Bayan tsare shi na awa 15 El-Rufa’i ya ce: Ba za mu bari a zare mana ido baBayan tsare shi na awa 15 El-Rufa’i ya ce: Ba za mu bari a zare mana ido ba
Mataimakin Sakataren Jam’iyyar APC, Malam Nasir El-Rufa’i ya ce ba za su bari gwamnati ta zare musu ido ba ta hanyar yi musu barazana.Tsohon Ministan Abuja Malam Nasir El-Rufa’i ya rubuta hakan a shafinsa na tiwita, inda ya zargi Gwamnatin Tarayya da kokarin razanar da su don ta samu sukunin gudanar da magudin zabe a […]
Mataimakin Sakataren Jam’iyyar APC, Malam Nasir El-Rufa’i ya ce ba za su bari gwamnati ta zare musu ido ba ta hanyar yi musu barazana.
Tsohon Ministan Abuja Malam Nasir El-Rufa’i ya rubuta hakan a shafinsa na tiwita, inda ya zargi Gwamnatin Tarayya da kokarin razanar da su don ta samu sukunin gudanar da magudin zabe a badi.
Ya caccaki gwamnatin ne kwana daya bayan da ya amsa gayyatar hukumar tsaron kasa ta (SSS) inda ya kwashe sa’o’i 15 a hannunta yana amsa tambayoyi.
Hukumar ta SSS ta gayyaci Malam El-Rufa’i ne domin amsa tambayoyi game da kalamin da aka rawaito ya ce ana iya samun tashin hankali matukar ba a yi adalci a zaben badi ba.
El-Rufa’i ya ce wannan zance ba ingiza tashin hankali ba ne, illa tunatarwa game da irin rikice-rikicen da suka biyo bayan zabubbukan da aka gudanar a baya.
Jam’iyyar APC ta yi Allah wadai da gayyatar ta SSS, inda ta yi zargin cewa gwamnati na amfani da jami’an tsaro da nufin karya-lagon ’yan adawa
A ranar Litinin da ta gabata ce Malam Nasiru El-Rufa’i ya amsa gayyatar Hukumar SSS, inda ya kai kansa hedkwatar hukumar SSS da misalin karfe 9:00 na safe tare da rakiyar Gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi da Sanata Chris Ngige da wasu mabobin Jam’iyyar APC, kuma ba a sako shi ba sai misalin karfe 12:35 na dare kamar yadda wani amininsa MuyiwaAdekeye ya fadi a tiwitarsa.
Da farko jami’an SSS sun je gidansa da ke Abuja amma ba su iske shi ba, inda aka shaida musu ya je dauko ’ya’yansa daga makaranta, daga nan ne suka shiga wasan buya kafin ya mika wuya ga hukumar.
Kafin ya bar gidansa El-Rufa’i ya shaida wa manema labarai cewa babu wata musgunawa da za ta hana shi bayyana gaskiya. Ya ce lura da halin Jam’iyyar PDP, idan ba a yi zabe na gsakiya ba babu wanda zai iya ba da tabbacin ba za a samu tashin hankali ba a badi.
Gwamna Rotimi Amaechi wanda ya tuka El-Rufa’i zuwa hedkwatar SSS ya shaida wa manema labarai cewa babu abin da zai hana ’yan adawa daga yin magana kan abin da ya kira zaluncin da ke gudana.