Bayan wata 2: Barayi sun ki sakin mahaifiyar Siasia duk da ya biya Naira Miliyan 1.5

Tsohon Kocin Najeriya Super Eagles Samson Siasia ya bayyana takaicinsa kan yadda duk da ya biya Naira miliyan daya da rabi a matsayin kudin fansa wadanda suka yi garkuwar da mahaifiyarsa sun ki sako ta bayan wata biyu da sace ta. A tattaunawar da ya yi da manema labarai a ranar Lahadin da ta wuce, […]

Bayan wata 2: Barayi sun ki sakin mahaifiyar Siasia duk da ya biya Naira Miliyan 1.5

Tsohon Kocin Najeriya Super Eagles Samson Siasia ya bayyana takaicinsa kan yadda duk da ya biya Naira miliyan daya da rabi a matsayin kudin fansa wadanda suka yi garkuwar da mahaifiyarsa sun ki sako ta bayan wata biyu da sace ta.

A tattaunawar da ya yi da manema labarai a ranar Lahadin da ta wuce, Siasia ya ce abin yana matukar tayar masa da hankali ganin yadda duk da amincewar da suka yi na karbar Naira miliyan daya da rabi amma sun ki sako ta.

Mahaifiyarsa mai suna Madam Beauty Ogere, kimanin wata biyu ke nan da yin garkuwa da ita a Jihar Bayelsa amma har rubuta wannan kabari ba su sake ta ba.  Kimanin shekara biyu da suka wuce an taba yin garkuwa da ita inda aka biya Naira dubu 600 kafin a sako ta.

An kama Madam Ogere ce tare da wadansu mata biyu. Daya budurwa ce dayar kuma mai shekara 66 mai suna Madam Florence Donana kuma suruka ce ga kawun Siasia.

Sai dai a lokacin da wanda ya kai kudin fansar mahaifiyar Siasia, maimakon su sake ta sai shi ma suka yi garkuwa da shi sannan suka saki Madam Florence.

“Yanzu maganar da ake yi, mahaifiyata da wata budurwa da wanda ya kai kudin fansar suna can a tsare a wajensu,” inji Siasia.

Siasia ya nemi taimakon jami’an tsaro kan su yi kokarin kwato mahaifiyarsa tare da  sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.