Bayar da ilimi kyauta: El-Rufa’i na yaudarar jama’ar Kaduna ne kawai –Gwamna Yero

Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya ce yaudarar jama’ar jihar dan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC Malam Nasir El-Rufa’i yake yi da ya ce zai bayar da ilimi kyauta idan aka zabe shi. Gwamna Ramalan Yero ya bayyana haka ne ta bakin kakakinsa Malam Ahmed Mayaki a tattaunawa da manema labarai a Kaduna […]

Bayar da ilimi kyauta: El-Rufa’i na yaudarar jama’ar Kaduna ne kawai –Gwamna Yero
Bayar da ilimi kyauta: El-Rufa’i na yaudarar jama’ar Kaduna ne kawai –Gwamna Yero

Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya ce yaudarar jama’ar jihar dan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC Malam Nasir El-Rufa’i yake yi da ya ce zai bayar da ilimi kyauta idan aka zabe shi.

Gwamna Ramalan Yero ya bayyana haka ne ta bakin kakakinsa Malam Ahmed Mayaki a tattaunawa da manema labarai a Kaduna a ranar Litinin da ta gabata.
Ya ce kowa ya san cewa a kasashen waje ’ya’yan El-Rufa’i suka yi karatu don haka da jin irin wannan kalami an san yaudara ce.
Ya ce, “Abin dariya ne mutumin da ya yi karatu a firamaren Gwamnati ta Kawo; amma ya bar ta a halin da take ciki; firamaren Kawo na daga cikin makarantu da Gwamna Mukhtar Ramalan Yero ya gyara.”
Ya je makarantar da ya yi watsi da ita, ya kaddamar da gangaminsa alhali lokacin da ya yi minister zai iya gyara ta amma bai gyara ta ba. “Amma yanzu saboda yana takara yake maganar bayar da ilimi kyauta idan aka zabe shi, alhali wannan gwamnati tana bayar da ilimin kyauta a yanzu haka,” inji Kakakin Gwamnan.
Ya kara da cewa’ “Abin dariya ne mutumin da ’ya’yansa suke karatu a kasar Ingila, saboda ba ka da yakini a kan tsarin ilimin nan kasar. Saboda ka samu dama kai ’ya’yanka, yanzu ka dawo ka ce wa al’ummar Kaduna z aka dauko ’ya’yanka su dawo makarantun gwamnati. Kuma abin dariya ne da raina hankalin mutane ya ce zai bayar da ilimi kyauta ko ’ya’yansa za su dawo makarantun gwamnati alhali bai da yaran da suke zuwa makaranta a yanzu.”
Gwamnan ya ce, da’awar El-Rufa’i na zai bunkasa jihar ma fadi ne kawai, domin bai san jihar ba. “Iyalansa suna zaune a Abuja, amma kana maganar sake fasalin Kaduna. Kadunar da ba ka sani ba. Wadannan muhimman batutuwa ne da ya kamata mu yi tambaya a kansu ba wai mu kawar da kai ba,” inji Maiyaki.
Gwamnan ya ce al’ummar Jihar Kaduna sun wuce a yi musu romon baka ko a yaudare su. Kuma duk wanda yake son ya shugabance su ya yi magana a kan wasu batutuwa ba wadanda aka riga aka magance su ba.
Maiyaki ya ce babu siyasa a batun mayar da Kwalejin Ilimi da ke Gidan Waya zuwa jami’a, inda ya ce a Jihar Kaduna ana samun masu neman shiga Jami’ar Jihar dubu 50, inda ake iya daukar dubu biyar zuwa dubu shida saboda karancin gurabe. Ya ce wannan ne ya sanya aka yanke shawarar kafa jami’ar. Kuma an kammala dukkan shirye-shirye don mayar da kwalejin jami’a.