Bayan sulhu: Ali da Zango sun fito a fim din ‘Akasi’
Tun lokacin da fitattun jaruman fina-finan Hausan nan Ali Nuhu da Adam A. Zango suka samu sabanin da har ta kai da sun raba gari da kuma sulhun da aka yi cikin azumin da ya gabata, masu sharhi kan al’amuran da ke faruwa a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood suka rika tofa albarkacin bakinsu cewa, […]
Tun lokacin da fitattun jaruman fina-finan Hausan nan Ali Nuhu da Adam A. Zango suka samu sabanin da har ta kai da sun raba gari da kuma sulhun da aka yi cikin azumin da ya gabata, masu sharhi kan al’amuran da ke faruwa a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood suka rika tofa albarkacin bakinsu cewa, wannan sulhun ba zai je ko’ina ba. Wadansu daga cikin masu sharhi a masana’antar sun rika cewa Ali Nuhu yana son Zango ya ci gaba da yi masa biyayya ne, shi kuma Zango yana ganin yanzu ya fi karfin a ce zai ci gaba da yi wa wani biyayya a masana’antar, kuma hatta ’yan fim da dama sun rika nuna shakku kan dorewar sulhun jaruman.
Furodusa AbdulRahman wanda aka fi sani da Abdul Amart na daya daga cikin wadanda suka yi uwa da makarbiya wajen ganin an sulhunta jaruman biyu, inda shi ne ma ya dauki nauyin sulhu ta hanyar kama otel din da aka yi sulhun a Kaduna a cikin azumin da ya gabata.
Furodusan ya bayyana wa Aminiya bayan da aka yi sulhun cewa ya ji irin shakkun da jama’a suke nunawa game da sulhun, musamman ganin cewa an shirya za a yi buda-baki a gidajen jaruman amma hakan bai yiwu ba. Ya ce hakan ya sanya ya rika tunanin yadda zai nuna wa duniya cewa sulhun da aka yi yana nan daram, ba zai rushe ba. Ya ce domin tabbatar da haka ne ya sa ya shirya wa jaruman sabon fim a karkashin kamfanin Abnur Entertainment mai suna ‘Akasi.’
Ya ce: “Muna so mu nuna wa duniya cewa abin da ya faru ya wuce, sai na ce me zan yi a matsayina na furodusan da ya jagorancin sulhunta jaruman biyu don in kara dankon zumunci a tsakaninsu. Hakan ya sanya na shirya wannan aikin, muka hada su. Ko a Kannywood wasu ba su gamsu da sulhun ba, amma ganinsu a wannan lokeshin, suna wasa da dariya kamar babu abin da ya faru, sai suka sallama, wanda hakan ba karamin alheri ba ne ga Kannywood.”
Furodusan ya nanat kyakkyawar dangatakar da ke tsakanin jaruman biyu a yanzu ta fi ta da danko da karfi. “Duk yadda kuke idan ba a haduwa sai a ga kamar babu zumunci ko kyakkyawar dangantaka, amma idan aka kusanci juna, sai ka ga an magance kananan maganganu. A yanzu kyakkyawar dangantaka a tsakanin Ali da Adamu ta fi da, wadanda suka ga yadda suka yi aikin fim din ‘Akasi’ za su tabbatar da hakan. Hadin kan jaruman alheri ne ga Kannywood,” inji shi.
Da aka tambaye shi matsayin da kowa ya taka a fim sai ya ce Ali Nuhu ne babban jarumin fim din, sai Zango ya tallafa masa duk da cewa kowa ya san Zango ne babban jarumin kamfaninsu.
Ya ce “Fim din ya zo da sabon abu, domin Ali dan kwangila ne, kuma shi ne ya jagoranci fim din, inda Adam Zango ya tallafa masa, mutane za su yi mamakin dalilin da ya sa muka sanya Ali Nuhu matsayin jagoran fim din musamman ganin an san cewa fina-finan kamfaninmu Adamu ne babban jarumi, to abin da nake so in kara fada wa mutane shi ne, rol din ne ya kira Ali, haka shi ma rol din ne ya kira Zango, kuma Zango bai yi korafi kan hakan ba, sannan Ali bai yi alfahari da hakan ba.”
Furodusan ya bayyana cewa jigon fim din a kan siyasa ne, sannan yana dauke darussan da za su zama hannunka mai sanda ga ’yan siyasa da kuma yaransu. “Ya kuma fadakar kan yadda wadansu tsirari suke amfani da matsayinsu wajen kuntata wa mutane.”
Fim din ‘Akasi’ wanda aka kammala daukarsa a Kaduna a ranar Lahadin da ta gabata, kamfanin Abnur Entertainment ya dauki nauyin shirya shi, inda Abdul Amart ya shirya shi, Nura M. Inuwa ya dauki nauyi, Falalu dorayi kuma ya ba da umarni.
’Yan wasan da suka fito a cikinssa sun hada da Ali Nuhu da Adam A. Zango da Jamila Nagudu da Nafisa Abdullahi da Baban Chinedu da Suleiman Bosho da Mustapha Naburaska da Aina’u Ade da Baban Mulika da sauransu.