Bayan ziyarar kasar Amurka sai me…

A ranar Alhamis din makon jiya ce, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya dawo gida bayan ziyarar aikin kwanaki hudu wato Lahadi 12 zuwa Laraba 15-07-15 da ya kai kasar Amurka, bisa amsa gayyatar da Shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya yi masa a lokacin taron kungiyar kasashen nan bakwai masu karfin masana`antu da ake wa […]

Bayan ziyarar kasar Amurka sai me…
Bayan ziyarar kasar Amurka sai me…

A ranar Alhamis din makon jiya ce, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya dawo gida bayan ziyarar aikin kwanaki hudu wato Lahadi 12 zuwa Laraba 15-07-15 da ya kai kasar Amurka, bisa amsa gayyatar da Shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya yi masa a lokacin taron kungiyar kasashen nan bakwai masu karfin masana`antu da ake wa lakabin G7, wanda aka yi a kasar Jamus cikin watan Yunin da ya gabata. 

Tabbas ziyarar ta dauki idanun duniya baki daya, ba ma a cikin kasar nan kadai ba, saboda irin yadda aka rinka hasashen Shugaba Obama ya gayyaci Shugaba Buhari ne da aniyyar ya cusamasa ra`ayin kasar nan ta karbi tsarin auren jinsi da Kotun kolin kasar Amurka ta halarta a kasar (Wa`iyazu billah) a kwanakin baya, alhali mu a nan kasar tuni Majalisun Dokoki suka zartar da dokar da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sanya wa hannu da ta haramta auren jinsi.
Ba ko shakka, bisa ga irin karfin tattalin arzikin kasa da na fada a jin da a yau kasar Amurka ke tinkaho da shi a duniya, da irin yadda shugaba Buhari ya shigo mulki a cikin mawuyacin hali na tabarbarewar matakan tsaro da na tattalin arzikin kasa da na rashin ayyukan yi da sauran matsaloli da suke gallabar kasar nan, tabbas yana bukatar samun tallafi daga babbar kasa irin ta Amurka da sauran takwarorinta irin na su kungiyar G7, kai harma da na cikin Nahiyarmu ta Afirka, kamar yadda muka gani yanzu kasashe irin su Janhuriyar Nijar da Chadi da Kamaru daBenin da ita kanta kasar nan sun taru sun kafa Rundunar tsaro tahadin guiwa da aniyar su yaki gwagwarmayar masu tada kayar baya na `yan kungiyar Jama`atu Ahlis Sunnah Lid Da`awati Wal jihad da ake ma lakkabi da Boko Haram.
Kamar yadda `yan kungiyar G7, suka gayyaci shugaba Buhari a wancan taron da suka yi a kasar Jamus, wanda Amurka na ciki,suka kuma ce ya je masu da kundin dukkan bukatunsa, haka ita ma kasar Amurka ta neme shi da yi, har ma ta kara fadadawa da ayarin nasa ya kunshi manya-manyan masu Masana`antu da Kamfanoni da `yan kasuwar kasar nan. Haka kuma din aka yi, bukatu irin na yadda shugaba Buhari zai kawo karshen rikicin`yan kungiyar Boko Haram da samun daidaito akan matakan tsaro a kasa baki daya, da yadda zai yaki cin hanci da rashawada yadda zai kawo karshen satar man fetur da iya karbo dukiyoyin da wasu shugabannin kasar nan suka sace suka kai kasashen waje da farfado da tattalin arzikin kasar, ta yadda ayyukan yi za su karu, na cikin manyan bukatun da shugaba Buhari ya tattauna kuma ya mikawa shugaba Obama da sauran makarraban kasar Amurka da ya samu tattaunawa da su a cikin ziyarar.
Shugaba Buhari, ya samu tattaunawa ta kai tsaye da mataimakin sugaban kasar Amurka Mista Joe Baden, wanda ya fara ba shi tabbacin kasar sa akan yaki da `yan kungiyar Boko Haram, amma kuma sai ya shawarci kasar nan da lalle ta hada yakin da shirye-shiryen kyauta jin dadi da tattalin arzikin jama`a, domin a ta bakin Mista Baden, yaki kadai ba zai kawo karshen wannan ta`addanci ba. Ya kuma shawarci shugaba Buhari da ya dage wajen yaki da cin hanci da rashawa, sannan kuma ya tabbatar da cewa mutane masu amana kadai ya ba mikamai a gwamnatinsa.
Shi ma shugaba Barrack Obama, a ganawar da suka yi da shugaba Buhari, kusan abinda mataimakinsa ya fadawa shugaba Buhari ya maimaita, ya kuma bayyana shugaba Buhari da cewa mutum ne mai mutunci, wanda mutuncinsa ne ya sa `yan Najeriya suka bashi goyon bayan da suka ba shi a babban zaben kasar na watan Maris da ya gabata. Mista Obama ya kuma bayyana kasar nan da cewa ita ce uwargarken nahiyar Afirka, don haka kome na nahiiiyar ta Afirka ya dogara ne kacokan akanta. Sai ya bada tabbacin cewa kasarsa za ta ci gaba da taimakawa kasar nan, muddin Najeriya din za ta tsaya akankamanta gaskiya da adalci cikin tafiyar da mulkin demokradiyya.
Bayan shugaba Obama, shugaba Buhari ya samu ganawa da jami`an gwamnatin kasar Amurka na da da na yanzu, sun kuma tattauna batutuwa daban-daban, musamman akan tafiyar da mulkin demokradiyya da yaki da masu tada kayar baya da cin hanci da rashawa da kuma yadda kasar nan za ta samu karbo kudaden da jami`an gwamnatin da suka gabata suka wawashe suka kai kasashen waje. Don kuwa bayan wannan ziyara a ruwaito gwamnan jihar Edo Mista Adams Oshiomhole. yana fadawa manema labaran fadar shugaban kasa a Abuja cewa akwai Minista daya daga cikin Ministocin tsohon shugaban kasa Jonathan da ya sace Dalar Amurka biliyan shida. Tirkashi! Ka ji mai karatu.
Su ma ayarin `Yan kasuwa da masu Masana`antu suka rufawa shugaba Bahari baya, sun samu tattaunawa da takwarorinsu na kasar Amurka da na sauran nahiyar Afirka akan yadda masu zuba jari daga kasar ta Amurka da sauran kasashen duniya za su shigo kasar nan su zuba jari, musamman akan fannin noma da wutar lantarki. Ziyara dai ce da za ka ce kwlliya ta biya kudin sabulu ko yanzu domin babbar kasa mafi karfin tattalin arzikin kasa da na masana`antu da tafiyar da mulkin demokradiyya da ma karfin fada a ji a duniya irin Amurka ta gayyaci shugaban babbar kasa a nahiyar Afirka irin Najeriya, a kuma samu tattaunawa gaba da gaba da kusan dukkan wadanda suka kamata, a kuma yi alkawurra taimakawa mai neman taimako irin kasar nan a irin wannan mawuyacin hali, ai sai a ce son barka da fatan Allah Ya ba da ikon a cika alkawurran da akai mana.
Amma kuma wani hamzari ba gudu ba, lalle akwai bukatar shugaba Buhari ya zuba idanu ya tabbatar da cewa dukkan alkawurrar da kasar Amurka ta yi masa na taimakawa akan yaki da `yan tada kayar baya da sayar mana da makamai (abin da ta ki yi a baya, ta fake da sunan za ta karya hakkin dan Adam, alhali ta dade tana karya shi cikin rikicin kasar Isra`ila da Palisdin), dataimakon horas da sojojinmu akan dibarun yaki da ta`addanci da alkawarin za ta horas da jami`an tsaronmu akan bincike da gabatar da kararraki akan wadanda suka sace mana makudankudadenmu suka kai kasashen waje da uwa uba yadda za a maido mana wadancan makudan kudadenmu da shugaba Buhari ya ce a duk shekara ana sace Dala biliyan 10 zuwa 20, musamman daga kudaden man fetur din mu, sun tabbata.
Shigar kasar Amurka da sauran kasashen Turai, musamman kungiyar G7, cikin harkokin kasar nan gadadan, tun kafin zabe da lokacin zabe da bayan zabe, har suka taimaka Shugaba Jonathan ya bar karagar mulki, duk dole mu fahimci cewa sun yi ne saboda suna ganin durkushewar tattalin arzikinmu zai shafi nasu, ta yadda Kamfanoninsu da Masana`antunsu za su rasa kasuwar da suke samu, don haka lalle mu fahimci manufofinsu don mu kara shirin zama da su. Allah Ka kama wa shugabanninmu.