Bayan shekara 32 Medico ta sake fama da mummunar girgizar kasa
Tun Larabar da ta gabata ake ta aikin ceton mutanen da mummun ar girgizar kasa ta rutsa da su a kasar Medico, inda a kalla mutum 217 suka mutu a daidai kwatankwacin lokacin zagayowar irin wannan girgiza mai muni da kasar ta yi fama da ita a baya. Tun daga shekarar 1985 da aka yi […]

Tun Larabar da ta gabata ake ta aikin ceton mutanen da mummun ar girgizar kasa ta rutsa da su a kasar Medico, inda a kalla mutum 217 suka mutu a daidai kwatankwacin lokacin zagayowar irin wannan girgiza mai muni da kasar ta yi fama da ita a baya.
Tun daga shekarar 1985 da aka yi fama da mummunar girgizar kasa a kasar Medico lamarin bai sake rincabewa said a shekara 32 suka cika bayan da ranar ta kewayo.
Babban tashin hankalin shi ne yaddda girgizar ta rufta da wata makaranta a babban birnin kasar, inda yara 21 da manya biyar suka mutu, tare da wasu 30 da suka bata.
“Babu wanda ya san irin radadin da nike ji a halin yanzu,” a cewar wata uwa, Adriana Fargo, wadda ta tsaya a gaban makarantar tna jiran labarin ’yarta ’yar shekara bakwai.
Hankalin kasar ya koma kan makarantar elemantare ta Enrikue Rebsamen da kuma wata karamar sakandfare da ke kudancin birnin Medico.
daruruwan sojoji da ‘’yan sanda da masu aikin sa-kai na ta fafutikar ture buraguzan tun cikin dare don tono malami da dalibai biyu, wadanda aka ceto su da ransu.
Shugaban kasa Enrikue Pena Nieto, wanda ya yi hanzarin zuwa wajen da girgizar ta auku ya yi gargadin cewa akwkai yiwuwar karuwar adadin wadanda suka mutu. Tuni ake ta zartgin munin al’amarin ya kazance a gine-ginen makarantun kasar wadanda ba su da nagarta. kasar Medico ta hadu da mummunar girgizar kasa wadda ta yi sanadiyyar rasa rayukan daruruwan mutane. Munin girgizar kasar ya sanya ana ta fafutikar kwashe majinyata daga asibitocin kasar.