Bayern Munich ta lashe gasar Bundesliga

Bayern Munich ta lashe gasar karo na 11 a jere.

Bayern Munich ta lashe gasar Bundesliga

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta lashe Gasar Bundesliga bayan da ta doke FC Kologn da ci 2 da 1.

Tun da fari Munich na mataki na biyu a gasar inda Dortumnd ta ba ta tazarar maki daya.

Dortumnd ta barar da damarta na lashe gasar, bayan da ta yi kunnen doki da kungiyar Mainz a gida.

Dan wasan gaban Dortumnd, Haller ya barar da bugun fenariti, lamarin da ya sanya kungiyar ta rasa lashe gasar.

Tuni dai aka nada Bayern Munich a matsayin Zakarar Bundesliga na 2023.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan