Bayan shafe shekara 320, an daina buga jarida mafi dadewa a duniya a kan takarda

Tun shekara ta 1703 dai aka fara wallafa jaridar

Bayan shafe shekara 320, an daina buga jarida mafi dadewa a duniya a kan takarda

Jaridar Wiener Zeitung

Wiener Zeitung, jaridar da aka yi ittifakin ta fi kowacce dadewa a duniya, a yanzu an daina buga ta a takarda bayan shafe shekara 320, inda za ta koma intanet zalla.

Hakan, a cewar jaridar, wacce ake bugawa a Vienna, babban birnin kasar Austriya kuma mallakin gwamnatin kasar ce, ta daina fita a takarda ne saboda yadda kudaden tallen da take samu a takarda suka ragu matuka.

An dai fara buga jaridar a takarda ne tun a shekarar 1703.

Daina buga jaridar dai ya biyo bayan wata sabuwar doka da gwamnatin kasar ta fitar, inda ta kawo karshen wajabcin da ke kan hukumomi da ma’aikatun gwamnati na sanya tallace-tallacensu a jaridar takarda kawai.

Sauyin dai ya yi sanadin raguwar kudaden tallace-tallacen da suka kai Yuro miliyan 15 ga jaridar, kuma ya sa ta rage yawan ma’aikatanta da mutum 63, ciki har da na ’yan jaridarta da suka ragu daga 55 zuwa 20.

Ana sa ran dai za a ci gaba da wallafa jaridar ne a intanet kawai, kodayake za a rika ci gaba da sayar da kwafin ta ta intanet din ga masu karatu ta yadda za a ci gaba da samun kudaden shiga.

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano

Ɗan Gwamnan Jigawa ya rasu kwana guda bayan rasuwar mahaifiyarsa

Mutum 38 ne suka mutu a haɗarin jirgin sama a Kazakhstan