Bayan shirin dakarun Nukiliyar Rasha, Zelensky ya je Amurka
Wannan dai ita ce ziyarar Zelensky ta farko zuwa wata kasa domin neman dauki, tun bayan da Rasha da auka wa kasarsa da yaki, sama da kwana 300 da uska gabata.
Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya kai ziyara Amurka don neman dauki bayan takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, ya sanar cewa dakarun rundunar nukilyar kasarsa na cikin shirin yaki.
Wannan dai ita ce ziyarar Zelensky ta farko zuwa wata kasa domin neman dauki, tun bayan da Rasha da auka wa kasarsa da yaki, sama da kwana 300 da uska gabata.
- Dokar Cire Kudi: Emefiele ba zai bayyana gaban Majalisa ba
- Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Gambiya
Wani bidiyonsa da aka fitar ya nuna shi a tashar jirgin kasa da rakiyar motoci a kasar Poland, makwabciyar kasarsa.
A yayin da yake hanyarsa, Zelensky ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa zai yi amfani da damar wajen kara karfin tsaron kasarsa.