Bayern Munich ta dauko aron Cancelo daga City

Cancelo yana da kwantaragin zama a City har zuwa shekarar 2027.

Bayern Munich ta dauko aron Cancelo daga City

Bayern Munich ta kammala kulla yarjejeniyar daukar aron mai tsaron bayan Manchester City, Joao Cancelo.

An kammala yarjejeniyar ce a wannan Talatar da ke zaman ranar rufe kasuwar musaya da cefanen ’yan kwallo a Turai.

Cikin sanarwar da City ta fitar, ta ce Cancelo zai yi zaman aro a kungiyar ta da ke buga gasar BundesLiga zuwa karshen wannan kakar.

Sai dai wasu bayanai na cewa Bayern na da zabin sayen dan wasan a kan farashin fam miliyan 70 idan kakar wasannin ta kare.

Cancelo wanda ya ci wa kasarsa Portugal kwallaye bakwai a haskawa 41, ya isa Munich ne bayan an auna koshin lafiyarsa a ranar Litinin.

Masu sharhi kan harkokin tamaula na ganin cewa zuwan Cancelo zai iya zama barazanar kawo karshen zaman dan wasan bayan kungiyar na Faransa, Benjamin Pavard.

A shekarar 2019 ce Cancelo mai shekaru 28 ya tafi City daga Juventus a kan farashin fam miliyan 65, inda a yanzu yana da kwantaragin zama a kungiyar har zuwa shekarar 2027.

Akwaii yiwuwar Cancelo ya soma wasansa na farko a Bayern yayin karawar da kungiyar za ta yi da Mainz a DFB-Pokal, ko kuma a wasan bakunta na Bundesliga da za ta je Wolfsburg ranar Lahadi.