Shugaban Karamar Hukumar Kala Balge Ya Koma Gida Bayan Shekara 10
Shugaban Karamar Hukumar Kala Balge na yanzu, Ajid Musa Ajid, ya koma Rann Hedikwatar yankin bayan shafe shekaru 10 da ya yi kaura a sakamakon rikicin Boko Haram. Shugaban karamar hukumar Ajid ya samu rakiyar mataimakinsa, Hakimin Rann, wakilin Hakimin Kala, DPO na ’yan sanda da jami’an Civilian JTF da dai sauransu. Ajid ya bayyana […]
Shugaban Karamar Hukumar Kala Balge na yanzu, Ajid Musa Ajid, ya koma Rann Hedikwatar yankin bayan shafe shekaru 10 da ya yi kaura a sakamakon rikicin Boko Haram.
Shugaban karamar hukumar Ajid ya samu rakiyar mataimakinsa, Hakimin Rann, wakilin Hakimin Kala, DPO na ’yan sanda da jami’an Civilian JTF da dai sauransu.
Ajid ya bayyana farin ciki da shiga garin ba tare da wata barazana ta tsaro ba.
“Bayan shekaru 10 ba tare da sanin halin da garinmu yake ciki ba, yau mun shiga Kala Balge ba tare da wata barazanar tsaro ba,” in ji Ajid.
- ’Yan ɗarikar Tijjaniya sun yi wa Sarki Sanusi II mubaya’a
- Masu kamun kifi da ISWAP ta kashe a Borno sun karu zuwa 31
Da ya shiga garin na Rann ya yi jawabi ga al’ummar yankin, inda ya ce, ‘Ina so in gaya wa mutanenmu, ciki har da wadanda suka yi gudun hijira na tsawon shekaru, su kwantar da hankalinsu.
“Na ga halin da ake ciki a garinmu kuma zan sanar da gwamna cikin gaggawa don yin wani abu a kai cikin lokaci.
“Za mu komo karamar hukumarmu da zama daram nan ba da dadewa ba don cigaba da gudanar da mulki kamar yadda yake a baya in Allah Ya so.”
Shugaban ya amince da kokarin da gwamnatin jihar ke yi na tsugunar da ’yan gudun hijirar, ya kuma yi alkawarin sanar da gwamnan irin ci gaban da aka samu a garin na Rann dangane yadda yanayin zaman lafiya ya Kankama tare da taimakon Allah da Kuma jajircewar jami’an tsaro.
“Duk da damina ta gabato, za a sake tsugunar da al’umma tare da kula da su don a ci gaba da noma da sauran ayyukan da za a bunkasa tattalin arzikin garinmu da jiharmu bayan damina.”
Ita wannan karamar hukuma ta Kala Balge dai na a gabashin jihar Borno, kusa da kasar Kamaru wato tana kan iyaka.