Bayern da PSG na ribibin Ziyech, Tottenham za ta maye gurbin Conte
Barcelona ta amince ta sayi dan wasan Atletico Madrid da Portugal Joao Felix.
Manchester City na shirin soma tattaunawa da Julian Alvarez na Argentina game da sabunta kwantiraginsa duk da cewa dan wasan mai shekara 23 ya isa kulob din a bazarar da ta gabata. (Mirror)
Tottenham ta kyallara ido kan tsohon manaja Mauricio Pochettino a matsayin wanda zai maye gurbin Antonio Conte, idan dan Italiyan ya kawo karshen aikinsa a karshen kakar bana. (Nicolo Schira)
- NAJERIYA A YAU: Shin don talakawa gwamnoni ke adawa da canjin kudi?
- Dawowar sanyi a Kano: Jama’a na kuka, manoma na murna
Dan wasan baya na Croatia, kuma na RB Leipzig, Josko Gvardiol, mai shekara 21, ya ce ya na son buga wasa a Firimiyar Ingila kuma tun shekarar 2020 ya ke kwadayin komawa Leeds United. Ko a bara Chelsea ta so ta saye shi. (Times – subscription required)
Tottenham na zawarcin dan wasan Real Madrid da Jamus, Antonio Rudiger, 29, a bazara. (Fichajes – in Spanish)
Bayern Munich ta PSG na zawarcin dan wasan Chelsea da Morocco, Hakim Ziyech, mai shekara 29. (Fichajes – in Spanish)
Manchester United na shirin yi wa David de Gea karin albashi zuwa £250,000 duk mako domin ganin golan na Spaniya mai shekara 32 ya ci gaba da zama a Old Trafford, sai dai tuni kungiyar ke hangen golan Leeds Illan Meslier, 22, a matsayin wanda zai maye gurbinsa. (Sun)
Mai kungiyar Chelsea Todd Boehly ba shi da niyyar korar manajan kungiyar, Graham Potter duk da rashin nasarar da Chelsea din ta yi a hannun Southampton a ranar Asabar. (Mirror)
Tayin sayen Manchester United da Sir Jim Ratcliffe ya yi kasa yake da tayin Sheikh Jassim Bin Hamad Al Thani ya yi na £5bn. (Foot Mercato – in French)
West Ham za ta yi tayin sayen dan wasan Manchester United Scott McTominay da dan wasan Ingila Harry Maguire, 29 da mai buga wa Netherlands tsakiya Donny van de Beek, 25, da kuma dan wasan gaba na Faransa Anthony Martial, 27. (CaughtOffside)
Hammers din na zawarcin dan wasan Lazio mai buga wa Serbia tsakiya Sergej Milinkovic-Savic, 27, cikin ’yan wasan da za su maye gurbin Declan Rice, idan dan wasan mai shekara 24 ya bar kulob din a bazara. (Sun)
Barcelona na bibiyar Manchester City kan dan wasanta na tsakiya, asalin Sifaniya Rodri, gabanin bude kasuwar saye da sayar da ’yan wasa inda sun kai tayin farko kan fam miliyan 80 kan dan wasan mai shekara 26. (Football Insider)
Masu hannun jari na Qatar za su iya neman hannun jari a Tottenham, ko da Sheikh Jassim Bin Hamad Al Thani ya kammala sayen Manchester United. (Times – subscription required)
Barcelona ta amince ta sayi dan wasan Atletico Madrid da Portugal Joao Felix a Janairun 2022, sai dai yarjejeniyar ba ta tabbata ba saboda dokokin hukumar kula da kudaden da kulob-kulob ke kashewa wato FFP. (AS – in Spanish)
Blackburn Rovers sun yi wa dan wasan Chile Ben Brereton Diaz, 23, tayin £30,000 duk mako tsawon shekara daya domin ya ci gaba da zama da su dai-dai lokacin da Villareal ke zawarcinsa. (Sun)
Newcastle United na shirin sayen dan wasan Fulham da Amurka, Antonee Robinson, 25. (Football Insider)
Dan wasan Nottingham Forest Lewis O’Brien, 24, ya ja hankalin kungiyoyi kamar New York City da Columbus Crew da kuma Atlanta United. (Sun)
Liverpool ta soma tattaunawar farko kan sayen dan wasan Colombia na ’yan kasa da shekara 20, Kevin Mantilla, 19, daga Independiente Santa Fe. (Football Insider)
Newcastle United na zuba ido kan dan wasan Arsenal kuma mai tsaron gidan Scotland Kieran Tierney, mai shekara 25. (Football Insider)
An yi wa iyalan Glazer tallafin tattalin arziki, domin ci gaba da mallakar kungiyar Manchester United bayan kungiyar mai mazauni a New York ta yi rijistar kudin ruwa a hannun jarin da ta zuba a kulub din. (ESPN)
Inter Milan na cikin masu zawarcin dan wasan Borussia Monchengladbach kuma na gaban Faransa Marcus Thuram, mai shekara 25, gabanin kungiyoyin Manchester United da Bayern Munich. (Calciomercato – in Italian)
Chelsea da Tottenham na duba yiwuwar dauko dan wasan gaba na Ireland Evan Ferguson, mai shekara 18. (Sun)
Sevilla na duba yiwuwar dauko aron dan wasan Manchester City da Sifaniya Sergio Gomez, mai shekara 22. (Fichajes – in Spanish)