Bayan sakin fursuna ya saci mota a harabar gidan yari
An sake tsare wani fursuna mai suna Kebin Jones dan shekara 33 a karshen makon da ya gabata, wanda ake tuhumarsa da laifin satar mota da aka ajiye a harabar gidan yarin Kansas a Amurka. A cewar majiyar WIBW an sake tsare Jones ne sa’o’i kadan da aka sake shi daga gidan yarin Shawnee County […]
An sake tsare wani fursuna mai suna Kebin Jones dan shekara 33 a karshen makon da ya gabata, wanda ake tuhumarsa da laifin satar mota da aka ajiye a harabar gidan yarin Kansas a Amurka.
A cewar majiyar WIBW an sake tsare Jones ne sa’o’i kadan da aka sake shi daga gidan yarin Shawnee County Jail da ke karamar hukumar Shawne a jihar Kansas a Amurka.
Jami’an tsaron gidan yarin sun gano Jones lokacin da ya bude wata mota da aka ajiye a harabar ajiye motoci na gidan yarin. Daga bisani aka gano motar ba ta Jones ba ne, ta wani makwabcin gidan yarin ne mintuna kadan da ajiye motar.
Mai motar tare da makwabtansa sun rike Jones har sai da jami’an tsaro suka zo. An kama Jones an kuma sake mayar da shi gidan yari da laifin satar mota tare da laifin barnatar da dukiya.