Bayan Sallar Azahar za a yi Jana’izar Alhaji Musa Musawa
Dattijon Arewa, Alhaji Musa Musawa, ya rasu yana da shekara 86 bayan fama da jinya
Daya daga cikin fitattun dattawan Arewa, Alhaji Musa Musawa, ya riga mu Gidan Gaskiya bayan fama da rashin lafiya.
Za a yi Sallar Jana’izar Alhaji Musa Musawa a Masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarki a Kaduna, bayan sallar Azahar, ranar Alhamis.
- Shekarau ya ki karbar takardar shaidar cin zaben Sanata
- An gurfanar da matasa 2 kan yi wa mai cikin wata 8 fyade a Abuja
Alhaji Musa Musawa wanda ya koma ga Mahaliccinsa a ranar Laraba, ya rasu yana da shekara 86 a duniya, ya bar ’ya’ya da jikoki da dama.
A lokacin rayuwarsa, ya kasance tsohon dan jarida, tsohon jakadan Najeriya, tsohon shugaban matasa na kungiyar masu kishin Arewa ta NEPU, tsohon ma’ajin jam’iyyar PRP.
An haifi Musa Musawa ne a ranar 1 ga watan Afrilun 1937 a garin Bichi an Jihar Kano, kuma mahaifiyarsa, wadda ’yar asalin garin Musawa a Jihar Katsina ce, ta rasu tun yana jariri.
Kasancewar mahaifinsa bai sake yin aure ba, sai ya kai shi kauyen mahaifiyarsa inda ta ya taso a hannun wata innnarsa, wadda ta kula da shi, har ya taso.
Daga baya ya koma Bichi, inda ya yi karatu, inda daga nan ya fara samun aikidar fafutikar yaki da danniyar turawan mulkin mallaka da gwamnatin da ta kafa a Arewacin Najeriya.