‘Bayan wata uku da biyan fansar Naira miliyan 1.2 har yau ba a sako mahaifinmu ba’
Yaushe aka sace mahaifinku, kuma me ake ciki a yanzu? A ranar 10 ga watan Nuwamban bara ne aka sace mahifinmu Alhaji Tijjani Abdullahi Muhammad mai shekara 58 a kan hanyar Jos zuwa Pambeguwa zuwa Zariya. Ranar ya yi mana waya cewa ya taso a motar haya, amma bai iso gida yadda ya saba ba, […]

Yaushe aka sace mahaifinku, kuma me ake ciki a yanzu?
A ranar 10 ga watan Nuwamban bara ne aka sace mahifinmu Alhaji Tijjani Abdullahi Muhammad mai shekara 58 a kan hanyar Jos zuwa Pambeguwa zuwa Zariya. Ranar ya yi mana waya cewa ya taso a motar haya, amma bai iso gida yadda ya saba ba, inda duk muka shiga damuwa matuka. Mun kira wayarsa amma ba ta shiga, daya daga cikin ’ya’yansa mai suna Hauwa A. Tijjani ta ce da gari ya waye wato ranar Asabar, sai aka kira wayarta aka ce an yi garkuwa da mahaifinsu sai sun biya kudin fansa.
Nawa suka ce ku biya?
Sun ba mahaifinmu waya an yi magana da shi, suka ce a kawo kudin fansa Naira miliyan 16 amma aka yi ta ciniki da su har suka yarda a kawo Naira miliyan daya da dubu 200.
A ina mahaifinku yake aiki?
Mahaifinmu yana aiki ne a Cibiyar Horar da Ma’aikata ta kasa (ITF) da ke Jos a Jihar Filato. Shekarunsa 58, yana da mata biyu da ’ya’ya shida da jikoki uku.
Yaya aka yi wajen bayar da kudin fansar?
Mu da abokan aikinsa da suke ofishinsu muka hada Naira miliya daya da dubu dari 200 muka bai wa wani dan uwanmu ya nufi hanyar Pambeguwa daga Zariya suka yi ta waya da masu garkuwa da mutanen har suka hadu, da ya mika wa wani daga cikinsu kudin, sai ya kira wani ya shaida masa an kawo kudin, sannan ya ce masa ya koma gida ya jirayi dawowar mahaifinmu sumui lumui. Kuma ya ce su Fulani ne masu fada da cikawa, domin haka kada a damu.
Yaushe aka biya kudin fansar?
An biya kudin fansar ne ranar 19 ga Nuwanban bara, wato kwana tara bayan da aka yi garkuwa da shi. Amma yanzu wata uku ke nan da wasu kwanaki sai addu’a kawai muke yi domin ba a ji duriyarsa ba, kuma wayarsa da wadda aka yi ta musayar waya da masu garkuwa da mutanen duka ba sa zuwa.
A ina aka karbi kudin?
A wani kauye ne mai suna Yari da ke kusa da garin Pambeguwa a Jihar Kaduna.
Ko kun sanar da hukuma abin da ke faruwa?
Da farko an taru a kan cewa kada mu sanar da hukumar saboda tsoron kada su kashe shi. Amma daga baya mun fada wa Rundunar ’Yan sanda a Zariya inda suka ce za su bincika, amma har yanzu ba mu ji komai ba.
Wane mataki kuka dauka bayan haka?
Mun koma kauyen na Yari da ke kusa da Pambeguwa inda muka yi ta tambayar mutane, amma suka ki cewa uffan domin suna jin tsoro.
Shin me ofishin da yake aiki suka yi?
Abokansa sun ba da gudummawar kudi daga aljihinsu, amma sun ce ba wata dokar gwamnati da ta yarda a dauki kudin hukuma domin biyan fansar ceton wanda aka yi garkuwa da shi.
Me kuke fata gwamnati ta yi don ceto mahaifinku?
Muna rokon a taimaka mana domin a gano shi da kuma fatan a karfafa tsaro a Jihar Kaduna da kasa baki daya.