Bayan shekara 62 Masarautar Ningi ta samu Waziri

Masarautar Ningi ta naɗa sabon Wazirin Ningi bayan shekara 62 da dakatar da sarautar.

Bayan shekara 62 Masarautar Ningi ta samu Waziri

Masarautar Ningi da ke Jihar Bauchi ta naɗa sabon Wazirin Ningi bayan shekara 62 da dakatar da sarautar.

Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya, ya naɗa tsohon Jakadan Najeriya a kasar Qatar, Ambasada Shuaibu Ahmed Adamu, a matsayin Wazirin Ningi na huɗu.

Shekarar 1961, wata takaddama ta sa Gwamnatin Jihar Arewacin Najeriya ta dakatar da Wazirin Ningi, Ali Waziri, wanda shi  ne shugaban majalisar masu naɗin sarki a masarautar.

A halin yanzu Wazirin Ningi na Hudu shi ne Shugaban Majalisar Binciken Kuɗi ta Najeriya.

Da yake jawabi a bikin naɗin Wazirin, Sarkin Ningi Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya, ya ce an saɓo Adamu ne saboda gogewarsa da kuma yadda yake hidimta wa al’umma da kuma gudummawarsa ga Masarautar Ningi.

Ya ce Waziri, wanda shi ne shugaban majalisar naɗin sarki a masarautar, yana da matuƙar tasiri a tsarin gudanarwar masarautar.

A nasa jawabin, Wazirin Ningi Ambasada Shuaibu Ahmed Adamu, ya yi alkawarin amfani da ƙwarewarsa wajen tabbatar da wanzuwar aminci da cigaba masarautar.

Tinubu zai tafi Faransa daga nan ya zarce Habasha

NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana

Jami’ar ABU da ke Zariya ta yi sabon shugaba

An soma rigimar haraji tsakanin China da Amurka