Bayani kan sabuwar shekara ta 1441 (2)

Kissar Annabi Musa (AS) da Fir’auna “Sai muka dawo da shi wurin mahaifiyarsa don hankalinta ya kwanta kuma don kada ta yi bakin ciki don ta san cewa alkawarin Allah gaskiya ne, sai dai kuma yawancin mutane ba sa fahimtar haka” (Kasas: Aya ta 13). “Lokacin kuma da ya kai karfinsa, ya kuma kammala, sai […]

Bayani kan sabuwar shekara ta 1441 (2)
Bayani kan sabuwar shekara ta 1441 (2)

Kissar Annabi Musa (AS) da Fir’auna

“Sai muka dawo da shi wurin mahaifiyarsa don hankalinta ya kwanta kuma don kada ta yi bakin ciki don ta san cewa alkawarin Allah gaskiya ne, sai dai kuma yawancin mutane ba sa fahimtar haka” (Kasas: Aya ta 13).

“Lokacin kuma da ya kai karfinsa, ya kuma kammala, sai Muka ba shi hukunci da ilimi, kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa (Kasas: A ya ta 14).

Bayan haka wadansu mutane suna fada sai ya je raba su sai daya daga cikinsu ya ki rabuwa sai ya naushe shi ba da niyyar ya kashe shi ba, sai ya mutu, shi kuma wanda ya mutu yana daga cikin jama’ar Fir’auna ne. Daga nan sai Annabi Musa (AS) ya yi kaura ya tafi Madayyana. Ya zauna har tsawon shekara goma, ya yi aure a can sannan ya dawo. A kan hanyarsa ta dawowa sai Allah Ya ba shi Annabta, sai Allah Ya aike shi a kan ya je wajen Fir’auna. Sai ya tafi wajen Fir’auna, cewa: “Shin labarin Musa ya zo maka? Lokacin da Ubangijinsa Ya kirawo shi a kwari mai tsarki wato Duwa?  Aka ce da shi “Ka tafi zuwa ga Fir’auna, hakika shi ya yi dagawa, Sannan ka ce “Shin zai yiwu gare ka  ka tsarkaka?  Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka ka ji tsoronSa?”

Sannan ya nuna masa babbar aya.  Sai ya karyata ya kuma yi sabo. Sannan ya ba da baya yana barna. Kuma ya tara jama’arsa ya yi shela. Sai ya ce “Ni ne Ubangijinku mafi daukaka!”

Saboda haka Allah Ya kama shi da azabar kalmar farko da ta karshe. Hakika a cikin wannan lallai akwai izina ga wanda yake tsoron Allah.”

Daga nan sai Fir’auna ya ce abin da ya zo da shi sihiri ne,  shi ma yana da masu sihiri, sai aka ajiye lokaci suka zo da nasu macizan, shi kuma da sandarsa, sai suka tattauna a kan wa zai fara  sai ya ce su fara. Sai suka jefa nasu macizan sai shi ma ya jefa sandarsa sai ta cinye duk macizansu baki daya.

“Sai matsafa suka fadi suna masu sujada suka ce, “Mun yi imani da Ubangijin Musa da Haruna.”

Sai Fir’auna ya ce “Yanzu kwa yi imani da shi tun kafin in yi muku izini? Hakika shi ne babbanku wanda ya koya muku tsafi. To lallai zan yanke hannayenku da kafafuwanku sabani (Wato hannun dama da kafar hagu), kuma ba shakka zan tsire ku a jikin kututturan dabino, lallai kuma za ku zan wane ne tsakanin ni da shi wanda ya fi tsananin azaba kuma wanda azabarsa tafi dorewa. “Muka kuma yi wa Musa wahayi cewa “ka tafi a cikin dare da bayiNa, hakika za a biyo bayanku (Suratul Shu’ara’i: Aya ta 52 zuwa 68).  “Sai Fir’auna ya aika birane don a tattaro masa mayaka. “Kuma hakika su lallai ne suna musguna mana. “Hakika kuma mu lallai ne masu kwana cikin shiri ne.” Allah Ya ce, “Sai Muka fitar da su daga gonaki da wuraren ruwa mai gudana. Da taskoki da mazauna na alfarma. Kamar haka ne muke gadar da su ga Bani Isra’ila. Sai suka riske su a lokacin fitowar rana. To lokacin da jama’ar biyu suka ga juna, sai sahabban Annabi Musa suka ce “Hakika lallai ne za a cim mana!” Sai Annabi Musa ya ce, “A’aha, ko daya ba za su riske mu ba. Hakika Ubangijina Yana tare da ni, zai kuma shiryar da ni hanyar tsira.  Sai muka yi wahayi ga Musa cewa: “Ka bugi kogi da sandarka, da ya buga sai kogin ya dare, kowane yanki sai ya zama kamar katon dutse.  Muka kuma kusantar da wadancan (wato mutanen Fir’auna) zuwa kusa da kogin.  Muka kuma tserar da Annabi Musa da wadanda suke tare da shi gaba dayansu. Sannan Muka nutsar da wadancan (wato mutanen Fir’auna da shi). Hakika game da wannan lallai akwai aya mai nuna cikar kudirin Ubangiji, amma yawancinsu ba su zamanto masu ba da gaskiya ba.  Kuma hakika Ubangijinka lallai Shi ne Mabuwayi Mai rahama (Saratul Shu’ara’i: Aya ta 52 zuwa ta 68).

Wannan shi ne labarin Annabi Musa (AS) da Fir’auna da karshen Fir’auna. To yaushe wannan abu ya faru kuma yaushe Annabi Musa ya samu wannan nasara.To amsar wannan tambaya ita ce: “Annabi Musa ya samu wannan nasara ce a ranar Ashura wato 10 ga  Muharram, don haka wannan watan wata ne babba maj daraja da alfarma. An samu Hadisi daga Bukhari da Muslim daga Abdullahi dan Abbas (RA) ya ce; Manzon Allah (SAW) ya zo Madina ya samu Yahudawa suna azumin Ashura sai ya ce wace rana ce wannan wacce kuke azumi a cikinta? Sai suka ce a cikinta ce Allah Ya tserar da Annabi Musa da mutanensa, aka kuma hallakar da Fir’auna da mutanensa. Sai Annabi Musa ya yi azumi a wannan rana don gode wa Allah. To muma muna koyi da shi, shi ya sa muke azumi a wannan rana. Sai Annabi (SAW) ya ce; To ai mu ne muka fi cancanta mu yi azumi a wannan rana don murnar kubutarsa. Sai Annabi ya yi azumin Ashura kuma ya umarci sahabbai da yin azuminsa.

Hakika yin azumin Ashura da farko ya zama wajibi ne kowane Musulmi ya yi shi,  amma lokacin da aka farlanta azumin watan Ramadan sai ya zana Sunnah mai karfi.

Sayyida Hafsat (RA) ta ce abubuwa hudu suna daga cikin Sunnar Annabi Muhammad (SAW): “Azumin Ashura da Azumin Goma ga Zul-Hajji da Azumi Uku a kowane wata da Raka’a biyu bayan fitowar Alfijir.” Ahmad da Nisa’i  suka ruwaito. Albani ya inganta shi.

An tambayi Ibn Abbas (RA) a kan azumin Ashura. Sai ya ce ban san wani azumin da Annabi yake yi don neman falalarsa ba, kamar azumin Ashura. Buhari da Muslim ne suka ruwaito.

Wannan yana nuna mana a sarari azumin wannan rana yana daga cikin muhimman azumi. Kuma Annabi (SAW) ya yi bayanin azumi wannan rana yana kankare zunubin shekara guda. Annabi (SAW) ya ce azumin Ashura ina kyautata zato ga Allah Ya kankare laifin shekera guda idan an yi shi. Imam Muslim ya ruwaito.

Kuma Imam Muslim ya sake ruwaitowa daga Dan Abbas (RA) ya ce lokacin da Annabi ya yi azumin Ashura kuma ya umarci a yi shi, sai dai sahabbai suka ce ai rana ce da Yahudawa da Nasara suke girmama ta. Sai ya ce musu, insha Allah idan shekara mai zuwa ta zo za mu yi azumi biyu. Za mu yi tara mu yi goma. Amma kuma kafin shekara ta zagayo Annabi (SAW) ya bar duniya.

An dada samun wani Hadisi daga Muslim Annabi (SAW) ya ce an ce ku saba wa Yahudu ku yi azumi kafin Ashura ko ku yi azumi bayan Ashura.

Imam Ibn Kayyim ya ce; matakan azumin Ashura uku ne:

  1. Yin azumi kafin Ashura kuma bayan ka yi Ashura sai ka yi wani azumin.
  2. Ka yi azumi kafin Ashura kuma ka yi azumi bayan Ashura. Wato ka yi tara kuma ka yi goma.
  3. Yin azumin Ashura shi kadai, kowane ka yi amma mafificin azumi shi ne ka yi tara da goma.

Don haka ka saba wa Yahudawa ke nan don su guda daya kawai suke yi kai kuma ka yi biyu.

Sai malamin ya ce idan ka yi azumi kafin shi kuma ka yi azumi bayansa haka ya fi kyau kuma ya fi cika har dai ka natsu ka tabbatar ka yi azumin Ashura cikakke idan akwai shakkar shiga sabon wata saboda Sunnah ta tabbatar da cewa kowane mutum ana so ya rika azumi uku kowane wata musamman azumi a wannan wata na Muharram yana da daraja na musamman da lada mai yawa.

Imam Muslim ya ruwaito daga Abu Huraira (RA) Annabi (SAW) ya ce; “Mafificin azumi bayan watan Ramadan shi ne azumin wata mai alfarma kuma mai albarka wato Muharram, mafificin Sallah bayan watan Ramadan shi ne nafilolin dare.

Kuma daga cikin abin da ake so mutum ya yi na azumi shi ne azumin Litinin da Alhamis. Saboda an rawaito cewa Annabi (SAW) yana azumi duk ranar Litinin da Alhamis, sai aka tambaye shi, sai ya ce “Ai ranaku ne da ake daukar aikin masu aiki, kuma wanda aka dauki aikinsa yana azumi ya fi lada.”

Kuma an ruwaito cewa ana son yin azumi guda uku kowane wata. Ranar 13 da 14 da 15 ga kowane wata. Ana kiransu da darare masu haske a wata.

Za a iya samun Imam (SP) Ahmad Adam Kutubi ta: 08036095723

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos