Bayani a kan rawar da Najeriya ta taka a taron ITU na duniya na bana

Kafin  Aled Iwobi ya zura kwallon da ta ta yi sanadiyar samun gurbin Najeriya a gasar cin kofin duniya na badi, bangaren sadarwar kasar ta riga ta yi gaba wajen daga sunan kasar a idon duniya. Najeriya ta samu kyaututtuka guda 5 a taron na ITU na bana a can birnin Busan da ke Koriya […]

Bayani a kan rawar da Najeriya ta taka a taron ITU na duniya na bana

Kafin  Aled Iwobi ya zura kwallon da ta ta yi sanadiyar samun gurbin Najeriya a gasar cin kofin duniya na badi, bangaren sadarwar kasar ta riga ta yi gaba wajen daga sunan kasar a idon duniya.

Najeriya ta samu kyaututtuka guda 5 a taron na ITU na bana a can birnin Busan da ke Koriya ta Kudu a watan Satumba, kwanakin kadan kafin Super Eagles su saka murna a zukatan ‘yan Najeriya.

Samun nasarorin yana cikin rawar da tawagar kasar ta taka a lokacin taron, wanda ya samu halartar manyan baki masu fada aji a bangaren sadarwa ta duniya. Ba shakka taron ITU ne taro mafi muhimmanci a tarukan bangaren sadarwa. Don haka dole ayi murna idan aka lura da inda aka samu damar lashe wannan kyaututtukan.

Ga wadanda yanzu suke samun wannan labarin, a taron ITU na duniya, Hukumar Sadarwar Najeriya (NCC) ce ITU ta sanar a matsayin babbar abokiyar hulda saboda yadda ta dage wajen halartar tarukan ITU na tsawon shekaru. Kuma Hukumar ta samu takardar shaidar godiya ta musamman daga ITU da na zauren Thematic da kuma kyautar mahalarta masu aminci da kuma masu goyon baya na bana.

Hakanan kuma, Najeriya ta lashe kyautar ITU ta duniya, saboda zama gwamnatin da ta fi kowace wajen habbaka harkokin kananan kasuwanci da masana’antu (SMEs).

Uku daga kananan masana’antu da NCC ta je da su taron sun hada da Miss Temitope Awosika (Medsaf), Mista balentine Ubalua (Ubenwa) da Mista Chizaram Ucheaga (Mabis Computel), suna cikin wadanda ITU ta ba kyauta na duniya.

Wannan a bangaren kyaututtuka ke nan, halartar taron na ITU musamman a shekaru biyu da suka wuce, ya matukar nuna yadda kasar ke cike da bangarorin kasuwanci.

Wannan shekarar ba a samu wani canji ba a bangaren baje fasaha ba. Watakila canjin da aka samu kawai shi ne yadda Farfesa Umar Garba Danbatta ya yi amfani da wannan damar wajen nuna wa duniya cewa wannan gwamnatin ta saukake yayanin kasuwanci a kasar, kamar yadda yake a kunshe a cikin tsarin farfado da tattalin arzikin kasar.

Bayan haka kuma, idan mutum na neman wanda zai iya wannan aikin, babu wanda ya fi tsohon malamin jami’an cancanta. Saboda a shekaru biyu da ya yi a matsayin shugaban hukumar, hukumar ta samu nasarar yin ayyukanta a bayyane, inda a sanadiyar haka ne hukumar ta tara wa Gwamnatin Tarayya makudan kudin da ya kai Biliyan 140, duk da cewa NCC ba hukumar tara haraji ba ce.

Hukumar gyara harkokin ma’aikata (BPSR),  bayan lura da ayyukan hukumar, ta ba hukumar maki mai yawa a cikin sa’anninta a bangaren tsarin aiki. NPSR ta yaba wa hukumar inda ta ce hukumar na da “Tsarin kasuwanci mai karfi da yake taimakawa wajen yin aiki mai kyau.” A lokacin da take ba hukumar kyauta.

Sai dai kuma, Hukumar Tsara Nisan Zango ta Tasa, wadda ta tsara samun nisan kashi 30 a badi, zai zama babba abin tattaunawa, saboda yana bukatar jari mai girma.

A lokacin da yake jawabi a dakin daukan sautin ITU, Danbatta ya nuna cewa “Dokokin gwamnati bai tsaya a kan nisan zango ba. Amma dai Gwamnatin Tarayya a kwanan nan ta fito da tsarin farfado da tattalin arziki da cigaban kasa. A wannan sabon tsarin, an ba hukumar NCC aikin kula da samar da ababen bukata a bangaren nisan zango.

“Tsarin shi ne za mu samar da tallafi ga wadanda suka zuba jari, wanda zai hada da rage kashi 30 na kudin haraji da kuma rage wasu kudade musamman wajen shigo da kayan aiki da sauransu.”

Hakanan kuma shugaban hukumar ya ce saukarsu ke da wuya a yankin Asiya, suka fara gabatar da ayyuka, musamman wajen bayar da albishir da cewa an samu canjin mai aminci a Najeriya.

“Muna ta sanar da masu zuba jari a wannan taron cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta samar da canje-canje masu kyau, sannan ta saukake yayanin kasuwanci.

“An bayar da doka da cewa dole a rika yin ayyuka a bayyane domin a tabbatar da cewa an yi abin da ya kamata a kan lokaci. Har za a iya ladabtar da duk wata bangaren gwamnati da ta ja lokacin kafin ta amince da wata takardar da aika mata.,” inji shi.

Amma ‘yan kasuwa suna bukatan tabbaci a kan kasuwancinsu. Kuma wannan shi ne abin aka fi tattaunawa akai a wajen taron.

Danbatta ya yi amfani da damar wajen bayyana misalai na yadda hukumar NCC tare da hadin gwiwar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta hana bankuna sayan kanfononin sadarwa.

“Hukumar NCC na tabbatar muku cewa kofarmu a bude take. Kuma za mu duk mai yiwuwa wajen ganin mun tsare muku kasuwancin ku,” inji shi.

Ya kara da cewa NCC za ta ci gaba da aiki da nagarta, da zai bayar da tallafi ga masu zuba jari domin su ci gaba da samun riba mai yawa.

“Mun hada karfi da wasu hukomomi  cewa bankuna su daina sayan kamfanonin sadarwa. Bankuna ba za su iya rike kamfanonin ba, su tsaya a bangaren kudi kawai su ci gaba da samar da cigaba kamar na shaida suna yi.

“Kamar wannan kamfanin da yanzu aka mayar da sunansa 9 Mobile, wanda yanzu yake hulda da mutane sama da miliyan 20 a Najeriya. sakon da muke ba ‘yan kasuwa shi ne mu a NCC, kullum muna aiki ne domin mu tabbatar da tsabta da aiki mai kyau a bangaren sadarwar Najeriya, tare da tabbatar da tsare jarin ‘yan kasuwa.,’ inji shi.

Musa shi ne mataimakin shugaban NCC a kan harkokin yada labarai.