Bayan shekara 9, kotu ta wanke Sule Lamido da ’ya’yansa daga zargin almundahana

Kimanin shekara 9 ke nan ana fafata shari’a a kan lamarin

Bayan shekara 9, kotu ta wanke Sule Lamido da ’ya’yansa daga zargin almundahana

Sule Lamido tare da dansa, Mustapha

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja a ranar Talata ta wanke tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido da ’ya’yansa biyu daga zargin rub da ciki a kan wasu kudade.

Kotun, wacce Mai Shari’a Adamu Waziri yake jagoranta, ta ce Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ba ta da hurumin sauraron karar da aka shigar mata kan batun tun da farko, saboda kusan dukkan abubuwan da ake karar a kansu a wajen yankinta aka aikata.

Babbar kotun dai ta ki amincewa da karar da aka shigar gabanta a kan batun tun da farko.

Daga nan ne Lamido ya daukaka karar a gaban kotun yana kalubalantar hukuncin da kotun baya ta yanke.

An dai gurfanar da Lamido ne a gaban Mai Shari’a Adeniyi Ademola bisa zarge-zarge 43 a shekarar ta 2016, wadanda suka shafi hada baki da kuma wasa da aiki kan kudin da suka kai Naira biliyan 1.351.

An dai gurfanar da shi ne tare da ’ya’yansa biyu, Aminu da Mustapha, wanda shi ya yi wa PDP takarar Gwamnan Jigawa a 2023, sai kuma Wada Abubakar da kuma wasu kamfanoni guda hudu.

Kamfanonin sun hada da Baimana Holdings Ltd da Bamaina Company Nigeria Ltd da Bamaina Aluminium Ltd da Speeds International Ltd da kuma Batholomew Darlington Agoha.

Kimanin shekara tara ke nan ana tafka shari’a a kan lamarin.