Bayan shekara 50 da rasuwar Sardauna

Hakika mutuwar rigar kowa. A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah, yau shekaru hamsin kenan da rasuwar Sir.Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto. Tabbas ! Rasuwar shi babban gibi ne a kasar mu, wanda kuma har yanzu ba mu cike wannan gibi ba. Kamar yadda tarihi ya nuna an haifi Sa Ahmadu Bello a ranar […]

Bayan shekara 50 da rasuwar Sardauna
Bayan shekara 50 da rasuwar Sardauna

Hakika mutuwar rigar kowa. A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah, yau shekaru hamsin kenan da rasuwar Sir.Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto. Tabbas ! Rasuwar shi babban gibi ne a kasar mu, wanda kuma har yanzu ba mu cike wannan gibi ba. Kamar yadda tarihi ya nuna an haifi Sa Ahmadu Bello a ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1910 a wani gari da ake kira Rabba a cikin Jihar Sakkwato da ke Arewacin Najeriya. Kakan sa shi ne, Sarkin Musulmi Malam Bello, wanda ya kasance daya daga cikin mutanen da suka kafa daular Musulunci ta Sakkwato a wancan karnin. Kuma shi da ne ga Margayi Mujaddadi Shehu Usman danfodiyo.
Margayi Ahmadu Bello ya fara yin karatun sa a garin su na Sakwato sannan ya wuce zuwa Makarantar horar da Malamai da ke cikin birnin Katsinan Dikko. Daga bisani Sultan na Sakkwato ya nada shi Malamin Makarantar Middle School da ke Sokoto. A shekarar 1938 aka nada shi Sardaunan Sakkwato bayan da ya gaza cimma kudurin sa na ganin ya zama Musulmi a lokacin.
Haka kuma ya halarci  kwasa-kwasai a Ingila da ke kasar Birtaniya, domin yin karatun da ya shafi sanin harkokin mulki a shekarar 1948. Sannan ya kuma fara shiga harkokin siyasa gadan-gadan ne bayan dawowar sa daga karatun, inda har aka zabe shi ya zamo Mamba a Majalisar dokoki ta  Arewacin Najeriya. Kuma ya zama Ministan ayyuka da raya kasa.
Bugu da kari Ahmadu Bellon ya kasance Firimiya na farko a yankin Arewa daga Shekara ta 1954 zuwa 1966. Kazalika Sardaunan Sakkwato (Gamji dankwarai) Ya kuma jagoranci Jam’iyyar su ta NPC, wadda ta samu nasarar lashe kujeru da dama a zaben da aka gudanar bayan samun yancin kai a lokacin.Sannu a hankali bayan kammala zaben ya zabi ya ci gaba da kasancewar sa a matsayin Firimiya, inda ya nada Sa Abubakar Tafawa balewa ya zamo FiraMinista a lokacin.
Hakika Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto Gamji dankwarai ya taka rawar gani sosai, wadda har yanzu ba mu sami wanda ya dan kwatan ta irin hobbasar da ya yi ba.Sardaunan ya yi rawar ganin sosai musam man wajen hada kan yankin Arewacin kasar nan, wadda ke da dimbin mabiya addinai iri daban-daban.Ya kuma aiwatar da dimbin ayyukan ci gaban kasa. Yana cikin wannan namijin kokari ne duniya kuma tana matukar farin ciki da irin ayyukan alherin da ya samar wa kasa.S ai dai kash! Yayin da duniya take ganin kokarin sa a she wasu su kuwa suna can suna kokarin raba shi da duniyar, inda suka yi kokarin hallaka shi ta hanyar yi masa mummunan juyin mulki, wanda aka yi sanadiyar rasuwar sa !
Juyin mulkin dai wasu ’yan kabilar Igbo ne suka jagorance shi a gidan sa da ke Kaduna.  A ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966.
A karshe ina rokon Allah Ubangiji ya jikan sa da rahama, Ya kuma kyautata karshen mu. Da fatan shugabannin mu na wannan zamanin za su rika kwatanta ayyukan alherin da ya samar ba wai ado ko amfani da sunan sa kawai ba.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno