Bayan shekaru 28, an kammala aikin matatar ruwa ta Zobe a Katsina
Har yanzu da sauran aiki bayan kamala aikin da ya shekara 30 yana tafiyar hawainiya.
Me zai sa gwamnati ta shafe shekara 28 ba tare da kammala wani aiki da ta fara ba? Rashin muhimmancinsa ne ko rashin kudin aiwatar da shi? In kuma akwai to me ya faru da kudaden da gwamnatocin tarayya da na jiha suka narka a kan wannan aiki cikin tsawon wannan lokaci?
Wadannan su ne tambayoyi da ake ta yi game da aikin samar wa birnin Katsina da wasu garuruwa da ke kewaye da shi ruwan sha daga babbar madatsa ruwa ta Zobe.
- Yadda mutanen gari suka kama ’yan bindiga a Zariya
- Sojoji sun kama makamai a fadar sarakunan Binuwai
- Sana’ar wankin mota ta fi min komai —Matar aure
Aikin daya ne daga cikin Ayyukan Samar wa Birane Ruwan sha na Gwamnatin Tarayya wanda a karkashinsa aka tsara sama wa Jihar Katsina akalla kashi 50% na tsaftataccen ruwan sha.
Aiki da aka fara shi tun a shekarar 1992 ya yi ta tafiyar hawainiya na kusan shekara 30, saboda rashin kudi da rashin ingattun tsare-tsaren da hangen newan shugabanni da kuma rashawa.
A cikin shekara ta 1970, gwamnatin mulkin soja ta Obansanjo ta fara tunanin gina madatsar ruwa ta Zobe.
Amma Gwamnatin Shugaban Kasa Shehu Shagari ita ce ta gina shi sannan Shagari ya kaddamar da shi a 1983.
Manufar gina dam din na Zobe ita ce bunkasa harkokin noman rani da samar da ruwan sha da kuma samar da wutar lantarki.
Sai dai kuma shekara 38 bayan kaddamar da wannan babbar madatsar ruwa mai iya ba wa kadada 10,000 ta noman rani, sam ba a amfana da shi yadda ya kamata.
Dam din da a wancan lokacin aka gina shi kan Naira 50,000,000,000 a halin yanzu ayyukan da yake yi ba su kai suka kawo ba.
Binciken Aminiya ya gano cewa bangaren madatsar ruwan ta Zobe masu bisan mita 9 da kuma tsawon mita 2,750 suna nan daram-dam.
Amma kuma babu cikakkun ayyukan noman rani masu yawa da suke gudana a yankunan wannan dam.
Sannan har yanzu ba a sanya ko da dambar wani aiki ba don samar da wutar lantarki a ciki ko gabar madatsar ruwan.
Haka kuma Aminiya ta gano yadda dam din yake ta cikewa ta wani bangarensa daga Gabas.
Dam din ya cike da kimanin fadin mita 300,000 wanda kuma tuni mazauna kauyukan da ke kewaye da wurin suka mayar da sashen da ya cike din gonaki.
Shin mazauna Katsina sun fuskanci karancin ruwan sha a tsawon wannan lokaci?
Musa Dahiru, mazaunin Unguwar Sabon-layi da ke cikin birnin Katsina ya bayyana wa Aminiya cewa kafin a kammala aikin samar da ruwa daga Zobe a bara, sun yi shekaru da dama suna fuskantar matsalar ruwan sha.
“Tun fiye da shekara 15 nake sayen ruwa daga ‘yan ga-ruwa a kullum don yin amfani a gida.
“Kusan kullum sai na sayi akalla jarka 10. Amma yanzu Alhamdulliah, muna samun ruwan famfo akai-akai.”
Haka shi ma Malam Adamu da yake zaune a Tsohuwar Tasha cikin garin Katsina, ya tabbatar wa Aminiya cewa tun daga bara, suna samun ruwa akalla sau uku a mako.
Adamu ya ce, “Ana kawo ruwa sau ukku a mako. Sai dai ya kamata su kara kaimi don ganin muna samun ruwan a kowace rana.”
Kwamishina Albarkatun Ruwa na Jihar, Musa Adamu Funtua ya bayyana wa Aminya cewa duk da yake cewa abin takaici ne yadda wannan aiki na samar da ruwan sha daga Madatsar ruwa ta Zobe ya dauki dogon lokaci, amma daga karshe dai gwamnatin jihar ta samu nasarar kammala shi.
Ya ci gaba da cewa sun samu nasarar kammala aikin jawo ruwan ne bayan da Gwamnatin Jihar ta hada karfi da karfe da Gwamnatin Tarayya.
“Na yarda cewa shi kansa Dam din Zobe ba a aiki da shi yadda ya kamata ballantana dubban jama’a su ci gajiyarsa yadda ya dace.
“Haka kuma abin takaici ne yadda wannan aiki na jawo ruwa daga Zobe Zuwa Dutsin-ma da kuma birnin Katsina ya dauki shekaru da yawa ana yin sa.
“Sai dai wannan ya faru ne saboda yadda gwamnatocin baya suka yi ta kwan-gaba-kwan-baya da aikin.
“Kowace gwamnati idan ta zo, a maimakon ta ci gaba daga inda wadda ta gada ta tsaya, sai ita ma ta fito da nata sabon aikin.
“Sai dai wani abu guda shi ne, dukkaninsu suna da muradin ganin an kamala aikin. Wannan shi ne dalilin da ya sanya aka dauki shekaru masu yawa ba tare da kamala aikin ba,” inji shi.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa “Haka aka yi ta yi har ya zuwa lokacin da marigayi ’Yar’adu ya dawo karo na biyu a kujerar gwamna inda ya yanke shawarar fadada aikin jawo ruwan a mataki na farko kashi na biyu wato Phase 1b, wanda ya hada da Kafin-Soli da sauran garuruwan da suke a waccan shiyyar.
“Amma dai in gajarce maka labari, maganar nan da nake da kai a yanzu tuni haka ta cimma ruwa, wato Gwamnatin Jihar Katsina ta hada karfi da karfe da Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Kasa kuma mun samu nasarar kammala aikin jawo ruwa daga Zobe zuwa Katsina da Dutsin-ma, wanda shi ne muke kira phase 1a.”
Adamu Funtuwa ya kara da cewa, “Wannan aiki an kamala shi dari bisa dari. Kuma mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Honarabul Aminu Bello Masari tuni ya kaddamar da shi ya kuma mika wa Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Jihar Katsina hakkin ci gaba da gudanar da al’amuransa, wanda kuma muke yi don inganta rayuwar al’umma.”
Sai yaushe za a kammala aikin kashi na biyu, ko sai an sake jiran wasu shekaru 28 nan gaba?
Adamu ya yi wa Aminiya karin bayanin cewa a halin yanzu gwamnatin jihar ta sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakaninta da Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Kasa kan kammala aikin jawo ruwa daga Zobe wanda zai ratsa Dutsin-ma zuwa Kafin-Soli da sauran garuruwan.
Ya kuma tabbatar da cewa aikin ba zai dauki lokaci mai yawa ba.
Shin matatar tana samar wa birnin Katsina yawan ruwan shan da mazaunansa suke bukata a kullum?
Shugaban Hukumar Ruwa ta Jihar Ibrahim Dasuki Abubakar ya bayyana cewa a halin yanzu matatar ruwan ba ta iya samar da yawan ruwan da mazauna Katsina suke bukata a kullum.
Dasuki ya ce, “A halin yanzu birnin Katsina kawai a kullum yana bukatar a ba shi litar ruwa har 130,000,000.
“Shi kuma Dam din Zobe a halin yanzu yana iya tacewa tare da turo wa Katsina litar ruwa 40,000,000 a kullum ne kawai.
“Sannan kullum yana tura wa Dutsin-ma litar ruwa 5,000,000. Haka ma garin Katsina a kowace rana yana samun litar ruwa 35,000,000 daga Dam din Ajiwa.
“Don haka, a takaice, idan ka hada ruwan da ke shigowa daga Zobe da wanda yake zuwa nan Katsina daga Ajiwa.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa muka yi tsari na shiyya-shiyya na ba da ruwa a cikin garin Katsina – inda za ka ga in yau an ba wa wadannan unguwanni, gobe kuma sai a ba wa wasu.
“Wannan tsari haka ake yin sa a ko ina ka je, saboda zai yi wuyar gaske ka samu kasar da take samar wa jama’a yawan ruwan da suke bukata a kullum,” a cewar Dasukki.
Kalubale
Ya ci gaba da cewa babban kalubalen da ma’aikatarsa take fuskanta a yanzu shi ne na rashin wutar lantarki.
“Ka san kalubale ba ya karewa a rayuwa. Akwai kananan kalubale na gyaran tsoffin bututan ruwa da suka dade a kasa.
“Amma dai a halin yanzu kalubalen da muke fuskanta wajen ayyukan samar da ruwan sha daga Zobe da ma Ajiwa, bai wuce na wutar lantarki ba, domin har yanzu wuta ba ta da tabbas.
“Kana iya ganin an kawo ta amma kuma sai ka tarar ba ta da karfin da za ta iya daukar wasu injinanmu.
“Amma Alhamdulillahi, gwamnati na kan kokarin ganin ta kauda wannan matsala, musamman ma a can Ajiwa inda tuni Gwamnatin Jiha ta sanya hannu kan yarjejeniya da wani kamfani da zai kawo tare da sanya wata na’urar wutar lantarki mai karfin 7.5 MGA wacce za ta taimaka wajen kara karfin wutar ta yadda ko da an kawo wuta ba karfi za ta karfafata ta yadda injinanmu za su iya aiki da ita,” inji shi.
Shin Dam din na da ingantattun kayan aiki na zamani?
Shugaban Madatsar Ruwa ta Zobe, Abubakar Ibrahim wanda ya zagaya da Aminiya ciki da wajen Dam din ya bayyana cewa ma’aikatar cike take da sabbin kayan aiki na zamani da za a ci gaba da cin gajiyarsu nan da shekaru masu yawa a gaba.
“Kamar yadda ka gani da idanunka, duk injina da kuma na’urorin da suke a wajen nan sabbi ne fil. Haka kuma ka ga yadda shi ma Dakin-Gwaje-gwajenmu yake na zamani.
“Wannan shi ne dalilin da ya sanya na fada maka [cewa] wannan matatar ruwan tana daya daga cikin manyan matatun ruwa na zamani da ake da su yanzu a Najeriya.
“A nan muna aiki ne ba dare ba rana. Kuma akullum muna tura wa birnin Katsina da garin Dutsin-ma tataccen ruwan sha lita 45,000,000.”