Bayan zabe, mu hada kai mu zauna lafiya – Yan Arewa Mazauna Jihar Edo
Al’ummar Arewa mazauna Jihar Edo suna ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu da bayar da shawarwari ga sabuwar gwamnati da za a shiga inuwarta nan da makwanni masu zuwa. A cikin wadanda wakilin Aminiya ya zanta da su bayan kammala zaben gwamnoni da wakilan majalisun dokoki na jihohi da ya gudana a makon jiya, akwai mai […]
Al’ummar Arewa mazauna Jihar Edo suna ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu da bayar da shawarwari ga sabuwar gwamnati da za a shiga inuwarta nan da makwanni masu zuwa.
A cikin wadanda wakilin Aminiya ya zanta da su bayan kammala zaben gwamnoni da wakilan majalisun dokoki na jihohi da ya gudana a makon jiya, akwai mai ba Gwamnan Jihar Edo shawara a kan harkokin da suka shafi al’ummar Arewa mazauna jihar, Alhaji Sahabi Aliyu Umar (JP). Da yake tofa albarkacin bakinsa ya ce: “Ni dai babu abin da zan ce illa kawai godiya ga Allah da Ya ba mu sa’a da hada kai muka gudanar da wadannan zabuka lami lafiya. Don haka ina yin kira ga daukacin ’yan Najeriya a kan mu ci gaba da yi wa wannan sabuwar gwamnatin addu’ar fatan alheri kuma Allah Ya bai wa shi sabon Shugaban kasa ikon shugabanci da yin aiki da adalci. Kuma bayan wannan, ina ba sabon shugaban shawara da ya hada kan al’ummar kasar nan ba tare da nuna wani bambanci ko wariya ba.”
Yayin da ita kuma Mataimakiyar Shugabar kungiyar Mata ’Yan Arewa Mazauna Jihar Edo, Hajiya Asabe Usmanu ta ce: “A matsayina na mataimakiyar shugabar kungiyar mata ’yan Arewa a nan Edo, ina ba wannan sabuwar gwamnati shawara da ta yi kokari ta taimaka ta share wa al’ummar Najeriya hawaye kuma duk wanda ya ba ta shawara, ta tsaya ta yi nazari a kai domin kauce wa kuskure a cikin aikin jama’a. Su kuma al’ummar Najeriya, su goya wa sabuwar gwamnatin baya da ba ta hadin kai da shawarwari nagartattu.”
Shi kuwa Malam Muhammad Taufik Dele, makaniken mota, yana mai cewa: “A hakikanin gaskiya zabukan bana abin farin ciki ne ga ’yan Najeriya. Don haka addu’armu ita ce Allah Ya ba wannan shugaban ikon jagoranci da adalci ga jama’a Musulmi da Kirista kuma shi shugaban ya dubi matsalolin talakawa da idon basira don magance su cikin sauki. Su kuma ’yan uwana ’yan Najeriya, mu yi hakuri da juna, mu manta da bambance-bambancen da ke tsakanin juna.”
Muhammed Aminu Zugana, dan kasuwa mai sayar da agogo da sarka ya ce: “Ni dai na gode wa Allah tunda an yi wadannan zabuka lami lafiya. Don haka ina yin kira ga daukacin al’ummar Najeriya da su ba da hadin kai ga wannan sabuwar gwamnatin da ci gaba da yi mata addu’ar fatan alheri. Ita kuma gwamnatin ina yin kira da roko gare ta da ta dube mu, mu da muke kananan ’yan kasuwa, ta tallafa mana a kan sana’armu da muke yi.”
Muhammadu Sani kuwa ya ce: “Ni dai babu abin da zan ce illa addu’ar Allah Ya ba Janar Buhari ikon cika alakawarin da ya yi wa ’yan Najeriya a kan batun tsaro da yaki da cin hanci da rashawa. Bayan wannan, ina kira ga ’yan uwana ’yan Arewa mazuna nan Jihar Edo, da su gyara halayensu tsakaninsu da juna da kuma da abokan huldarsu, ’yan asalin Jihar Edo.”
Malam Yusufu Ma’azu kuwa na cewa: “Ni dai sai godiya ga Allah tunda yake mun samu mun gudanar da kowane zabe cikin kasar nan lami lafiya. Don haka shawarata ga wadanda suka samu nasara ita ce, su tsaya a kan gaskiya su yi wa al’ummar kasa adalci, sannan su kuma wadanda ba su samu kai labara ba, su rungumi kaddara su dawo a hada kai a zauna lafiya.”
Akwai kuma wani matashi, Ali Adamu Bobi da abokin sana’arsa ta wasan kwaikwayo, bayan bayyana farin cikinsu sai suka taya Shugaban kasa mai jiran gado murna da yi masa addu’a. Daga bisani kuma suka bukaci sabuwar gwamnatin da ta sa su, su ma ’yan dirama cikin mutane da za a tallafa wa sana’arsu a cikin kasar nan.