Bayanin Wasan Kwaikwayo a Hausa (2)
A makon jiya mun kawo ma’anar Kalmar Wasan Kwaikwayo a mahamgar masana da kuma ginshikai hudu da ake gina Wasan Kwaikwayo a kansu wadanda suka hada da sake kama ko canja tufafi ko murya. A samu wani wuri na musamman (wato dandali ko dandamali) sannan ya kasance yana dauke da wani sako sai na karshensu […]
A makon jiya mun kawo ma’anar Kalmar Wasan Kwaikwayo a mahamgar masana da kuma ginshikai hudu da ake gina Wasan Kwaikwayo a kansu wadanda suka hada da sake kama ko canja tufafi ko murya. A samu wani wuri na musamman (wato dandali ko dandamali) sannan ya kasance yana dauke da wani sako sai na karshensu shi ne; dole a samu tanka-in-tanka. A yau za mu kawo muku bambancin tsakanin wasa da Wasan Kwaikwayo da kuma takaitaccen tarihin shi kansa Wasan Kwaikwayon.
Bambancin wasa da Wasan Kwaikwayo
Ta hanyar kwaikwayo ne dan Adam yake koyon magana da kuma dabarun sarrafa harshe, haka kuma ta kwaikwayo ne yake koyon yadda ake sarrafa abubuwan da ke kusa da shi, ta hanyar samar da muhalli da tufafi da makamai da sauransu.
Kuma ta kwaikwayo ne dan Adam yake koyon sana’a kamar noma da farauta da kira da sauransu. Ke nan Wasan Kwaikwayo dadadden al’ada ce a cikin rayuwar Hausawa, saboda haka ana kallonsa ta hanyoyi da dama.
A ra’ayin wani masani Ibrahim Yaro Yahaya, ya ce “A al’adance ko a gargajiyance Wasan Kwaikwayo na nufin dukkan abubuwan nishadi da ban-dariya da tsokana da annashuwa da kuma motsa jiki da akan yi a wurare daban-daban, musamman a wuraren bukukuwa da bakin kasuwa, domin a nishadantar ko a fadakar da al’umma.”
Haka kuma a wani hadin gwiwa a tsakanin masana biyu, a nasu ra’ayin, wato Abdulkadir Dangambo da Ibrahim Yaro Yahaya sun ce: “Wasan Kwaikwayo wasa ne inda akan aiwatar da wata matsala ta rayuwa cikin siffar yakini ko kuma a rubuta shi.”
Haka Abdulkadir Dangambo ya ce “Wasan Kwaikwayo kamar yadda sunansa ya nuna, wasa ne da aka gina kan kwaikwayon wani labari ko wata matsala ta rayuwa da ake son nuna wa ga jama’a.”
Shi kuwa Tanimu ’Yar’aduwa ya bayar da ma’anar Wasan Kwaikwayo ne kamar haka: “Wasan Kwaikwayo kamance ne na wasu halaye ko yanayin rayuwa, wadanda masu hikima sukan shirya su gabatar da shi ta hanyar annashuwa da raha da nishadi don cimma wata manufa.”
A wani aiki da su Sadiya Omar Bello suka tsattsefe, sun ce “Wasan Kwaikwayo wani tsararren abu ne wanda ake kwatanta wata rayuwa ta wani yanayi don bayyana wa mutane ta hanyar wasa.” Har wa yau Atiku Dunfawa ya ce “Wasan Kwaikwayo shi ne duk abin da aka tsara kwaikwayonsa don nuna cewa jama’a su gani, kuma shi wannan abin da za a nuna yana iya kasancewa ya taba faruwa, yana kuma iya kasancewa bai taba faruwa ba, sai dai an zauna ne an kago shi da kwakwalwa don nuna wa jama’a.”
Bugu da kari, za mu iya fahimtar cewa wasan kwaikwayo ba abu ne na gaskiya ba, kirkirarsa ake yi, don haka idan muka dauki wadannan kalmomi guda biyu, wasa da kuma kalmar kwaikwayo za su tabbatar mana da cewa, wasa dai wani abu ne da Hausawa ke nufin duk wani abu da aka gabatar wanda ba gaskiya ba ne, sannan kowa ya amince ana yin sa ne domin samar da raha da ban-dariya, ba don cin mutunci ko cin zarafin wani ko wata kungiya ba. Shi kuma kwaikwayo yana nufin aikata wani abu ta hanyar canja kama ko murya ko jiki ko siffa ko muhallin yin aikin da nufin nuna kwaikwayo ko nunin abin da ake so juya.
A bisa wadannan bayanai za mu iya fahimtar cewa Wasan Kwaikwayo yana da siffofi biyu a al’adar al’ummar Hausawa. Da farko dai akwai wasu al’adu masu tsari irin na wasan kwaikwayo. Na biyu kuma, akwai Wasan Kwaikwayo irin wanda muka sani ana shiryawa, ana gudanarwa a dandamali, ko a gidan rediyo da talabijin.
Takaitaccen tarihin Wasan Kwaikwayo a Hausa
Shi dai wasa irin na nishadi ko na kwaikwayo ko kuma na motsa jiki dadaddiyar al’ada ce a kasar Hausa kamar yadda muka yi bayani a baya, musamman ganin cewa ya girmi rubutacce. Ke nan dole ne a amince cewa tun fil azal akwai Wasan Kwaikwayo a rayuwar kowace al’umma kafin zuwan rubutu. Saboda haka idan aka koma kan batun tarihin Wasan Kwaikwayo a kowace al’umma ya dace ne a koma ga al’adu da adabin gargajiya domin ganin ko akwai masu kama da irin wannan abu, a nan abin da ke da muhimmanci ba yanayin da aka samu abin ba, wato a rubuce ko a ka, irin amfanin wannan abu a tsakanin jama’a. Haka kuma ba maganar rana ko wata ake yi ba, a’a, lokacin da ake jin cewa ya samu ginuwa a tsakanin al’ummar. Saboda haka a takaice za mu iya cewa Wasan Kwaikwayo ya samo asali ne tun farkon ginuwar al’ummar Hausawa. Ita wannan al’umma tana tafiya ne da al’adunta na gargajiya da suka hada da wasannin gargajiya da sauran wasanni. Saboda haka za mu iya karkasa wasannin zuwa gida-gida kamar haka: Wasannin gargajiya na wasa kurum: Wasan kura ko na maciji ko na kunama. Wasannin sana’a da suka hada da wasan gardawa (hawan kaho) da na ’yan tauri (Wasan Tauri) da na ’yan kama da na ’yan dabo. Wasannin dandali ko wasannin yara da suka hada da A-sha-ruwan -tsuntsaye da Dan-akuyana da na ’Yar tsana. Wasannin bukukuwan al’ada da suka kunshi wasan Giwa-sha-laka da Bikin Budar Daji da na Kalankuwa da Wasan Bori. Sai dai kafin mu shiga takaitaccen bayani kan tarihin Wasan Kwaikwayon Hausa bari mu dubi asalinsa da alakarsa da sauran na sassan duniya. Kusan duk an yarda cewa Wasan Kwaikwayo shi ne ginshikin hanyoyin da dan Adam ke bi yana koyon yadda zai rayu. Watakila, ke nan za a iya danganta asalin Wasan Kwaikwayo da farkon bayyanar dan Adam a doron kasa. Akwai ra’ayoyi da dama game da asalin samuwar Wasan Kwaikwayo, akwai masu ra’ayin addini shi ne asalin Wasan Kwaikwayo. Masu wannan ra’ayi suna ganin cewa Wasan Kwaikwayo ya samo asali ne ta hanyar bautar gumaka da kabilun Girkawa ke yi a wani biki wanda ya shafi addininsu. Suna gudanar da wannan bauta a wani kayyadajjen lokaci na shekara. Kuma wannan biki a gaban ’yan kallo ake gudanar da shi. Haka kuma akwai wani ra’ayi mai nuna cewa a Gabas ta Tsakiya da kuma kasar Indiya har ma da wasu sassa na Afirka mutanen sukan yi wani abu mai kama da Wasan Kwaikwayo musamman a lokacin da suke yin ta’azziyar bikin mutuwar muhimmin mutum don nuna girmamawa a gare shi.
Saboda haka Wasan Kwaikwayo na nishadi, ko wanda ake yi don motsa jiki, ko na addini abu ne wanda ya samo asali da dadewa a Kasar Hausa. Wasan Kwaikwayo ya samu ne tun wanzuwar al’ummar Hausawa. Kuma muna hangen cewa abubuwan gargajiya sun girmi na zamani ko wadanda ake rubutawa. Abin nufi a nan shi ne Wasan Kwaikwayo ya samu ne ga al’ummar Hausawa tun kafin wanzuwar ilimin zamani na karatu da rubutu.
Da dadewa akwai wasu al’adu da yara ko samari suke gabatarwa ta hanyar kwaikwayo a tsakaninsu, shekaru aru-aru kafin al’ummar Hausawa su fara hulda da cudanya da wasu al’umma da ba su ba, wato na ketare. Daga cikin irin wadannan al’adu na Hausawa akwai: wasan langa; a cikin wannan wasa yara za su kwaikwayi yadda ake yaki. A nan yara za su kasu gida biyu ne wannan langar da wancan, kuma kowane gida yana kokarin ture langar dan uwansa ko abokin wasansa. Kuma su wadannan gidaje biyu suna daukar kansu a matsayin abokan gaba na garuruwa guda biyu. Sannan kowane gari yana karkashin sarkinsa.
Da ganin wasan kansa yaran na kwaikwayon dabi’ar yaki ne a cikin wasa. Bayan wannan akwai bikin ’yar-tsana. Galibi yara ’yan mata su ne suke yin wannan wasa. Wasa ne wanda idan yarinya ta mallaki ’yar-tsana, sai ta rika yi mata raino irin na gaske, ta rika kwaikwayon ciyar da ita, tana yi mata wanka, idan ta girma ta yi mata kunshi, ta yi mata ado na tufafi da sauransu har ta kai fagen yi mata aure da sauran hidimomi. A irin wannan wasa ’yan mata na kokarin su kwaikwayi yadda ake rainon mutum tun yana karami har ya girma, har a yi masa aure a cikin wasa.
Babu ko tantama tunda aka samu wasa da kuma kwaikwayo, to ya zamo Wasan Kwaikwayo ke nan. Bayan wannan, hasali ma manya da kansu baya ga irin wadannan wasannin gargajiya na yara, akwai wadansu al’adu da sukan yi masu siffar Wasan Kwaikwayo. A cikin irin wadannan al’adu, akwai: Bori: wannan wata al’ada ce a Kasar Hausa wadda Hausawa kan yi don neman kubuta daga wata cuta da ta kama mutum tana wahalar da shi. Idan ana neman waraka daga wannan cuta mai rikitarwa, to wani lokaci a ce sai an yi wa mutum mai irin wannan cuta girka kafin ya samu waraka. To sai ’yan bori su taru ana yi musu kida da goge ko garaya ko molo ko duma ko dundufa. Su ko sai su hau bori suna tuma suna faduwa.
Ta wannan haujin sukan kwaikwayi iskokin da ke tare da su ta hanyar jirkita magana da siffofinsu. Haka kuma akwai Wasan Kalankuwa: Kalankuwa wani wasa ne da samari da ’yan mata kan shirya suna kwaikwayon aikin mulki da gudanar da shari’a a karkara da kuma yanayin zamantakewa a cikin kaka. Akan gabatar da irin wannan wasan a gaban manyan gari da sauran mutanen gari a matsayin masu kallo. Kuma akan tanadi wuri na musamman don gudanar da wannan wasa, kuma a cikin wannan wasa akan kwaikwayi wasu halaye da dabi’un mutane. Kuma masana na hangen cewa tun a wajen sana’ar Bahaushe ta farko, wato farauta akwai birbishin Wasan Kwaikwayo a ciki. Wannan yana da alaka da irin abubuwan da suke faruwa can daji idan an je wurin farauta. Domin wani lokaci akan samu ’yan farauta da irin su Bikin Budar Daji ko Shan Kabewa da sauransu. Kamar yadda tarihi ke maimaita kansa, Wasan Kwaikwayo ya samu ginuwa a tsakanin al’ummar Hausawa tun fil azal. Wannan ne ya sa aka rarraba shi zuwa gida uku kamar haka: Na daya akwai wasannin gargajiya na Hausa. Na biyu wasannin dandali wato wadannda samari maza da ’yan mata ke yi. Na uku, wannan ya kunshi bukukuwa.
Mun ciro wannan rubutu ne daga shafin makarantarMalamBambadiya: bambadiya.blogsport.com
Za mu ci gaba