, ba shugaba ne zai tsaya a kansa ya ce ya yi abin da ya dace ba. Imaninsa da Allah da hukunce-hukuncensa zai yi amfani da su wajen yin abin da ya dace ko akasin haka. Abin da shugaba ko gwamna ko gwamnati za ta shigo ciki shi ne idan mutum ya ketare iyaka a huldarsa da abokan zamansa ya kai ga shiga hakkinsu da doka ba za ta iya lamunta ba. Yaya Buhari zai yi da kai idan a boye kana tauye mata da ’ya’yanka saboda kai ne mijinsu ko mahaifinsu? Ina ma zai samu labarin abin da kake yi?
Alhamadulillahi yanzu jama’a sun fara nuna wa barayin gwamnati da suke zuwa da kudi suna rabawa ga shugabannin jam’iyyu da jami’an tsaro da sarakuna da malaman addinin domin su murde zabe. Zai yi kyau nan gaba jama’a su rika nuna musu kyama. Ban yarda da masu cewa idan barayin siyasa suka kawo muku kudi ku karba ku ki zabensu, a’a duk wanda ya kawo muku kudi don yana son kau zabe shi, ku gaya masa a idonsa cewa ba za ku karba ba. Ku gaya masa cewa kun gaji da bakin mulkinsa da sata. Ku shaida masa a kan idonsa cewa za ku gwammace ku mutu da talauci domin ’ya’yanku da jikokinku su samu ’yanci daga bakin mulkin da ke cike sakaci da tsaron rayuka da dukiyar jama’a. Ku shaida masa gwanda talauci ya kashe ku domin ’ya’yanku su samu damar da za su yi karatu su samu aikin yi da ku karbi kudinsa da zai tabbatar da ku a cikin talauci.
Akwai wajibcin mu fara fitowa muna nuna wa ’yan siyasa da masu mulki zababbu da nadaddu cewa, dukiyarsu ta haram da suka tara ta handama da cuta da karya, ba ita muke bukata ba, muna bukatar a kare mana rai da dukiya da addini da mutunci fiye da Naira ko Dalar da suke dofara mana.
Siyasa lamari ne da ke bukatar mutane na kwarai, saboda da ita ake yin mulki, amma sai yanzu ta zama wulakantacciyar sana’a, duk wani mugu sai ya ce shi dan siyasa ne, ya yi ta raba kudi a zabe shi, sai abin da hali ya yi. Duk wani dan Najeriya mai hankali ya ga yadda bangaren shari’a da na zartarwa da na dokoki suka sukurkuce, jami’an tsaro da dimokuradiyyar kanta duk sun zama akwai-ya-babu. Duk wadanda aka zaba da masu hankoron a zabe su; daga Basidi sai Hauhabu sai Murakkabu,saboda lalacewar al’amarin illa nadiran, dan abin da ba a rasa ba, su ma kusan sun bata a yama. Duk rafkanuwar da masu mulki suka yi idan ka ce, subhanallah, to ka zama makiyi, babu maganar gyarawa. Bayan ko Salla kake bin liman idan ya yi rafkanuwa aka ce subahanallah, ya kasa gyarawa sai a jawo shi baya, wani ya zama limamin ya gyara a ci gaba da Sallar.
Maganar mulki ko shugabanci magana ce ta adalci a kan kowa da kowa. Mulki shi ne karshen karfi na yin gyara ko barna, saboda haka bai kamata a danka mulki a hannun mabarnaci ba, Basidi ko Hauhabu ko Murakkabu. Duk wata amanarmu, ya kamata mu nema mata ahlin da ya dace da ita musamman amanar rayukanmu da lafiyarmu da dukiyarmu da mutuncinmu da addinimu. To yanzu Allah Ya sa mun gane, mu canja, to amma fa ba canja shugabanci ba ne kawai aiki. Canja halaye da dabi’unmu shi ne babban canji.
Tunda Allah Ya tsara yadda za a yi shari’a ta adalci, ya tanadi a yi kotu da alkalai da kurkuku da ’yan sanda tun a nan duniya kafin a je Lahira a yi hukuncin karshe. Kowa ya san ba shi ne ya halicci kansa ba, Allah ne Ya halicci kowa da komai, Ya kuma tsara yadda Yake so mu rayu. Saboda haka mu kiyaye dokokinSa da umarninSa, mu yi abin da Ya ce, mu bar abin da Ya hana, shi ne zaman lafiyarmu. Allah Ya tsara mana yadda za mu rayu da juna, komai irin bambancin da ke tsakaninmu; na addini, kabila, bangare ko launin fata.
Yanzu dai kowa ya ga yadda rashin tsaro ya kai mu, kowa ya ga yadda talauci ya kai mu, shin za mu yi wani yunkuri na mayar da kasar nan kan turbar kwarai mu bude sabon babi na samar da adalci a tsakanin al’ummar Najeriya, ko za mu ci gaba da barna don samun mata’in duniya?
Ga duk masu arziki ko mawadata musamman wadanda suka mallaki rijiyoyin mai da kamfanonin sadarwa da bankuna da masana’antu, su yi kyakkyawan amfani da wannan dama su zuba jarinsu su yi mana taimakon gaggawa wajen magance yunwa da cututtuka domin rage zafin kiyayyar da ke tsakaninsu da talakawa.
Allah Yana taimakon duk wadanda suka yunkura wajen taimaka wa kansu ne. Idan Allah ya saukar da ruwa, ya rage ga masu shuka su je su yi. IkonSa ne Ya fito musu da abin da suka shuka, har su girba.
Abdulkarim daiyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya.
08060116666, 08173106666, 08023106666.