Bayan Rantsarwa: Gobe Buhari zai kai ziyara ta farko kasar waje

A gobe Alhamis shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyarar musamman kasar Saudiyya, wannan ziyarar ita ce ziyararsa ta farko da zai fara bayan rantsar da shi da aka yau Laraba a matsayin shugaban Najeriya karo na biyu. A ranakun 16 zuwa 21 ga watan nan da muke ciki ne, shugaban ya ziyarci kasar Saudiyya […]

Bayan Rantsarwa: Gobe Buhari zai kai ziyara ta farko kasar waje

A gobe Alhamis shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyarar musamman kasar Saudiyya, wannan ziyarar ita ce ziyararsa ta farko da zai fara bayan rantsar da shi da aka yau Laraba a matsayin shugaban Najeriya karo na biyu.

A ranakun 16 zuwa 21 ga watan nan da muke ciki ne, shugaban ya ziyarci kasar Saudiyya inda ya yi Umrah. Majiyarmu daga fadar shugaban kasar ta tabbatarwa Aminiya duk an kammala shirye-shiryen ziyarar shugaban zuwa kasar Saudiyyan.