Bayan samun ’yancin kai na kudi ga kananan hukumomi saura na…..

Tun a zamanin Majalisar Dokoki ta Kasa ta shida zuwa ta takwas (daga shekarar 2007 zuwa 2011 da 2011 zuwa 2015 da 2015 zuwa 2019) ake ta cece-ku-ce duk lokacin da aka zo gyaran kundin Tsarin Mulkin Kasar nan na 1999, a kan saka bukatun da za su ba da dama ga kananan hukumomin kasar […]

Bayan samun ’yancin kai na kudi ga kananan hukumomi saura na…..
Bayan samun ’yancin kai na kudi ga kananan hukumomi saura na…..

Tun a zamanin Majalisar Dokoki ta Kasa ta shida zuwa ta takwas (daga shekarar 2007 zuwa 2011 da 2011 zuwa 2015 da 2015 zuwa 2019) ake ta cece-ku-ce duk lokacin da aka zo gyaran kundin Tsarin Mulkin Kasar nan na 1999, a kan saka bukatun da za su ba da dama ga kananan hukumomin kasar nan 774 ’yancin cin gashin kai a kan yadda za su rika sarrafa kudadensu.

A duk tsawon wancan lokaci bukatun sukan samu amincewar Majalisar Dokoki ta Kasa, amma da sun zo majalisun dokoki na jihohi sai wasu majalisun jihohin su hau kujerar na ki, bisa ga umarnin da ake zargin gwamnonin jihohinsu kan ba su na su yi haka.

Alhali wani sashi a kundin Tsarin Mulki ya yi tanadin cewa ba za a iya gyara shadara daya ba a cikin kundin ko da kuwa Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da yin haka sai an samu akalla kashi biyu cikin uku na majalisun dokokin jihohi sun amince da gyaran. Ma’ana sai majalisun dokoki na jihohi 24, daga cikin 36, sun amince, al’amarin da ya gagara samuwa a tsawon shekara 12, duk da an samu gyara wasu sassa na kundin, musamman a lokacin Majalisa ta Shida.

Ana zargin gwamnonin da ’yan majalisun dokoki na jihohi  da fakewa da tanade-tanaden sashi na 163, na kundin Tsarin Mulki da kananan sassan da ke karkashinsa irin na 6, da ya tanadin kafa Asusun Hadin-Gwiwa a tsakanin gwamnatocin jihohi da kananan hukumominta don rabawa bayan samunsu, kamar yadda kananan sassa na wancan sashi suka yi tanadi.

Bisa ga wadannan tanade-tanade, gwamnonn jihohi suke tasarufi da kudaden kananan hukumominsu ta yadda sai abin da suka ga dama suka sam musu.

Sai ga shi daga matsin lambar kasashen Turai da Amurka da kungiyoyinsu na duniya irin su Majalisar Dinkin Duniya da masu rajin kare mulkin dimokuradiyya na ciki da wajen kasar nan, an wayi gari, ba tare da an gyara Tsarin Mulkin ba, daga watan Yunin bana dukkan gwamnatocin jihohi sun fara ba kananan hukumominsu kudadensu kamar yadda ya halatta a ba su, ba tare da ko sisin kwabo ya yi ciwon kai ba.

Samuwar hakan ya biyo bayan wancan matsin lambar kasashen duniya da kungiyoyinsu a karkashin kulawar ita kanta Majalisar Dinkin Duniyar da a bara ta zare wa kasar nan ido,  cewa duk da tana da Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), tilas sai ta kafa wata hukuma ta musamman da za ta dora wa alhakin bibiyar yadda ita kanta Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi suke sarrafa kudaden jama’arsu, wala’alla kason da suka samu ne daga Asusun Tarayya, ko wanda suka tattara a cikin gida, ko ma wadanda suka ciwo bashi a ciki da wajen kasar nan.

Hanzarin da aka ce Majalisar Dinkin Duniyar ta bayar ga kasashe irin namu masu tasowa wajen tabbatar da haka shi ne bisa ga irin yadda su suke bibiyar yadda kudade suke kara-kaina a duniyar nan, sun gano cewa, ana amfani da kudaden haram wadanda ake sacewa ko sama-da-fadi daga gwamnatocin wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci a duniya.

A karkashin dokar da ta ba kananan hukumomin ’yancin cin gashin kan bayan tanadar wasu ka’idoji da sharudda da za su rika bibiyar yadda za su kashe kudaden nasu, da suka hada da lallai kananan hukumomin su bude asusun ajiya iri uku. Na daya su bude asusun ajiyar da za su rika sanya dukkan kuadaden shigarsu na cikin gida da suka tara da kansu. Na biyu su bude ajiyar da za su rika zuba kudaden da za su ware don biyan albashi da alawus-alawus din ma’aikatansu. Na uku lallai su bude asusun  ajiyar da za su rika kebe kudaden da za su rika yin ayyukan raya kasa.

A kan yadda za su rika kashe kudadensu kuwa, an tanadi cewa shugaban karamar hukuma yana da ikon ya kashe har Naira dubu 250 ba tare da amincewar majalisar kanilolinsa ko ta jiha ba, idan ko ya wuce haka daidai da Naira daya sai ya kai batun gaban majalisa don neman amincewarta. Ita ma majalisar ba ta da ikon ta kashe abin da ya haura Naira dubu 500 a kowace rana. In ya wuce haka kuma sai sun tabo alli daga hukumar.

An kuma tanadi dawo wa kananan hukumomin kasar nan wasu hanyoyin samu kudaden shiga na cikin gida da gwamnatocin jihohi suka  kankane musu a da. Ya kuma zama wajibi ga kananan hukumomin su tashi tsaye wajen kara tattara kudaden shigarsu da fadakar da mutanen yankunansu a kan irin yawan ma’aikatansu da yawan albashin da suke biyansu da yawan kudaden da suke warewa don gudanar da ayyukan raya kasa da na yau da kullum. Ma’ana komai dai ya zama a fili ga mutane.

Kazalika an tanadi tarar daidai kudin da banki ya bari majalisa ta cire ba bisa ka’ida ba ga bankin. Sannan duk wani shugaba ko kansila ko jami’in karamar hukuma, kai ko Gwamnan jiha ne ko wani jami’in jihar  da aka samu da wawure ko yin sama-da-fadi da kudaden karamar hukuma, zai hadu da hukunci mai tsanani a cikin kasar nan, sannan kasashen duniya 160 da suka sa hannu a kan yarjejeniyar su sa masa takunkumi shi da iyalinsa na ba za su shiga kasashensu ba walau da sunan ziyara ko kasuwanci ko neman ilimi, kasancewarsa azzalumi kuma barawon dukiyar jama’arsa.

Ko shakka babu samuwar wadannan kudirce-kudirce ba karamar nasara ba ce cikin tsarin tafiyar da kananan hukumomin kasar nan a wannan mulki na dimokuradiyya.

Babban abin da ya tuna min shi ne lokacin mulkin Turawa da Jamhuriyya ta Daya da sojoji suka bullo da tsarin mulkin kananan hukumomin kasar nan a  1976.  A duk tsawon wancan zamani a tsarin mulki na En’e-En’e da sarakuna suke gudanar da wani bangare na mulkin jama’a, gwamnatocin En’e-En’e kudi gare su suna kuma gasa wajen gudanar da ayyukan raya kasa ga jama’arsu, irin su samar da harkokin kiwon lafiya da ilimi da ruwan sha da hanyoyi. Kai an ce En’en Kano bayan gudanar da irin wadancan ayyuka da na ambata a sama, har filin jirgin sama da tashar wutar lantarki ta Chalawa ta gina da kudadenta musamman na daga haraji da jangali.

Tunda wadancan kasashen duniya da kungiyoyinsu sun fara taimaka mana da haka, to, kuma ya kamata su ci gaba da taimaka mana kananan hukumomin su rika daukar kwararrun ma’aikata irin su likitoci da injiniyoyi da makamantansu. Hakazalika da yadda za a rika gudanar da sahihin zabe a kananan hukumomin, sabanin yanzu da duk jam’iyyar da ke kan mulki a kowace jiha ita take lashe zabubbukan.

A karshe muna yi wa ’yan kasa tuni a kan irin gudunmawar da za mu bayar ta hanyar sa ido tsakani da Allah a kan ayyukan da shugabanninmu suke aiwatarwa da kudadenmu. An dai ce gyara kayanka ba ya zama sauke mu raba.